← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 137

Sashe 113

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai yanzu Mommy ta iya tsayar da kukanta da kyar tace”Yahanasu dan Allah kar ki ce kin tsane ni! Komai da kika ga na yi wallahi duk na yi ne saboda ku!”
Cikin d’an d’aga murya Yahanasu tace”saboda ke dai Mommy!duk abunda kika yi saboda kanki kika yi!!!.
Mommy kina kallo fa tun Ina y’ar k’arama ko jama a idan na gani kuka nake yi hakanan na tsani komai na tsani kowa nima mutane suka tsane ni,
Kina gani yadda aka dinga yawo da ni k’asashen waje dan a gano matsalata na dinga shan wahala daga k’arshe aka ce depression gareni lokacin ko shekaru sha biyu nan Kai ba amma mommy ba ki yi motsin komai ba.
Sau nawa ana fasa d’aurin aurena kin san bani da kowa ba ni da komai amma Mommy haka kike murzawa idanunki toka ba kya zuwa ki dad’e da ni ki ji ainihin matsalata saboda kar a zargeki kar asirinki ya tonu,
a gaban idanunki su Yasira suke yi mini duk wani kalar cin kashi amma sai dai ki zuba ido kawai idan anyi sa’a shine za ki ce musu su daina amma ba ki tab’a tsawatar musu ko kuma ki tsayamini ba.!
Ta ina hakan ya zama ba selfishnesse ba???ta ina hakan ya zamo duk a ta dalilin neman farin cikina ne????”
Yahanasu ta yi mata tambayar cikin d’aga murya.”
Cikin share hawaye ta sake cewa”kuma ko tsafin ma da kuke tunanin shine ya yi tasiri a kaina ba ki tab’a yunk’urin gyarawa ba despite duk wannan wahalwahalun da na sha a rayuwa amma a haka kike tunanin idan kika ce mini ke mahaifiyata ce a gaba zan karb’eki in yafe miki saboda kina tunk’aho kin yi mini asiri ko?”.
Ba ta jira Mommyn ta bata amsa ba tace”Never!!!”
Sannan ta d’aura da cewa”Mama Khadija itace mahaifiyata har gaban abada shiyasa kika ga kawai na zuba miki idanu ban tab’a tunkarar ki da komai ba saboda ban d’auke ki uwa ba!
kamar yadda ba ki damu da ni ba nima haka ban damu da ke ba, na san a baya a lokacin da na ji maganganunku na shiga tashin hankali ga k’arancin shekaru ga kuma no one to talk to amma believe u me wallahi wallahi Mommy yanzu abun ba ya gabana. Alhamdulillah I ‘ve move on Ubangijina ya yaye mini damuwa.”
Cikin sake matsowa daff da ita tana kallon yadda take kuka billhakki da gaskiya tace”Dan haka Ina mai sake gaya miki ki janye maganar tsinuwa sannan ki kirawo Yashjub ya dawo gida cikin family d’insa if not tabbas Mommy za ki yi mamaki na saboda a yadda na ke jin haushi da takaicinki tona miki asiri its the least I can do a halin yanzu.”

Dai dai nan Baba Larai ta turo k’ofar ta shigo a d’an hargitse!

Kallonsu ta yi kamar yadda suma suke kallonta,ta riga ta san Yahanasu ta gama fasa kwai duba da yadda Mommy take kuka kamar ranta zai fita amma ba ta wannan ta ke ba tukunna dan haka ta kalli Yahanasu tace”D’an bamu guri!”
Daga haka ta ja hannun Mommy suka nufi bedroom d’inta.

Had’e rai Mommy ta yi kamar ta turje ta k’i binta sai kuma kawai ta rabu da ita ta yi mata shiru dan tsabar mugun mugun takaici da haushin Baba larai d’in ma ya sanyata ta kasa cewa komai.
Suna shiga Baba larai ta turo k’ofa ba tare da ta damu da yanayin Mommyn ba tace”an yanka ta tashi fa!babu aure tsakanin Kausar da Yashjub!..”
Ba ta jira Mommyn ta tambayeta k’arin bayani ba ta d’aura da cewa”kin san ai kawar musu da lissafin duk wani abun da zai sanya a fasa auren nan muka yi dama,shiyasa kwata kwata ba su yi tunanin ‘ba fa a d’aura aure da ciki ‘ ba.
Ni kaina ban sani ba sai yanzu da na fito zan zo nan na ji suna maganar Abhi da Daddy..wai har wani babban malami suka tambaya ya tabbatar musu da cewa ‘ba a aure da ciki!’
Ban ji bayanin nasu sosai ba dan k’us k’us suke yi a chan corridor na babban balcony kamar harda Hajiya mama suke maganar ta waya,shiyas….”

Cikin katseta Mommy tace”Larai me yasa kika b’oye
mini batun Yahanasu???”
Cikin rashin jin dad’i Baba Larai tace”kash!!!
Ki bar wannan maganar za mu yi ta amma ba yanzu ba yanzu mu ji da wannan ba mu san wani step su Daddy za su d’auka next ba ya kamata mu yi musu shigar sauri!”.

Cikin daka mata tsawa Mommy tace”ni kuma wannan maganar nake so mu yi dan haka ki amsa ni idan na ce miki me yasa kika b’oye min batun Yahanasu sannan me da me kika yi mata? Har ma da ni kaina tabbas kin yi mini abu dan haka ina son jin komai a yau a yanzu ba sai anjima ba idan ba haka ba wallahi za ki sha mamaki na!!”

Numfashi Baba larai ta fesar kafin tace”shikenan tunda kin dage sai kin ji!
Duk abunda na lissafa miki nace ce za mu yi mata shi na yi…”
Cikin tarar numfashinta Mommy tace”Sannan nima kika d’auke hankalina daga kanta ko?saboda akwai abubuwan da kika saka ni na yi kika kuma bani na ci duk sai yanzu kwakwalwata take fassaramin ma’anar su sannnan tun da na yi har yau ban k’ara tunanin fad’awa Yahanasu gaskiya ba!
Dan haka ba na son k’arya da b’oye b’oye larai!! Inaso ki gaya mini gaskiya tun rai na bai gama b’aci da ke ba!!!”.

Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace”Mommy gani na yi kina shirin tona mana asiri ni da ke kina shirin kaimu prison saboda muddin Daddy ya aan mun musanya Yara to
duk wani Abu da muka yi sai ya bnciko ya fito kowa ya gani a hankali a hankali k…”
Marin da Mommy ta d’auke ta da shi ne ya sanya ta yin shiru ta zuba mata jajayen idanuwanta cike da mamaki da shock.

Cikin fushi bak’in ciki da b’acin rai Mommy ta fara magana”a duk tsawon tarayyata da ke ban tab’a ce miki ki je ki yi gaban kanki ki yi kutse cikin rayuwata ki yanke hukuncin da kika ga ya dace miki ba! A tunani na shelter abinci da gatan da na yi miki ya ishi ace kin yi hankalin respecting d’ina da decision d’ina ba tare da kin yi mini shishshigi ba.!”

Cikin fushi sosai itama Baba larai d’in tace”Khadija ni kuma a tunani na na wuce wacce za ki ajjiye hakanan a cikin gidan ki tana yi miki duk abunda kike so kawai kamar wata y’ar aikinki,a tunani na ni yayarki ce shiysa har na yi miki shishshigin da kike magana a kai na yanke hukuncin da na tabbatar it’s for your own best!
Amma tunda duk irin rufin asiri da abubuwan da na yi miki tsawon shekaru sama da talatin duk ba ki gani ba yau ta kai har kin d’aga hannu kin Mareni shikenan!!!ba komai Allah ya had’a fuskokinmu da alkhairi..
Daga haka ta juya ta nufi k’ofa taana tsammanin Mommy za ta tsaida ita amma har ta fice daga d’akin Mommy ko tari ba ta yi ba.

Za ta nemo ta amma bayan ta tafi su daidaita su shirya dan tabbas
Yau kam ba za ta tsayar da Larai ba wallahi,sai ta nuna mata abunda ta yi ba ta kyauta mata ba ta yadda gobe ba za ta k’ara ba,kalli yadda ta saka k’iyayyarta a cikin zuciyar Yahanasu ta dalilin makircinta sannan gashi kwata kwata Yahansun ma ba ta k’aunarta sab’anin yadda Baba larai d’in tace Yahanasu ba za ta iya ko jayayya da ita ba! A tunanin ta aikinsu ne yake ci da ta ga Yahanasun shiru shiru ashe tsana da haushinta ne ya cika mata zuciya shiyasa ta ke yawan yin shiru ba ta kulasu.

Sai da ta tabbata Baba larai ta fice da ga side d’inta gaba d’aya tukunna ta fito daga bedroom d’in nata!kamar yadda ta yi zato ba ta tarar da Yahanasu ba dan haka ta zauna ta yi shiruu ta shiga lissafin ta hanyar da za ta bi ta daidaita tsakaninta da Yahanasu.
Ta fi minti ashirin a zaune su Yasira suka shigo a mugun hargitse suna cewa”ta zo
ta hana Baba Larai tafiya,ga ta chan ta had’a kayayyakin ta tsaff!tun d’azu suke lallashinta amma ta kafe Akan Itafa sai ta tafi kuma sai kuka take yi dan Allah ta zo ta tsayar da ita ta lallasheta maybe Daddy ko Hajiya mama ne suka yi mata wani abun.
Mik’ewa kawai Mommy ta yi ta fad’a cikin bedroom d’inta ta kullo k’ofar wanda hakan ya sanya suka
fahimci matsalar daga wajenta ta taso kenan dan haka kawai suka sauk’a da niyyar su je su ji da Baba larai first tukunna su dawo wajen Mommy su ji dalilin fad’an nasu sai dai suna sauk’a suka tarar da su Yasmeen suna shigowa cikin parlourn suka ce ta riga ta tafi jaka d’aya ma ta samu ta tafi da ita dan sun rik’e ragowar sun hanata ita kuma ta tafi kawai ta bar musu.Sun so su bita amma ba wani Napep d’in nata kuma a baki baki ta zauna ta k’i basu access har aka ja aka yi gaba,kuma kafin su shigo su d’au mota sunsan sun riga sun b’acewa ganinsu……

Duk wannan dramar da ake yi su Daddy suna jin su suka manna musu hauka daga k’arshema garden suka fice suka ci gaba da tattaunawarsu….Daddy ji yake kamar ya fi kowa farin ciki a ransa kuwa addu’a yake yi in shaa Allah Baba larai ta tafi ta bar gidansa kenan har abada next kuma Mommy ce!….Hajiya Mama ta ji dad’i da suka kirata suka gaya mata,tana fushi da su shiyasa yanzu ma kamar d’azu da suka kirata suka gaya mata zancen aure ba ta biye musu ba kawai dai tace”a ci gaba da addu’a”
daga haka ta kashe wayar tana jin sanyi a ranta,in shaa Allah k’arshen Mommy ya zo
kenan sannu a hankali za ta gani ne.
Har yanzu mamakinsu take yi tana mamakin yadda ita kanta su Mommy suka goge mata hadda!!amma ba komai ai gashi nan sun fara gani tun yanzu,kad’an ma suka gani in shaa Allah.
Chapter 113 · 0% Book details