← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 137

Sashe 111

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har kusan shekara d’aya zuwa biyu Hajiya mama ba ta gano wata hujja da zai sanya ta ce Yashjub ba d’an Mommy bane saboda yanzun kuma yadda Mommyn take yi masa babu wanda ya Isa yace ba ita ta haife sa ba,kuma a wannan lokacin ba ta san Mommy da mugayen halaye ba,shiyasa kawai ta kawar da komai ta cire shakku ta cigaba da addu’a ta mik’awa Ubangiji lamuranta ta barshi ya yi ikonsa dan har yanzu zuciyarta ba ta daina yi mata wasi wasin ‘anya Yashjub dan Mommy ne kuwa!!?’Gashi ita Babba ce ba zai yiu ta tada husuma akan wannan gagarumin al’amari haka ba azo a yi bincike aga ba haka bane gashi Ubangiji da kansa yace “kar ka tsananta bincike”
Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru ta ci gaba da addu’a,A lokacin ne kuma Mai gidanta ya rasu mahaifin su Daddy dan haka zaman ta ya dawo Gidan Daddy tunda shine Babba.
Sai dai ko sati ba ta iya yi a gidan ba ta ji komai ya fita a kanta ta tsani gidan ta tsani jama’ar gidan hakan ya sanya ta koma Uk da zama.Dukda tana so ta d’an saka ido akan zaman Daddy da amaryarsa saboda a lokacin dukda Daddyn ba ya yiwa Amaryarsa abubuwa a gabanta amma ta fahimci akwai matsala sai dai kuma ba zata iya zama a gidan ba dan haka ta hak’ura ta tafi bayan ta had’a su su biyu Daddyn da Amaryartasa ta tambayesu Daddy yace mata babu komai ba fad’a suke yi ba.
Itama amaryar haka.

Bayan shekara biyu ta zo hutu,a wannan lokacin ne ta ci karo da layu da abubuwa a d’akin Mommy k’asan gadonta lokacin Yashjub yana wasa ya tura Abun wasan nasa a k’asan gadon ya isheta sai da ta zo ta duba ta d’auko masa dan su Khadijan duk basa nan sun fita barka…
Hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba saboda har da tsaka mai rai a cikin kwalba da abubuwa na tsafi kala kala ta gani a k’asan gadon Yarinyar da kusan rainon ta ma ita ta yi.
A lokacin Mahaifiyar Mommy itama ta rasu,kasancewar Hajiya Mama babbar k’awa ga mahaifiyar Mommy kafin rasuwar ta ya sanya ta ga ba laifi bane ba idan ta kirata ta zaunar ta yi mata magana ta kub’utar da ita daga kan Hanyar b’ata da halakar da ta d’auka wanda ba ya b’ullewa.
Dan haka suna dawowa ta nemi ganinta, sai da suka keb’e iyaka su biyu kawai tukunna tace mata“ta ga abubuwan da ta ajjiye a d’akin ta a k’asan gado”….nasiha sosai Hajiya mama ta yi mata tace “ ta rik’e Allah da addu’a shi zai sa Imam ya so ta ba wai tsafi ba,a duk lokacin da ka yiwa mutum tsafi ya so ka to fa idan abun ya karye tsanar da zai yi maka sai ta fi ta farko….”

Kan Mommy a k’asa lokaci da Hajiya mama take yi mata nasihar kuma daga ‘to’ sai ‘inshaaAllah’ kawai take ta cewa amma tana ji Daddy ya shigo tashi d’aya kawai sai ta fashe da kuka kuma ya yi tambayr duniyar nan ta k’i magana,ita kanta Hajiya mama kasa magana ta yi tsabar shock. Sai daga baya tukunna da kyar ta bud’e baki ta gayawa Imam d’in cewa “nasiha take yi mata akan biye biyen malamai”ita ba ma tace masa ta ga abu a k’asan gadon Mommyn ba!,
Ita Mommyn ce da kanta tace”ai Hajiya maman tace ta ga kaza ta ga kaza a k’asan gadon ta waye waye…”
Har da abunda Hajiya Mama bata ce mata ta gani ba duk sai da ta lissafo kaff abubuwan da suke a k’asan gadon nata
Tana magana tana kuka! kukan da duk wanda ya gani sai ya tausaya mata.
A take Hajiya mama ta ga alamun b’acin rai a fuskar Imam amma dai bai ce komai ba ya yi shiru,ganin Yarinya tana shirin shiga tsakaninta da d’anta ne yasa tace “to a je a duba”
A take with full confidence Mommy ma tace “ta yarda a je a duba”
Tun daga nan jikin Hajiya mama ya yi sanyi dan sai a lokacin ta tuna ba ta gyara katifar sosai ba dan ba zata iya ba ta yi nauyi,maybe Mommy ta gani sun gane an duba wajen watak’il sun kwashe….ai kuwa hakan ne dan ana zuwa in banda k’ura da akwatuna babu abunda aka gani a k’asan gadon Mommy.

Daddy bai ce mata komai ba,sai bayan kwana hud’u Allah kad’ai ya san mai da mai Mommy ta yi masa ta kuma fad’a masa tsabar an shanyesa hakanan ya zo yana ce mata wai”akwai wani Likita da zasu je ta gani idan mutum yana hallucination shi ake gani a kaff garin he’s the best”
a lokacin kacha kacha ta yi amsa ta koresa amma tundaga ranar daga ta ga k’adangare a d’akinta sai ta ga maciji kuma idan ta je ta tattaro mutane aka zo aka duba ba’a ganin komai! Hakanan za ayi ta kallonta ana mata kallon tab’abb’iya.
Ganin Mommy tana shirin haukatata ne ya sanya ta tattara kayanta ta d’auki Yashjub tace zai je ya yi musu hutu ta tafi da shi,dan abunda Mommy ta yi mata ya sanya ta fahimci tabbas za ta iya aikata fiye da chanjin Yaro ma.Tun da ga lokacin ta san yadda ta yi ta d’auke Yashjub gaba d’aya daga gabanta dan indai harshashenta daidai ne to kuwa ta san tsaff Mommy zata iya cutar da shi ko ma ta kashe sa,tunda indai saboda dukiya ne ta musanya Yaran to kuwa bata ga reason d’inta da zai sa ta barshi a raye ba yanzu dan yanzu kam dukiya ta dawo hannunta,ita da su Yassir………

Yanzu kuma da Mommy ta tura su Yasira suka zubar wa da Manubiya ciki hakan ya sake assasa zarginta ta fahimci komai,shiysa ta cewa Daddy ya barta a gidan su yi bincike a kanta sosai saboda tana so ta gano gaskiyar lamari da kuma duk wasu abubuwan da ta aikata a b’oye su samu evidence a kanta ta yadda za su fi hukunta da hujja, dan tabbas ta san Mommy ta dad’e tana cutarsu ba tare da sun sani ba..to shi kuma Daddy gashi yanzu ya sake k’ak’abawa Yashjub Kausar.
Ta san ba laifin su bane ba amma she can’t help it dole ta fusata saboda abun ya tab’ata sosai.Dan Auren Kausar da Yashjub kamar an sake kafe Mommy a cikin zuriarta ne….

Sallamar Junior ce ta katsewa Hajiya Mama tunanin da take yi,
A hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ta kallesa tace”ba sa gidan ko?”
Jinjina kai ya yi yace”driver d’insa na samu yana tartare kayansa yace mini wai an sallameshi ne saboda Yash d’in yace masa “sun tashi daga gida”
Yau da asubah wai ya kaisu hotel d’azu kuma ya je ya d’aukesu ya kaisu airport,yace bai san jirgin Ina suka bi ba.

Ajiyar zuciya ta sauk’e tace masa”ba ni wayata”kawai.
Yana mik’a mata ta nemo number Daddy ta danna call ta kara a kunnenta.
Ko gaisuwarsa ba ta amsa ba tace
“Yashjub ya tafi ba ya nan,ya turo mini message ya gaya mini abunda Khadija ta je gidansa ta yi Jiya,yace min dan Allah kar a nemesa.
Dan haka Ina mai baku umarnin kar wanda ya bibiyesa kamar yadda ya buk’ata,
ku bar shi ya huta da bala’in Khadija da y’ay’anta.
Ka ja mata kunne ka jawa su Yasira kunne sannan ka gaya wa d’an uwanka shima ya sani.”
Tana gama fad’in haka ta kashe wayar ta ajjiye a gefe zuciyarta tana wani irin tafarfasa.

Daga wajen Hajiya mama direct gida Yahanasu ta nufa dan tana son magana da Mommy yau kam ba za ta yi shiru ba!abun ya yi yawa.
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 40
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

A d’akin su Yadira ta same ta ita da su suna hira…
Tana shigowa duk suka d’ago suka kalleta sai kuma suka d’auke Kai babu wanda yace mata ci kanki hakanan suka ci gaba da hirar su,Mommy tana shirin yi mata magana ita Yahanasun ta riga ta ta hanyar cewa”Ina so za mu yi magana!”
Sai da gaban Baba larai ya yanke ya fad’i dan in ba da kyar ba a yadda ta ga Yahanasu yau kam tabbas za ta iya fasa mata kwai a wajen Mommy kuma ta san Mommyn za ta ji haushinta.
Kallon Yahanasu Mommy ta yi kafin ta d’an kalli Baba larai sai kuma ta mik’e ta nufi Yahanasu n ba tare da ta saurari
Yusra wadda take cewa”eh lallai rainin hankali ma kenan.”ba.

Duk idanu suka zuba musu Baki sake har suka fice daga d’akin.

Side d’in Mommy suka nufa suna shiga Mommyn ta kalleta tace”ya aka yi ??Yahanasu”.
Har ga Allah ta san bai kamata ta dinga jin haka game da uwar da ta kawota duniya ba amma she can’t help it!
Wani Irin haushi da takaicin Mommy take ji,ba ma ta jin za ta iya tsayuwa su yi wata doguwar magana dan haka cikin k’aguwa da son barin inda take ta d’an matso kusa da ita tana kallon cikin idanunta tace”ki cewa Yashjub kin janye maganar tsinuwa sannan ki daina treatning d’insa da tsinuwa idan ba haka ba wallahi tallahi sai na gaya masa cewa ‘ba ke ce kika haife sa ba’!”.

Wani irin zabura Mommy ta yi jikinta ya d’au karkarwa gaba d’aya ta fice a haiyyacinta tashi d’aya fuskarta tayi jazur.
Chapter 111 · 0% Book details