← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 137

Sashe 79

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin kamar so take ta bugi cikinsa sannan kamar wayo take so ta yi masa ne yasanya ya dake yace’’ke!Kausar bana son hauka da shirme da sharri…idan ba so kike in yi miki more than abunda na yi niyyar yi ba to kawai ki bani amsoshina da na zo k’arba mu yi ta ta k’are,”
‘’How dare you!ta ya ma zaki k’ala mini sharri wai ni Ina so in kashe Yashjub! baki da hankali ne?kuma wa kike tunanin za ki gayawa wannan maganar ya yarda?bari ki ji ko Mommy idan kika gayawa wallahi ba za ta tab’a yarda da ke ba,za ki sha mamaki idan ta juya miki baya har abada ,dan babu uwar da za ta yarda wata tazo ta ce mata d’anta yanaso ya kashe d’anta!’’.

Goge hawaye Kausar ta yi ta d’ago ta fuskance sa tukunna tace’’Yassir cewa na yi ‘zan fad’awa kowa kaine ka cire tayar mota sannan zan fad’awa kowa kaine ka saka bomb a estate d’in Yashjub’.A kaff cikin maganata ka ji ta inda nace ‘kana so ka kashe Yashjub’?’’.

Cikin fushi hargagi da hargowa yace’’Kausar zan illataki fa! ni za ki yiwa wasa da tunani?ai indai aka ji kince na cire taya to an san kashe sa nake son yi kenan!’’
Tsit!haka muryarsa ta tsaya chak!yana mai recalculating what he just said yanzun a cikin kwakwalwar sa’’

Kafin ya yi cilli da belt d’in hannunsa tukunna ya d’aga hannu kamar zai damk’i wuyanta kamar kuma wanda ya tuna wani abun sai ya tsaya chak!! kafin ya juya mata baya yana wani irin huci kamar mayuncin zaki….

Wata bahaguwar ajiyar zuciya Kausar ta sauk’e kafin ta d’an matsa garesa tace’’ Bari kaji abunda baka sani ba! Ko da ace Mommy bata tab’a shiga aji ba,wallahi ba zan yi kaffara ba itama ta d’an fahimci wani abun,sakamokon yadda ka dinga k’ok’arin tonawa kan ka asiri tun a crime scene d’in,har sign na dinga yi maka da ido amma sam ka kasa fahimta
Shiyasa ka ga hankalina ya tashi raina ya b’aci,ga kuma rashin lafiyar da take damuna,’’
Ahankali ta sake taku d’aya ta kamo hannunsa ba tare da ta zagaya gaban sa ba ta ci gaba da cewa’’ranar a d’akinka na gaya maka we re on this together,Yassir tunda har na iya danne zuciyata na had’a ka da Munirat inaso ka san na d’auki mission d’innan da mahimmanci,duk da na san cewa kashe Yashjub ba ya cikin tsarinmu amma idan har ka gaya mini dalilinka zan goya maka baya,kai ko da ace ba za
ma ka gaya mini dalilin naka ba Yassir zan goya maka baya I love you I want to see u win akan komai kai kuma a ko da yaushe zargina kake yi ban san ta ya zan nuna maka ina sonka ka yarda da ni da gaske ba, da ace na san taimakon ka da muka yi da ni da Mommy zai janyo mini haka daga gareka da ban yi ba tunda na lura tun lokacin da na d’an ja baya da kai saboda mu samu a fasa aurenmu a k’ara maka share har gobe baka yarda da ni ba Yassir’’
Ta k’arashe maganar tana mai durk’ushewa a wajen ta fashe da kuka.

Ahankali Yassir ya sauk’e ajiyar zuciya tashi d’aya ya fara ganin rashin kyautarwar sa,how can he not trust Kausar?despite irin gogayyar da take yi wajen ganin ta taimaka masa,shi sai yanzu ma kwakwalwar sa ta d’au charji amma kwanaki da d’azu gaba d’aya duk kishi ya rufe masa ido,tabbas everything is fair in love and war!’they are at war’ dan haka komai is fair kamar yadda ta fad’a dan ta had’asa da Munirat saboda su samu su yi achieving abunda suke so bai kamata ya dasa ayar tambaya a kanta ba wanda hakan ne farkon zargin nata da ya fara,tunda in komai ya yi daidai ya tafi yadda suke so ai sune da win.

Ahankali ya juyo yana jin tsananin tausayi da k’aunarta suna ratsa sa ya ce ‘’stand up’’
A ranshi yana mai cewa “inshaaAllah zai yi k’ok’ari ya goge tunanin’watak’il Kausar tana son Yashjub’ daga cikin zuciyar sa.But for last time akwai abunda yake son confirming ta yadda zai yarda da ita d’ari bisa d’ari.
Ganin ta k’i tashi ne ya sanya shi ya durk’usa ya kamota ya d’ago da ita tashi d’aya ya sakata a jikinsa yana mai bubbuga bayanta alamun rarrashi,sun jima a haka sai da ya ji ta yi shiru tukunna yace “Kausar one last question….na ga kina kuka sannan na ga hankalinki ya tashi kuma muna shiga da kika ga Yashjub da Manubiya kika juya za ki fita which means you can’t take it ba zaki iya ganin su a haka ba kenan!,inaso ki faiyyace mini dalilin reaction d’inki ta yadda komai zai tafi normal a tsakani na da ke.”

Da d’an fushi sakamokon tuno mata da abunda ya fi komai d’aga mata hankali da yayi tace “Yassir bani da lafiya amai nake ji shiyasa na yi deciding in tafi”
Kallon ta ya yi kafin yace’’amai kuma?….wanne irin rashin lafiya kike yi da zai baiyyana kishi da b’acin rai a kan fuskar ki?ko dai ba zaki iya tolerating ganinsu…’’

Turesa ta yi da dukkannin ragowar k’arfin da take ji tukunna ta juya a fusace ta nufi toilet…bin ta shima ya yi dan bai gama da ita ba yet.

Tana d’auko pts d’in ta juya za ta fita suka yi kicib’is da shi,kallon sa ta yi ta kamo hannunsa ta damk’a masa still tana kallon cikin idanunsa tace
“Bani da lafiya!”

Had’e girar sama da k’asa ya yi
kafin ya d’ago abunda ya ji ta saka masa a cikin hannunsa,sai da ya kai hannun nasa saitin fuskarsa kafin ya
janye idanunsa
a cikin nata
ya mayar kan tsinken.
Da mamaki k’arara kwance a kan fuskarsa yace
“What!!”
Sai kuma ya kalleta yace
“How?”

Cikin fushi tace
“Kut!!!tambaya ta ma kakeyi
‘How??’.“
Tsabar takaici kasa ma cigaba da tsayuwa tayi dan haka ta bangaje sa ta wuce.

Lumshe idanunsa yayi ya furzar da iska kafin ya bud’e ya juya da sauri ya bi bayanta.
Har ta kusan kaiwa bakin k’ofar d’akinta dan haka ya bi bayanta da d’an gudu ya cafkota ya juyo da ita.

Takaicine ya sanya ta fashewa da wani sabon kuka gwanin ban tausayi.
Tashi d’aya jikin Yassir ya sake yin sanyi,bai ma san lokacin da ya janyota ya sake rungume ta ba,yana mai jin tausayi da k’aunar.
Cikin muryar lallashi
yace “Haba Kausar,sai kace wata k’aramar Yarinya?
kar ki damu kanki mana just like last time wannan d’in ma za mu san yadda za mu yi da shi,plss ki daina kukan nan.”

Cikin kuka tace”Yassir ka cuceni!
Shikenan ni na zama sarauniyar zubar da ciki kenan???
kaf gidan nan
a kaff cikin y’an uwan ka mata
ko missing period babu wadda ta tab’a yi amman ni k’iri k’iri ka maidani karuwar k’arfi da yaji
saboda ni ba y’ar uwarka baceba ko?
Idan nace ‘A’a’ kuma
ka dasa ayar tambaya a kaina.”

Kamar zai yi kuka yace
“Not at all Kausar,kawai dama I was thinking ne”
shiruu ya yi
sai kuma yace
“Shikenan
I trust you now na fahimci komai komai ya wuce,na yi trusting d’inki daga yau inshaaAllah”

Turesa ta sake yi
tana kuka kamar ranta zai fita
da kyar ta iya cewa Yassir
what were you thinking before a kaina?”

Sake ruk’ota yayi
cikin sigar lallashi yace
“Na fad’a miki ki manta kawai”

A karo na uku ta sake turesa itama tukunna tace
“You have to tell me
me kake tunani a kaina da! Ba ya ga tunanin ka na bana sonka ba na kishin ka?what is it?”

Runtse idanunsa yayi ya d’an sunkuyar da kansa
tukunna ya d’ago ya furzar da iska ya bud’e idanuwan nasa sannan yace
“Okay fine!
Da Ina tunanin kamar kina son Yashjub ne.”

Da k’arfi tace
“What,sai kuma ta sake fashewa da kuka
kafin ta sa hannu ta kamo sa sai da suka isa k’ofar d’akin ta murza key ta bud’e tukunna tace
“Get out Yassir!
Tunda dak’ik’in tunaninka
da kishi sun rufe maka ido
ba na jin akwai abunda zan gaya maka kuma ka yarda da ni.Think what ever you want to think ban damu ba tunda duk bayanin da na yi maka ranar a d’akinka ba ka yarda ba
htta sirrin da Mommy ta gaya mana wanda ba kowa ake so ya ji ba duk sai da na gaya maka..amma shine still ba m yarda da ni ba??
shikenan!!
Ba komai.”

Ahankali yace “Kausar”

Cikin fushi tace
“trust is a very important thing Yassir taya ma za ka yi wannan tunanin a kaina?.
Baka san yadda ka yi hurting d’ina ba yau!
Just get out of my room”

Matsowa ya yi da sauri yai hugging d’inta yasa k’afa ya tura k’ofar ya rufe.

Ba yadda ba ta yi da shi ba
amman sam ta kasa kwatar kanta,dan haka ta fashe da wani sabon kuka.

Lallashinta ya shiga yi a chan k’asan zuciyarsa kuma yana daya sanin zarginta da yayi…

Sai da ya ji ta d’anyi shiru
tukunna ya cikata ya ce”na yi laifi
For the first time gashi na yi accepting na yarda na yi miki laifi,ki yi hak’uri
InshaaAllah ba zan sake ba
sannan daga yau ba zan sake dasa ayar tambaya a kanki game da komai ba I promise!
Duk abunda kika yi I’m going to trust you ko menene.
Pls Kausar forgive me”
Ya fad’i hakan ya na k’ok’arin durk’usawa.

Da sauri ta rikesa ta d’an girgiza masa kai…sake yunk’urawa yayi zai durk’usa dan haka tace
“Ya wuce ba komai”

Ahankali yace “thanks love..sosai sosai”
Sai kuma ya d’an kalli flat tummy d’inta yace”mu zauna sai mu yi magana ko?”

Jinjina kai kawai ta yi
daga haka ta wucesa ta isa
bakin gadonta ta zauna

Tana zama shima ya zauna
Ba tare da b’ata lokaci ba yace
“Yaushe kike so mu je asibitin??”

Sai da ta d’an d’auki lokaci tukunna tace”ba zan je asibiti ba,idan cikin ya kai wata biyar sai in fara zuwa awo
InshaaAllah”

Da sauri yace “Kausar pls
kar mu yi haka da ke mana!
Wacce irin magana ce wannan??”
Chapter 79 · 0% Book details