← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 137

Sashe 115

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yadda na fita daga haiyyacina sai da ya bawa mahaifiyata da Hajiya Mama tsoro amma mazajensu suka tsawatar musu aka ce a rabu da ni hakanan sai da na gama shan wahala imam ya gama cin amarcinsa tukunna Abban mu ya ce in koma tare da zazzafan warning d’in idan har ya ji case ya taso daga waje na to na bar Imam kenan har abada ba zai bari in koma gidansa ba.
Ina mutuwar son Mijina ba zan tab’a iya rayuwa babu shi ba gashi ba zan iya zama da kishiya ba shiyasa na shiga tsaka mai wuya na rasa abunyi na rasa tudun dafawa
A wannan lokacin ne larai ta dawo hannun Mahaifiyata da zama (matsayinta na y’ar uwar mahaifiyarta)saboda an samu matsala da ita a k’auyen su an d’aura mata sharrin maita.
Itama tana da damuwa nima Inada damuwa shiyasa muke zama muke tattaunawa…Larai ta tausaya mini sosai haka kurum da na zo komawa tace Tana so za ta biyo ni.
A wannan lokacin da kyar su Abba suka amince saboda Larai a k’alla ta bani shekaru sha biyar kuma suna so in je in zauna lafiya ni kad’ai in yi hankali kar mu je da larai in ga mu biyu ne in yi rashin mugunci..amma sai mahaifiyata tace ba komai mu je kawai saboda ta ga mun shak’u muna d’ebewa juna kewa sannan tunda Larai ta zo ba mu sameta da wata muguwar d’abi’a ba in banda addini da sanin ya kamata da muka santa da shi.
Haka nan aka tambayi Imam ya amince muka tafi gidana tare da Baba larai.
A ranar da na koma ma Imam ba a d’akina ya kwana ba,ko kallona ba ya son yi sai bayan kwana hud’u ya kiramu ya raba mana kwana Akan za mu dinga yin kwana uku uku ni da Abokiyar zama na.
Sai da girki na ya zagayo sau hud’u tukunna ya fara kwana a cikin d’akina saboda da a parlour yake kwana,ko da ya fara kwana d’akin nawa shima kuma babu abunda yake shiga tsakanina da shi sai dare wajajen 12 zai shigo Idan aka kira assalatu kuma ya fita da ga nan ba zan sake saka shi a idanuna ba sai wani daren a cewarsa aiki ya yi masa yawa!
Da gaske na san ba ya gidan tun safe har dare amma kuma sai ranar girkina ne ya ke yin scarce dan duk ranar da aka ce miki yau girkin Khadija ne to tun kafin Magrib yake shigewa d’akinta ba abunda yake fito da su sai sallah da cin abincin dare da ake yi tare daga sun yi isha ya kira ta ba kuma zan sake ganinsu ba sai washegari,haka nan zan yi ta jin hirarsu yana dariya yana raha.
Abun ya ishe ni gashi ban Isa yin rigima ba na san tsaf su Abba za su raba auren ni kuma ba zan iya rayuwa babu shi ba shiyasa na yanke shawarar kashe kaina kawai!!!!…
ranar da zznyi abun Allah ya taimakeni na d’aga kwalbar fiya fiya kenan zan sha Larai ta shigo ganin yadda na firgita ta fahimci ba ni da gaskiya aikuwa tun kafin ta gama dubawa ta gane menene a ciki.

Hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba dan haka ta fito min a mutun k’iri k’iri tace min Itafa ta biyo ni ne saboda tana so za da taimaka mini..
Ba ta b’oye mini komai ba tace a kwai wani boka a k’auyensu mutumin tun yana zuwa mata a mafarki har ta gano location d’insa a wata bukka chan a cikin daji ta je..nan yake sanar mata tun ranar da aka haifeta ya san dama itace za ta gaje sa…
Tun bata d’auki abun serious ba har ta d’auka!!!
bata da uwa sai matar uba dan haka bata yi shawara da kowa ba ta biye masa! ba a yi wata d’aya ba ta koyi kusan komai ya kokkoya mata abubuwa yace ta rik’e da kyau hannunta yana da zafi fiye da zaton mai zato
Akan wata k’awar su da suka yi fad’a ta fara gwadawa matar har yau tana nan a k’auyen su ba ta gani,daga nan sai ta gayawa babbar k’awarta…tun daga ranar duk wani abu da k’awar take so sai da ta yi mata aiki a Kai ta samu!!
A b’oye suke yin abun kuma daga ita sai waenda ta yi trusting shiyasa abun bai baza gari ba.
Amma ta ce mini abu d’aya ne har yau ta kasa yiwa kanta aiki a kai shi ne mijin aure dan ko da ta koma wajen bokan ya koya mata duba da ta duba ranar aurenta ta ga ‘babu!’ hakan bai sa ta yi giving up ba hakanan har gobe take neman mijin aure ido a rufe amma babu shi babu alamarsa.
Ragowar k’awayenta da k’annen k’annen k’awayenta duk sun yi aure kuma ba laifi sun rik’e mata sirrinta ba su fad’awa kowa ba,Mutuwar wannan boka itace ta tona mata asiri dan da ya kusa mutuwa sai ya raba sunanta ma clients d’insa to ta hakane da wata mata ta zo wajenta ta sa ta yiwa d’an kishiyarta asiri ya yi ta rashin lafiya d’aga k’arshe Yaron har ya zo ya rasu..shine fa da bincike ya yi bincike aka ganota aka ce za a k’onata a k’auyen ai mayya ce tunda gashi da ma gata babu miji kuma zan iya ce miki kaff k’auyen mu har yau ba ayi mai kyan larai ba shiysa su kuwa suka ce mata mayya.

Ina gama jin labarinta ko wasi wasi ban tsaya yi ba na amince da tayinta muka fara aiki babu dare ba rana a kan Khadija da Imam.
Ba a yi sati d’aya ba kusan gaba d’aya hankalin Imam ya dawo kaina yaddda yake treating Khadija nima haka yake treating d’ina sai dai kuma ni kaina na san soyayyar Amaryarsa ta daban ce duba da yadda ba ya kishi na kamar yadda yake kishinta dan haka muka sake zage damtse aiki ba dare ba rana ga kuma kissa da muka bawa mahimmanci,dan ko
wani abun aka yi sai dai in shige d’aki in yi kuka in goge daga ni sai larai ba ma tab’a bari wani ya ji ko ya gani…

Haka kurum kwata kwata sai na kasa d’aukar ciki.
Hankalina bai gama tashi ba sai da Imam ya kwashe dukiyar sa gaba d’aya ya damk’awa d’an cikin anaryarsa !!!
dama chan ba so nake yi Yaron ya zo duniya ba saboda Larai ta ce mini tabbas Namiji za ta haifa…dan haka Ina jin wannan batun na jajirce na dinga yiwa Larai kuka har sai da ta taya ni muka kashe Yaron tun yana ciki saboda ita Larai ta ce za ta yi komai amman banda kisan Kai dan shi ya rabota daga garinsu ya kusan tona mata asiri bayaga haka ita har ga Allah ba ta son yin kisa..to kukan da na dinga yi mata da kuma zancen raba dukiya da ta ji ne ya sanya ta biye mini a wanchan lokacin.

Tun daga nan muka k’ara k’aimi akan asirin da muke yiwa Khadija akan ta bar gidan Imam,mu bata ta ci ta sha mu zuba mata a ruwan wanka amma sam abu ya k’i yin tasiri a kanta kwata kwata ba ta ma da shirin tafiya,abun yana kama ta ba wai ba ya kama ta kwata kwata ba kawai dai ba ya yin tasiri a kanta.

A kwana a tashi a haka har muka samu ciki a tare ni da ita…
Tunda muka samu ciikin Larai take aiki Akan ni in haifi Namiji ita kuma ta haihu babu rai kamar yadda ta yi na farko…cikin yana yin watanni biyar Larai ta fahimci Tabbas fa Khadija sai ta haihu kuma Namiji za ta haifa sannan Yaron mai tsananin albarka ne dukkannin abunda ya saka a gaba sai ya cimma kuma attajiri ne mai masifar kud’i sa’a da nasara ta ko wanne angle na rayuwarsa!.
Sai da na suma a tsaye dan hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba saboda a ranar ne na lab’e musu na ji Imam d’in yana sake damk’awa cikin jikin Khadija dukiyar sa kamar yadda ya yi a na farko ita kuma tace ba zai you ba shine yace mata to a cikin mu ni da ita duk wadda ta haifi Namiji ita za a bawa shiyasa na nufi wajenta a hargitse dan na San idan muka yi kunnen doki tsaff Imam zai yi son kai.
Shiyasa na nufi wajen larai direct mu samu mu tattauna ita kuma ina shiga
shine ta tare ni da wannan zancen….
Da kyar sai da Larai ta yayyafa mini ruwa tukunna na dawo haiyyaci na da kyar.
Ganin Ina shirin had’iyar zuciya in mutu ne ya sanya tace mini Y not mu musanya Yaran ni in karb’i mai albarkar..tashi d’aya tun kafin ta k’arasa na k’i amincewa na ce kawai a cigaba da aiki a kansa ta yadda ba zai yi albarka ba kuma ya yi rayuwa mara dad’i mara nasara ya mutu wulak’antacciyar mutuwa,tunda mun riga mun san sai fa ya zo duniya.

Wani babban tashin hankalin saida na yi scanning na tabbatar ni mace zan haifa saboda ban tab’a kawowa zan haifi mace ba duba da yadda muka dinga aiki a akan in haifi Namiji.

A wannan lokacin ma Baba larai ce ta sake bani shawara kamar farko a kan mu musanya Yaran idan bayan mun haihu an bayar da dukiyar idan ma kashe Yaron za mu yi sai mu yi tunda dai Yaro yana a hannunmu ai tsaf za mu iya yin kome muka ga dama sab’anin yanzu da yake a ciki.
Tashi d’aya na amince dan na gamsu kuma na fahimta…tun a lokacin muka san yadda muka yi muka siye likitan da muke zuwa asibitin wajensa ta hanyar yarda da shi da Baba Larai ta yi bayan ya fad’i mana hakan kawai yake da buk’ata daga garemu.
Chapter 115 · 0% Book details