Sashe 8
Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashi d’aya hankalinta ya sake tashi ko sallamar da Yassira tayi mata batajiba
ji tayi kawai ta kashe wayar.
Zato zunubi amma tunani da zarginta tashi d’aya akan Yassir ya dira dan in ba shi ba ta san kaf gidan babu wanda zai yi wannan aika aikar tunda dai su babu wanda ya ke shigo musu gida,besides in ba black snake wanda suka tab’a yin fad’a da Yash d’in ba ta san Yash bashida wani abokin fad’a,yo yaushe ma ya dawo k’asar dududu.
To amman mai yasa Yassir zai yi haka
saboda kishi ko me?tabbas dama ta san yana zargin ta bai gama yarda da ita ba amma sam ba ta yi tunanin abun na sa ya kai har haka ba.
Dan haka dole ta tashi ta d’au mataki saboda al’amarin na Yassir ya fara zama wani abun daban…ba ta riga ta tabbatar ba amma muddin ta gama tabbatarwa shi ne to fa ba za ta zauna ta zuba masa ido
tana gani yake wasa da rayuwar Yashjub ba,shirmen na sa ya yi yawa……
A hankali Tana Jin kanta yana wani irin mahaukacin sarawa
ta nemi guri ta kwanta ta lumshe idanunta a take hawaye suka shiga sintiri akan farar fuskarta har ga Allah ba ta san yadda za ta yi da Yassir wanda ya zame mata k’adangaren bakin tulu ba,ga shi ba ta Isa ta yi wani abun ko ta tunkare sa da maganar ba tunda ta lura abunda ya ke expecting daga gareta kenan.
Tashi d’aya ciwon kanta ya sake hauhawa in banda sarawa ba abunda kanta yake yi shiyasa ta yi shiruu ta kwanta ta lumshe idanuwanta ……….
Ba ta dad’e da gama waya da su ba suka dawo gaba d’ayansu,kafin kowa ya shiga inda take Yassir ya shiga shiyasa su Yasira suka wuce d’akunan su kawai.
Yayi mamakin ganinta a kwance hankalinta kwance
amman dai fuskarta ta kumbura tayi jaa which means kuka tayi,k’arasawa yayi inda take ya d’an zauna a gefen gadon a hankali yace ‘’Kausar’’
Dakyar ta samu ta danne zuciyar da ta ke yunk’uro mata..a da da farko ta san tana son Yassir,da Yashjub ya dawo gaba d’aya sai ta ji Yassir ya fita a ranta dan tashi daya k’aunar Yashjub ta ci k’arfin komai a zuciyar ta,a yanzu kuwa tabbas ta tsani Yassir tsana ba ta wasa ba
dan ya yi mata kane kane ya tare gaba ya tare baya ya hana ta sakat sannan wannan zargin da ta fara akansa yasa ta sake jin tsanar sa ta nunku a zuciyarta kuma indai har zargin ya tabbata to ba ta jin akwai wanda za ta tsana sama da Yassir a kaff fad’in duniyar nan…
Dakyar ta taushi zuciyarta
ta d’an bud’e idanunta kad’an.
Suna had’a ido da shi ta yi murmushi
ahankali ta d’an mike daga kwancen ta jingina a bakin gadon ta ce’’Baby!’’.
Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Yassir har sai da ta kai sa ga sauk’e wata sassanyar ajiyar zuciyar kafin ya sake matsawa kusa da ita ya ruk’o hannunta
ahankali yana kallon cikin idonta trying to fahimci yanayin da za ta shiga
Yace’’ban gan ki a asibiti ba,Y??’’
K’ura masa ido itama ta yi
kafin da kyar ta samu ta iya cewa’’i have better things to do,besides ba kai ne ka yi accident d’in ba
balle in damu kai na.’’
Wani kalar murmushi ta ga ya yi kafin yace’’this means kin san Yashjub ya yi accident
but ba ki damu ma kije ki dubashiba????’’
Wani k’ululun bak’in ciki Kausar ta had’iye tana jin wani kalar takaici ya na sake lullub’e ta…ji take kamar ta yi tsalle ta damk’i wuyansa har sai ta ga ya daina numfashi tukunna ta cikashi.Zuwa yanzu ta gama tabbatar wa Yassir ne ya kwance tayoyin motar Yashjub especially ma da ta tuna
yadda jiya yak’i barinta ta kwana a d’akin shi dama tun jiyan taketa sak’e sak’e a ranta
tana so ta fahimci what he is up to….
‘’Don’t you care about him??’’
Ya sake jeho mata tambayar
still yana kallon cikin idonta
Wato saboda ya na so ya fahimci ko tana son Yashjub shiyasa ya yi wannan haukar kenan??ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba,kafin da kyar ta ce’’like i just said Yassir
I have better things to do.’’Ta fad’a mishi hakan tana
mai kawar da kanta gefe,a ranta tace’’dole ta yi k’ok’ari ta danne kanta ta yi tunani mai kyau da taku mai kyau dan in dai ta bari Yassir ya fahimci wani abun tou daga ita har Yashjub rayuwar su tana cikin hatsari,dan ta lura Yassir ya haukace’’……
Matsowa kusa da ita yayi sosai ya sa hannu ya kamo fuskarta ya juyo da ita saitin tasa daff da shi tukunna yace
‘’Why are u crying ,then?yanda idanunki da fuskanki ya yi it’s obvious kuka kika yi.’’
Lumshe idonta ta yi ta bud’e
tukunna tace’’ba ni da lafiya’’
Murmushi yayi tukunna yace
‘’Kausar!you better not be lying ‘’
Ahankali tace ‘’na ce maka bani da lafiya shiyasa ka ganni haka me ye ne yake damunka haka wai?akwai matsala ne?’’
ta yi mishi tambayar idanunta suna ciccikowa da hawaye.
Zuciya da abinda take so tashi d’aya sai tausayinta ya lullub’e sa,dan haka duk sai jikin sa yayi sanyi yahau inda inda,a hankali ta saki siraran hawayen nata suka shiga sintiri wanda ya sake yin tasiri ba kad’an ba a zuciyar Yassir….dama tun da ya shigo ya ganta hankali kwance ya d’an sak’k’o da kuma ta ce ba ta damu ba sai ya kawar da zarginsa a kan ta dama kawai ya yi mata tambayoyin ne saboda yanaso ya tabbatar ta yanda zai kawar da duk wasu zarginsa a kanta,kuma inshaaAllah daga yau ya kawar inshaaAllah ba zai sake d’aura ayar tambaya a kanta ba.
Ahankali ya jawota jikinsu ya shiga lallashinta a chan k’asan ransa yace’’Alhamdulillah’’dan ba k’aramin dad’i ya ji ba da ya fahimta kuma ya tabbatar da Kausar d’insa ba ta son wanin sa.Amman fa dukda haka ba wai zai bar Yashjub bane dan ko ba komai ya san in dai Yash ya na da rai to ba bu shi babu walwala saboda har ga Allah jin sa yake yi kamar a tsakiyar kansa,ko yanzun ma da kyar ya ke ta lallashin kansa yake tausar zuciyar sa da take ta faman tunzura shi akan ya je
yace zai kwana ya kula dashi
daganan ya samu ya k’arasa abunda ya soma.
Kawai dai ya san indai hakan
ta faru tou kamar ya baiyyana kanshi ne saboda shi zai fara zama suspect tunda shi ya kwana da shi, shi kuma ya riga ya san ba zai iya danne zuciyarshi daga yi masa kwab d’aya ba dan indai suka kad’ance daga shi sai Yashjub tou tsaf zai iya danna masa pillow a cikin baccin sa.
Shiyasa ya taushi zuciyar sa ya hak’ura ya bari akan gara ya sake sabon plan ta yadda ba za’a kama sa dumu dumu ba..
….
Tun kwana biyu da suka wuce Baba ya fara tantama akan ‘anya kuwa Baraka tana gidan Musbahu duba da yadda kullum yake tare da mai sunan baba tun safe har dare,shiyasa yau yana zuwa ya tambayesa…cikin nutsuwa da fahimtarwa suka yi wa Baba bayanin abunda ya faru akan batun Baraka dalla dalla sannan suka ce’’ ya yi hak’uri akan k’in gaya masan da suka yi dama suna so ya d’an huta sanann abubuwa su d’an yi sanyi tukunna,dan ba sa so hankalinsa ya tashi sosai a lokaci guda.’’
Shiruu kawai ya yi da farko kafin daga baya yace‘Allah ya rufa asiri’’daga haka ya ja bakin sa ya yi shiru yana kallon su Muhsin suna koya wa inna rik’e abu dan jikin nata Alhamdulillah anata samun improvement a cikin kwanakin da basukai sati d’aya ba.
Suna nan zaune gaba d’ayansu zaune,Ya Nafi’u ya kira ya Musbah yace’’yanzu sir Najeeb ya kira sa yake sanar masa’Yashjub ya yi accident yana asibiti driver d’insa ma har ya rasu.’’
Tunda suka ji Ya Musbah ya yi salati dama gaba d’ayan su suka juyo suna kallonsa ai kuwa yana ajjiye wayar suka hau tambayar sa’’me ya faru’’
abunda ya Nafi’u ya gaya masa shima ya fad’a musu idanunsa a kan Manubiya,ai kuwa hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba,ga mamakin su kawai sai suka ga ta fashe musu da kuka.
Murmushi kawai Baba ya yi
yana mai jin wani kalar kwanciyar hankali da nutsuwa su na ratsashi
dama yanayin yanda suke waya akai akai ya fahimci kamar itama tana son Yash d’in
yau kam ya tabbatar,shiyasa ya ji zuciyarsa ta yi k’al!Atleast ya san zai kai Manu gidan wanda itama take tsananin so.
Cikin d’an k’ankanin lokaci suka yanke akan Manubiya ya Musbah Muhsin da Jidda su fara yin gaba su je su dubo shi su yi masa ya jiki,dan haka aka fara shiri dan su samu su je da wuri shi kuma Baba ya ce ‘’in Aisha ta zo kamar yadda Nafi’u ya ce,sai ta zauna da Inna shi kuma sai ya taho da mai sunan baba in ya farka dan tun d’azu da suka shigo ya fara bacci,tare kuma da ya Nafi’un wanda yace yana gama abunda yake yi za su zo
.In ya so sai su dawo gaba d’ayansu a tare’,
ya fad’i hakan yana mai zaro kud’i daga aljihun sa ya mik’awa Jidda yace’’gashi su siyawa Yashjub d’in su ayaba da lemo a hanya’’.
Jikin Manubiya har karkarwa yakeyi,tun kafin a kowa ya shirya ita har ta shirya ta karb’i
address da room number da sir najeeb ya turo a wajen ya Musbah ta zura hijabinta ta d’au jakarta da wayarta ta tsaya musu a bakin k’ofa.
Girgiza kai kawai ya Musbah yayi,wanda hakan ya sanya ta d’an lura da zumud’in ta dan haka ta fara kame kame tahau wasa da bakin hannun hijab d’in ta,Jidda ma dariya tayi
kafin ta kalli Baba ta ce’’Baba dan Allah bara in kira Siyama sai mu je tare
Kamar Baban zai hanata
sai kuma ya kawar da wannan tunanin a ganinshi ai babu mahaifiyar Siyama a cikin case din iyakar da aka yi mishi dasu
Iyakar tsakanin shi da su Uncle da Baba Habu ne,shiyasa yace mata ‘’to’’ kawai.