← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 137

Sashe 116

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranar da na fara labour muka bata magani itama muka tayar mata da labour ta hanyar ba ta kwayar da ya bamu a ruwa ta sha ba tare da ta sani ba.
Tana shiga d’akin haihuwa gudun kar ta fahimci wani abun aka shak’a mata anesthesia aka yi mata cs
Kusan a tare muka haihu
Ita aka fito mata da Yashjub ni kuma na haifoki Likitan da nurse d’in da Baba larai suka yi sauri suka sauya aka fitar da ke a matsayin Y’ar da ta haifa ni kuma bayan y’an mintuna aka fitar da Yashjub aka ce na haihu.

Daddy ya bada rabin dukiya kamar yadda ya yi alk’awari amma fa ba ni da burin mallakar wannan dukiya kamar yadda nake da burin kashe Yashjub saboda kwata kwata ko fuskarsa ba na son kalla gashi aka tilasta mini hakanan Ina ji Ina gani na dinga shayar da shi.
Kwatsam!!ina ta shirye shiryen yadda za a yi in raba shi da duniya ba tare da kowa ya zargemu ba sai ga ciki a jikina cikin y’an biyu mai wahalar laulayi.
Tun cikin yana da watanni hud’u Baba Larai ta fara mafarkai marasa dad’i game da Yaron da zan haifa..Tabbas mun fahimci Namiji ne kam wannan karon ammafa Yaron kwata kwata bashi da albarka ga kuma mutuwa da zai yi wulak’antacciya idan har bai yi arzik’i ba!!! sannan duk abunda ya soma to ba zai yi albarka ba…hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba dan sai da jini na ya hau na kwanta a asibiti sau bakwai saboda wannan duba da Baba larai ta yi ta gano mini bala’i..sai da muka nutsu muka yi lissafi Sosai muka bincika tukunna muka gano Ashe asirin da muka yiwa Yashjub tun kafin ya zo duniya ne ya fad’a a kan Yassir tunda asirin an yi sa ne a d’an Khadija matar Imam kuma kinga nima sunana Khadija sannan ko bayan da muka fahimci abun bai kama Yashjub ba bamu damu mu yi wani abun a kai ba dan kwata kwata ba mu kawo cewa zai fad’a kan Yassir ba bayaga haka babu ma ta yadda za a yi mu karya abun saboda ba zamu iya nemosaba dan a babban ruwa mai tafiya muka jefa dan haka kinga la shakkah ba ma ya cikin Nigeria ya bi ruwa.

Babu abunda ba mu yi ba babu abunda bamu gwada ba amma idan muka yi aikin muka gwada in banda wasu sabbin masifu a kan na da babu abunda muke gani a tauraron Yassir amma ita d’ayar Yarinyar lafiya lau dan zuwa wannan lokacin mun fahimci twins ne.

Kamar kullum a wannan lokacin ma Baba larai ce ta kawo shawarar’mai zai hana mu yi hak’uri mu taushi zuciyoyinmu mu raini Yashjub tunda shi zai yi albarka in ya so idan ya girma ya gama tara abunda ya tara sai mu San yadda muka yi muka d’aura Yassir a kan dukiyar sa shi kuma mu kashesa komai ya dawo hannun mu in ya so sai Yassir ya kula da komai tunda ba Yassir d’in ne ya fara tara wa ba ta san komai zai tafi cikin sauk’i abun zai yi albarka dan shi Yassir d’in abunda ya fara ne dakansa ba zai yi albarka ba.inshaaAllah komai zai yi kyau.
Sannan idan hakan ta faru babu batun wulak’antacciyar mutuwa a Yassir tunda a yadda ta gani sai idan ya rasa komai ya rasa kowa tukunna wannan al’amarin
zai faru da shi.

Ko kad’an ban yi mata jayayya ba dan nima plan d’in ya yi mini d’arr bisa d’ari.
Dan haka muka tashi muka tsaya tsayin daka na danne zuciyata na ja Yashjub a jikina na kula da shi duk dan saboda y’ay’ana sai dai kuma tun lokacin da Yashjub ya kai shekaru 5 a duniya na fahimci kamar ma ya tsane ni!sam ba ya son magana ma da ni ba ya son shiga jikina baya jan y’an uwansa a jiki…
Gashi duk ciki mahaifinku ya fi son shi
Daga k’arshe ma Hajiya mama ta d’aukesa gaba d’aya ya koma wajenta…na so ya dawo a wannan lokacin amman a banza dan yadda Hajiya mama ta ga na d’aga hankalina na san shiyasa ita kuma ta ce ba zai dawo ba.

Yashjub tun yana zuwa mana
hutu sau 2 a shekara daga baya ya koma sau d’aya ko
bayan shekaru biyu daga k’arshe ma ya daina sai dai Daddy da su Yassir su je ni kuma a lokacin mun yi kacha kacha da su Hajiya mama tace idan ta ganni a inda take sai ta yi mini abunda ban tab’a tsammani ba.

Tun Yashjub yana shekaru 17 na so ya fara saka su Yassir d’in a jikinsa da suka girma suka yi wayo nan ma na yi masa maganar ya fara saka shi a business d’insa amma ya k’i na zo nace to ya bashi jari nan ma ya k’i gashi a lokacin na fahimci son kan da Daddy ya kuma yi a share na company d’insa shima
gashi shi Yashjub d’in ba ma ya nan ballantana in san yadda zan yi in yaudare sa ya ja d’an uwansa shi kuma asiri bai cika tasiri a kan sa ba kamar Khadija
Hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba da na ji kishin kishin d’in Na’ima ta ce wa Yassir Yashjub take so dan dukda cewa na san mun cire masa son mata da sha’awar su a rai amman kuma na san in dai har Na’ima ta gayawa su Daddy tana son shi tofa dole ya aureta kuma yau da gobe sai Allah na san duk abunda muka yi dole wata rana Na’ima ta iya samun ciki…Shiyasa muka k’arawa abun namu k’aimi gaba d’aya ya kuma tsanar mata sannan muka fara aiki a kan ya dawo a yi ayi ya d’aura Yassir da Yassira a kan komai na dukiyar sa mu samu mu kashe sa dan na yiwa kaina alk’awarin jinin khadija bai Isa ya rayu ya ji dad’i har ya yi aure ba,saboda yadda Yashjub da mahaifiyar sa suka d’aga mini hankali he don’t deserve to live
That is my revenge….

Kwatsam!! Sai kuma tauraruwar mace ta fara b’ullowa wadda Baba larai tace ita za ta kawo
k’arshena muddin muka bari aka yi auren….
Yo dama ai ko ina hauka Yash bai Isa ya yi aure ya haihu ya ji dadi sannan Yaro ya shigo cikin gadon sa ba….ga kuma maganar matar ma ta zo har da su kawo k’arshena shiyasa na tsani kuma bata son Manubiya kamar mutuwa ta!

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta kalli Yahanasu tace”yanzu na san kin fahimci dalilina na aikata duk wani abunda na aikata kuma inda ace ba na sonki ko ban d’auke ki a matsayin jinina ba Yahanasu da ba zan tab’a zama in faiyyace miki komai in bud’e miki cikina kamar haka ba!!
Na san na yi laifi na san na yi kuskure amma Daddynku shine ummulaba’isin komai da na fara aikatawa sannan da tafiya ta yi tafiya na san kin fahimci saboda Yassir da kuma ku na aikata ragowar abubuwan da na aikata.
Sannan Manubiya had’ari ce ga rayuwata shiyasa ya zame mini dole in….”

Cikin tarar numfashinta Yahansun tana wani irin kuka kamar ranta zai fita tace”Mommy babu ruwan Mannubiya da duk wani abu da ya sameki da kuma yake shirin samunki Ubangiji ne ya fara nuna miki k’arshenki!!…”
Wani irin abu ne ya rik’e mata zuciya da mak’ogaro dan haka ta yi shiru numfashinta ya tsaya da kyar ta samu ya dawo ai kuwa tashi d’aya ta mik’e ta kamo hannun Mommy ta fara janta sai da suka isa bak’in k’ofa tukunna ta bud’e ta had’e hannuwanta waje guda tace”dan girman Allah ki fita,ki fita kafin ki sa zuciyata ta buga!!!!”

Tabbas Mommy ta fahimci tarkon ta ya kama kurciya Yahansu ba za ta iya yin komai ba kamar yadda take ik’irari kuma yadda ta bud’e mata cikinta ta fad’a mata sirrin ta ta san hakan ma sake k’ulle Yahansun ta yi da jijiyoyin jikinta dan haka ba za ta iya yin komai ba.
Shiyasa kawai ta shafa fuskarta a hankali ta d’an goge mata hawayenta daga haka ta sa Kai ta fice hankalinta a d’an kwance dan tun d’azu da Yahansu tace’ guilty conscious zai addabeta idan ta fad’i abubuwan da ta aikata aka hukuntata’
Ya sanya ta fahimci all she needs to do shine ta sake nunawa Yahanasu itan fa itace mahaifiyarta kuma tana sonta daga nan ta san za ta yi silencing d’inta shiyasa ta bud’e mata cikinta saboda tana so ta ga ta yarda da ita kuma ta d’auke ta y’a.
Kafin ta gama fita daga shock ta dawo dai dai ita kuma InshaaAllah kafin nan da lokaci k’ank’ani za ta san yadda zata da su Daddy za ra san yadda zata yi
distroying d’insu gaba d’aya ta kawo k’arshen su kar ma su sake bata ciwon kai

Mommy tana fita da sauri Yahanasu ta mayar da k’ofar ta rufe k’irjinta yana dukan tara tara dan bayaga haushi da takaici har ga Allah zuwa yanzu kam tsoron Mommy take ji Anya kuwa Mommy tana da zuciya a cikin k’irjinta??ita da Baba Larai anya kuwa za su ga Annabi?ashe dama akwai mutane irinsu har yanzu a duniya?
A da ita tana jin haushin Mommy saboda abubuwan da ta yiyyi ashe ba ta ji duka ba ba ta san duka ba!!!!
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ta shiga ambato a cikin zuciyarta kanta yana wani irin sarawa…tabbas kamar yadda Mommy ta yi zato a yadda ta zauna ta bud’ewa Yahansu cikinta hakan ya sanya Yahanasun ta d’an ji d’arr sannan kuma ta yarda Mommy ta d’auke ta a matsayin y’a!!
Ba wai ta yafe mata abubuwan da ta yiyyi ba kawai dai hakan ya sanya ta sake fad’awa cikin duniyar tsoron tona mata asiri saboda ta san guilty conscious ba zai bartaba no matter what uwa uwace gara kawai ta barta Ubangiji ya nuna mata iyakarta…
Ba za ta sake da ita ba ba kuma za ta kula ta babu ruwan kowa da kowa kamar da dan tabbas Mommy ba uwar da zaka sake ka yi mu’amala da ita baceba,she is everything Bad!…..
Chapter 116 · 0% Book details