← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 137

Sashe 91

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun a wajen kai amarya Yusra ta kira Ya’isha tace”to fa babu abunda aikin Baba larai ya yi dan ga Najeeb da Siyama nan kamar za su cinye juna!”
Dabass!!!haka Ya’isha ta zauna a kan kujerar parlourn Mommy sai kuma hawaye suka fara bin fuskarta…
Da mamaki Mommy da Baba larai waenda suke cikin tsananin farin ciki suka shiga kallonta don yanzunna ta dawo daga ganin Abbakar take ce musu”Da farko ya d’an so ya yi zurfin ciki amma daga baya ya amince d’ari bisa d’ari it’s like ya ma fi su son mutuwar auren Manu da Yash d’in,kuma yace’ba ya buk’atar sisin kobo kawai su kular masa da mahaifiyarsa su biya duk wasu kud’ad’en asibin ta.”
Hakanan suna ta murna ita da su to kuma me ya saka ta kuka tashi d’aya haka…
Mik’ewa Mommy ta yi ta k’arasa inda take ta shiga tambayarta,da kyar ta iya ce mata”ai Najeeb da Siyama aka
gani tare har yanzu suna tare ba su rabu ba….”
Sai kuma ta mik’e ta fice da sauri tana kuka.
Shiruu Mommy ta yi ta fad’a duniyar tunani,har ga Allah tana mutuwar son Najeeb ya auri Ya’isha gashi abun na Y’an matan nata xuwa yanzu ya fara damunta..Jiya ta ga d’aurin auren d’an k’awarta wanda suka shirya ita da k’awar tata a kan za a had’asa shi da Yasira,tsabar abun da munafurci ko gaiyyatar ta bikin ma ba a yi ba sai kawai d’aurin aure ta gani….
“Ki kwantar da hankalinki,inshaaAllah duk za su yi aure,Najeeb kuma shima ki barni da shi bari mu fara gamawa da Manubiya tukunna”
Muryar Baba ta katse mata tunaninta.
A hankali tace”Baba larai idan kuma ya kai kud’i kafin a gama da Manubiyan fa?”
“Kar ki damu ba zai kai ba,ai ita Manubiya inaga ba lalle ta k’ara sati biyu a cikin gidan nan ba!komai a shirye yake kuma yana tafiya a kan tsari ga kuma wanchan Yaro d’an albaraka Abbakar shima yana side d’in mu,dan haka kawai ki kwantar da hankalinki a kan komai…kar ki damu Najeeb will come around sannan shima wanchan na Yasirar ko a ta biyu ne za ta shiga inshaaAllah……”
“Allah yasa”
Kawai Mommy tace,daga haka ta yi shiruu haka itama Baba larai.

Bayan sati biyu!.

Satin su Jidda d’aya a Nigeria suka wuce Dubai ita da Al’Ameen dan cikin sauk’i ta samu visiting visa.

Najeeb da Siyama abu ya yi k’arfi da shi da Yashjub har sun je sun nemi izinin zuwa zance a wajen su Baba Habu wanda hakan idear Baba ce,yanzu haka kuma maganar kawo
Kud’i da saka rana ake yi…..

Yusuf kuwa babu shi babu labarinsa an hana ma ganinsa,sai dai hakan kms ya sake ruru wutar bala’i tsakanin Baba da y’an Uwansa a cewarsu”tsabar mugunta a gabansa shi da Yashjub aka tafi da Yusuf amma ba su yi komai ba instead ma su d’aurin aure suka ci gaba da yi.”

Ya’isha Yassira da Yusra kuma suna gidan Manu har yanzu sun kafa sun tsare,da farko ba sa samun damar yin chatting da Abbakar ta wayar Manu kamar yadda suka tsara sai da aka yi sati d’aya suka samu Siyama ta tafi tukunna….sai sun daidaici ta tada sallah za su d’auki wayartata su yi abunda suka ga dama su goge su ajjiye mata wayar kafin ta idar dama shima Abbakar ya san time d’in da suke samun chance shiyasa he’is always available……Ana gamawa za su goge gudun kar ta gani shi kuma Abbakar yana chan yana tarawa a tasa wayar.

A b’angaren Baraka da Ya Musbah kuwa,tunda ta ji labarin tashi tashin ma zama gida d’aya da su Inna tace ba ta san zance ba,gashi kuma tun a ranar aka basu notice akace su tashi daga wannan gidan da suke a ciki in one week time mai gidan ya siyarwa wani…
Sai da aka yi fad’a da ita a k’ofar gida tace”ai ba a tab’a bada notice d’in da ba na shekara d’aya ba dan haka ko ubanwa ya siyarwa gidan wannan tsakaninsu shi da sabon mai Gida ita kam ba za ta tashi ba sai ta cinye shekara d’ayar ta sannan ba za ta karb’i refund ba,da kyar aka rabata da mutumin dan shima d’an a yi ne,sai da ta koma ciki tukunna mutumin ya bawa ya Musbah kud’in hayar sa ya sake bashi hak’uri yace”ya taimaka su nemi gida su tashi ga kud’insa nan complete ma ya bayar”
Ya Musbah dama yana so ya ci gaba da makarantar da ya soma kuma har ga Allah zuwa yanzu yana son zama a kusa da su Baba shiyasa shi abun ma dad’i ya yi masa dan haka ya karb’a yace”ba komai za su tashi in one week time d’in inshaaAllah”

Yana shiga gidan da ya so ya yi mata bayani ta k’i fahimta sam ta rufesa da fad’a a ranar dai ba su yi bacci ba,kwana ta yi tana bala’i kuma ta tabbbatar masa da babu inda za ta je…..
Shi dai ya Musbah a hankali a hankali ya dinga kwasar kayansa da shi da mai sunan Baba suna kaiwa sabon Gida sannan ya je ya biya kud’in registration d’insa ya ci gaba da zuwa makaranta ranar da sati d’aya ya cika ya zo ya yi mata sallama yace”za su tafi shi da mai sunan Baba”

Da kyar Baraka ta fita daga shock d’in Musbahu wanda tana tunanin ta riga ta saka a kwalba bai Isa ya yi mata haka ba,ta fahimci akwai matsala shiysa ta danne zuciyarta kawai dan ta san dole sai ta sake sabon shiri kuma a yadda ya botsare mata idan tace za ta yi turjiya kanta za ta jawa shiyasa kawai ta ce “ba komai ya jira ta ita ma za ta bishi…..”
Sai washegari aka gama kwashe kaya….a plan d’in Baraka idan ta je sai ta yi abunda shi da kansa zai ce su bar gidan kuma sai ta had’a sa da su Inna wannan karon ta kissa asiri da komai za ta had’a…sai dai kuma tun da ta je ta ga d’ankareran gida ta ce ba ta ga ta tashi ba,ta san kuma fitar da su Inna a gidan aiki ne ko da zai yiu to ba yanzu ba….gashi ya Musbah gaba d’aya ya juya mata baya aikin ma ya daina tasiri a kansa Kwata Kwata ba ya sauraronta ba ya jin maganarta,dan yanzu ma k’iri k’iri so take ya d’aga katanga tsakaninsu da su Inna ya fitar musu da gate d’insu a daban tama ce ita da kanta za ta bayarda kud’in amma yace”ba ta Isa ba!”
“Idan kuma ta sake yi mishi wannan maganar shirmen wallahi sai ranta ya yi masifar b’aci”
Shiyasa gaba d’aya hankalinta yake a masifar tashe,ta sake dagewa gidan kullum idan ka shigo banda k’aurin hayaki mara dad’i babu yake yi dan haka suma su Inna suka sake dagewa da rok’on Allah.

Jiya da daddare Hajiya Mama da Junior suka zo….Shiyasa yau da safe su Manu suke ta shiri akan za su je.
Kana ganinta ka san ta ci kuka dan fuskarta duk ta kumbura shiysa tunda su Yusra suka ganta a haka farin cikin su ya nunku ya gagara b’oyuwa har sai da ta d’an lura..a b’angarenta kuwa fad’a suka yi ita da Yash jiya abunda bai tab’a shiga tsakaninsu ba kenan!
Tun bayan sati biyu da ya nemeta ta k’i bashi had’in kai ta fara kuka shikenan bai sake neman wani abu a wajen ta ba,abun ya yi mata matuk’ar ciwo dan a tunaninta sun wuce haka ita da shi ba ta tab’a expecting zai yi irin wannan fushin da ita ba mutumin da a ko da yaushe ya ke cewa”Manubiya ba ta laifi a wajen Yash,he loves her morethan life itself”amma shine wai zai yi irin wannan fushin da ita!
Ba wai fushi na k’in magana ba dan suna wasa suna dariya yana kula da ita yadda ya kamata kawai dai ko hannunta ya daina rik’ewa…..
Dama da haushin hakan a ranta yau kuma k’iri k’iri da ta yi masa maganar makaranta ba kunya ba tsoron Allah yace”ba za ta ci gaba ba!”
Daga haka ya shige toilet ya barta a tsaye kuma ko da ya fito ya ga tana kuka bai tsaya ya rarrasheta ba instead shima sai ya had’e fuska tamau ya ci gaba da shirinsa ko a jikinsa…hakanan yana ganinta har ta gama kukan ta ta sauk’a k’asa had’a breakfast bai ce mata komai ba.

A b’angaren Yash kuwa..dalilin da ya sa ya d’aga mata k’afa kwana biyu ba ya so ya cika nagging ne ya je garin haka ya fara fita a ranta shiysa ya hak’ura akan har sai yaga she’s ready tukunna…..sannan yana so ya yi k’ok’ari ya ga ya kawar da duk wani abun da zai sa ya yi zarginta ko ya ji haushinta.

A yadda ya ji tana waya dole ko ma waye ya dasa mata ayar tambaya amma shi kuma k’ok’ari yake yi ya goge zargi ya bawa hakan kyakkyawar manufa…

Ya san dole idan ta koma makaranta he’ll be restless tunda ga issue a tsakaninsu dana ba su gama sorting out ba!sannan ga ciki a jikinta da ake buk’atar ace ta huta,shiysa yanzu da ta yi masa maganar yace mata”A’a”kuma ya had’e rai.
Sannan har ga Allah ya na kishi shiyasa ya ga dacewar gara kawai ta yi online…
Kukan ta ya tab’a sa sosai amma ya san idan ba hakan ya yi mata ba,ba za ta hak’ura ba!.

Har ta kai masa breakfast ya ci ya fita,sam fuskarsa babu walwala.
Sai wajajen 11 bayan sun gama girki Yasira ta ja su ta kai su gidan ita kuma ta wuce office da so ta yi yau ta zauna amma sai Daddy ya kirata.
Chapter 91 · 0% Book details