← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 137

Sashe 65

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ya naga ka d’au hanyar gida?”
Muryar Yashjub ta katse masa lissafin sa
Sai da ya d’an d’au lokaci tukunna ya juya ya kalle sa ya ce
‘’Mommy ce tace in kai ku chan ku huta.Zuwa gobe sai su Yasira su je gaba d’aya a tayata gyaran gida dan ta san ba za ta iya ita kad’ai ba’’

Ba Manubiya ba hatta Yashjub sai da ya ji gaban sa ya yanke ya fad’i..shiruu kawai ya yi a ransa yace
“Allah ya rufa asiri”
Daga nan motar ta d’au shiru tsit kawai kakeji har suka k’arasa bakin mansion d’in aka bud’e musu suka shiga ba wanda ya sake cewa komai.

Tun kafin motar ta tsaya ya ga sun fito gaba d’ayansu
Har Kausar Ummi da Munirat..shine ya fara fitowa tukunna ya bud’ewa Manubiya gidan baya itama ta fito..kallon Kausar take yi tana mamakin kwalliyarta ta cikin glass d’in shiyasa ma ta kasa fitowa.
Gashi kayan jikinta k’anana ga hula ta d’aura a kanta amma ba ta cusa gashinta a ciki ba instead ta fito da shi duka yana reto gefe da gefe da baya ko k’aramin ribbom ba ta mak’ala ba ga wani irin high makeup da ta yi kamar wadda za ta je gasar saurauniyar kyau!
Ko ba a fad’a mata ba ta san saboda Mijinta ta yi wannan kwalliyar da shigar shiyasa ta kasa hana kanta jin kishi,dama tun d’azu a jirgi take jin amai da ciwon Kai ga zazzab’i yanzu kuma ganin Kausar ya sake b’ata mata rai shiyasa gaba d’aya ta shiga jinta wani iri sosai sosai.
Ahankali yake nazartar ta kafin yace”muje mana”
Ya fad’i hakan yana k’ok’arin ruk’o hannunta,gudun magana yasa ta d’an janye da style ta d’aga masa Kai alamun ‘to’
daga nan suka nufi inda dandazon su Mommy suke a tsatstsaye.

Ba abunda ya fi d’agawa Mommy hankali irin farin da ta ga Manubiya ta yi dan har wani d’aukar ido ta ga tanayi
Ta san sun yi mata ajiya a ciki
amma she can’t help it but to think ko dai cikine da ita,har Manubiya ta k’arasa inda take tsaye ta d’urkusa ta na gaida ita ba ma ta sani ba saida Baba larai ta d’an zungureta tukunna ta dawo cikin haiyyacin ta
Ahankali ta dafa kan Manubiya ta ce “lafiya y’ar albarka ya hanya?”
“Alhamdulillah”kawai Manubiya tace daga nan ta gaida Baba larai itama ta amsa mata da kulawa kafin ta mik’e ta nufi Ummi tana shirin durk’usawa Ummin ta rik’eta tace
“Sannu ya hanya”
cikin tsananin ganin girman matar Manubiya tace “Alhamdulillah”daga nan ta gaida ita sai kuma suka hau murna da hugging juna ita da su Yahanasu yayin da Yashjub yake chan suna gaisawa da su Mommy Baba larai tana tsokanarshi da ‘ya yi k’iba.’

Ko kallon Kausar bai yi ba
ko da ta matso ma tana kwarkwasa ta gaida shi bai amsa ba sai da Mommy tace’’Kausar fa tana gaida kai,”tukunna yace ‘’Alhamdulillah’’ba tare da ya kalle ta ba, dukda haka bata damu ba haka ta matsa kusa da shi sosai ta tsaya ana magana wanda hakan ba kad’an ba ya sake tunzura lissafin Yassir.
Sosai ran Ummi ya b’aci itama duba da yadda Kausar d’in ta matso kusa da Yashjub sosai
kuma Mommy ta rik’e masa hannu ta hanasa matsawa ana hira ana dariya it’s like so take ma Manubiya ta gani.
Shiyasa tun kafin Manubiyan ta juya ita kuma ta kamo hannunta suka yi ciki su da Munirat da Yahanasu.
Bata barta ma ta zauna a parlourn ba chan sama side d’in ta ta kaita har bedroom d’in ta tace “ta huta”daga nan ta cewa Munirat ta kawo
mata abincin da suka yi..
Sai dai a ga shishshiginta amman ba za a yi wannan cin kashin a gaban idanunta ta ta kyale ba
Dama tunda ta ji su Mommy sun dage a kan Yassir ya kawo su nan ta fahimci akwai abun da suke son yi….kuma ita har ga Allah girkin da Mommyn ta yi musu ba ta yarda da shi ba dan haka ba za ta bari ta ci ba shiyasa ta cewa Munirat ta kawo wa Manubiyan wanda su suka dafa.

Yashjub ya so su zauna a side d’in sa amman sai Mommy tace”tunda na kwana d’aya ne kawai su zauna a guest room gobe sai su wuce”
“To”kawai yace ba dan ya so ba dan 3 months ago Yahanasu ce masa ta yi ya zauna da matar sa kawai a uk har abada
In kuma hakan bai yiu ba to kar ya kuskura ya dinga favoring d’inta sannan ya d’an rage nuna mata soyayya a gaban su Mommy…..shima ya fahimci hakan kuma dama ya sa a ransa ba kwana kusa za su dawo d’in ba but no mattter yadda yaso ya dad’e ya yi kamar 2 years haka sai ya ji ya kasa kuma bazai ma yiu ba aiyyukan sa duk suna nan shiysa ya fara shirin dawowa to a wannan time d’in ne ma Daddy ya kira sa wanda kiran da ya yi masa da yanayin yadda ya yi masa magana da sanyin murya gaba d’aya ya kashe masa jiki duk abunda ya shirya ma zai fahimtar masa kuma zai yi a kan su Yassira gaba d’aya sai ya ji ba zai iya ba dan Daddy d’in sounds so disturbed it’s like Irin ya gaji da damuwa da cases d’innan tunda har ya sauk’o da kansa,kuma kamar akwai abunda ya taso masa yake damunsa maybe case d’in marigayiya…shine babba a ganinsa bai kamata ace shine zai saka Daddy a damuwa ko
ya k’ara masa damuwa ba..kwanaki ya yi masa wuta wuta yanzu kuma tunda ya sauk’o to Alhamdulillah shi kuma inshaaAllah ba zai taimaka wajen sake d’aga masa hankali ba,shiyasa ya yanke a kan zai yi ta addu’a kawai komai ya daidaita kuma inshaaAllah ba zai yi abunda Manu za ta kwana a ciki ba…

Baba larai ce tace “mu shiga ciki mana ku gaisa da Daddy a ci abinci ko?
Naga su Manubiyan ma har sun wuce.
Tun safe Mommyn naka take yi muku girki..babu wanda ya ci abinci ku ake ta jira”.

Murmushi ya yi ya kalli Mommy yace ‘’Thankyou Mommy’’
Daganan duk suka shige cikin parlourn Yashjub ya nufi chan sama wajen Daddy yayinda su Mommy suka fara rarraba idon neman su Manubiya
Da sauri Baba larai ta matsa kusa da ita k’asa k’asa tace
“To!Ummi ta yi sama da ita kuma in ba da kyar ba ta cika mata ciki da nata abincin kinga shikenan mun yi shiri da wahalar banza kenan….”
A zabure Mommy ta nufi sama d’akin Ummi.

Tun d’azu dama Ummi ta lura kamar Manubiyan bata jin dad’i dan haka suna zama da Munirat ta tafi d’ebo abinci ta kalle ta tace
“Baki da lafiya ne?”

Sai da ta d’an sunkuyar da kanta k’asa dan gaba d’aya kunyar Ummin take ji gashi ta hanata zama a k’asa kan kafet ta d’aura ta akan gadon ta d’are d’are
tukunna tace
“Zazzab’i nake ji da amai”

Wani kalar murmushi Ummi ta yi kafin tace “Sannu..
Inaga flight d’in ne ya ja miki hakan,akwai pottage na san za ki ji dad’in sa sosai yanzu Munirat za ta kawo sannu ko”

Ahankali ta jinjina Kai tace “Nagode Ummi”
Daganan ta d’auko wayarta ta shiga kiran su Innaa, tun a mota Jidda ta kirata tace mata sun iso
amma ita Jidda tana skul ta kira Innar kuma bata d’auka ba shine yanzu take sake gwadawa.

Ummi na cikin gaisawa da inna Mommy ta shigo…sai da ta basu mamaki sakamokon ganin ta a hargitse da suka yi,
dan haka sukayi sallama da Inna tukunna Ummi ta bata dukkannin attention d’in ta tace”ya na ganki a gigice ince dai lafiya ko?”

Tabbas zuwa yanzu Ummi ta fara kai Mommy bango da yanayin maganganunta masu harshen damo marasa respect.
Ba ta ita take ba yanzu
amman tabbas za ta samu lokacin ta soon .
Shiyasa kawai ta k’ak’alo murmushi da kyar tukunna tace “lafiya k’alau Ummi,
naga ban ganku a k’asa bane shine na biyo d’aukar y’ar tawa”.

Ita kanta Manubiya sai da ta ji bambarakwai dan yanayin kulawar da su Mommyn suke ba yau ta musamman ce saboda ko a waya idan za su gaisa da ita ba ta cika yi mata irin haka ba.

Murmushi Ummi ta yi tana shirin yin magana Munirat ta shigo d’auke da tray..cikin
tattausan lafazi tace
“Ai ni kam wai da har na yi shishshigi na sa Munirat ta d’ebo mata abinci,ki bari kawai ta ci anan naga duk kunya take ji ga gajiya”.

Jin jina Kai kawai Mommy ta yi daganan ta juya ta fita..tana fita ta hango Yashjub yana sauk’owa tare da Daddy.
Cikin sanyin jiki ta k’arasa suka gaisa da Daddy dama Yashjub d’in take nema ga kuma har da Daddy a kusa da shi dan haka a ranta tace “perfect’’.
Cikin sanyin murya tace
‘’Am ko za ka yiwa Manubiya magana ta fito mu je kuci abinci ,na gama had’a dining a k’asa Inata jiranku tun dazu’’

Murmushi ya yi yace ‘’ok Mommy.
Bara in kira ta tana d’akin Ummi ko?”

Jin jina kai ta yi kawai.

Daga haka ya wuce itama ta nufi k’asa Daddy ma ya wuce k’asan.

Yashjub yana shiga ya tarar da su Yahanasu suna ta faman k’ok’arin zuba mata abinci.
Sai da suka gaisa da Ummi dan d’azu su Mommy ba su bashi dama ba tukunna ya kalli Yahanasu da ta gama zubawa Manu abinci ta mik’a mata ta fara k’ok’arin bud’e d’aya kular.
Bai so zai ce wani abun ba dan ya san Ummi zata ji babu dad’i amman kuma Mommy ta yi masa magana kuma a gaban Daddy sannan ita da kanta aka ce ta yi girkin shiyasa kawai ya dake ya ce “Am Yaha!ko za ku sauk’o da ita da abincin k’asa ko?,basu gaisa ma da Daddy ba”

“Ok”kawai Yahanasun tace
Daga nan shi kuma ya juya ya fita dan baiji dad’i ba
Ummi zata ga kamar ya gwale ta ne.

Yana fita Ummi ta girgiza Kai kawai ta riga ta san ba yin kan sa bane ba.
Daga haka tace musu su sauk’a da abincin.
Chapter 65 · 0% Book details