← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 137

Sashe 97

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kwana a tashi zama ya dawo da su Kano.Sai a lokacin Khadija ta gaya musu tana da y’a Yahanasu.
Addu’ar ta d’aya Allah ya sa ba a chanja musu makarantar da ta san an fara saka su ita da Yashjub tun farko ba,dan haka suka tambayi baban Al’ameen suka tafi ita da Ammi.
Ba su sha wahala ba dan tashi d’aya matar ta shaida ta ta amsheta hannu bibbiyu har da hawayenta tana cewa”ai ce musu aka yi ta rasu,amma ta je gida an ganta?ko dai nan wajen Yahanasu ta taho direct??ta je su ganta suma hankalinsu ya kwanta waye waye…”
Ita dai Khadija ce mata ta yi tou kafin tace”a kawo mata Yahanasu da Yashjub.”

“Yashjub ai ya dad’e da komawa Uk,amma Yahanasu dai tana nan,da tare take ma da siblings d’inta to yanzu basu da nursery section sakamokon gobarar da suka yi shine aka chanja musu school.”
Matar ta faiyyace mata hakan tana mai fita domin ta je ta taho mata da Yaha.

Sai da Khadija ta yi kuka,saboda da kyar Yahanasu ta shaida ta.
Tana murna tana kuka kamar ranta zai fita haka ta mak’alk’ale y’ar tata.

Hatta Ammi da mai makarantar sai da suka yi kuka..

Tun daga ranar duk ran Jumaah kafin su d’auki Al’ameen a school sai sun biya sun ga Yahanasu,Yarinyar ta shak’u da mahaifiyarta sosai zuwa yanzu….Khadija Ammi da Baban Al’ameen suna shiryen shiryen zuwa su je a yi magana ta fahimtar juna a samu Imam ya bawa Khadija Yahansu kwasam rannan sun je mai makarantar tace “Mahaifin Yahanasu yace idan ta sake barinta ta shiga makarantar sai ya k’ulle ta!.
Dan Allah dan Annabi ta yi hak’uri ta tafi kuma yace idan har ta sake zuwa kusa da y’ar sa wallahi kowa sai ya ji kansu kuma kowa sai ya ji abunda ta aikata har ita y’ar tata”…

….Babu kalar tambayar da su Ammi ba su yi mata ba a kan ta yi musu k’arin bayani amma ta k’i cewa komai,Baban Al’ameen da har yana shirin shiga kotu a samu a kwato mata y’arta amma ta hana ta kuma rok’esu akan kar su sake yin maganar a bari ya wuce kawai…Zuwa yanzu sun riga sun san Khadija sun san ba muguwa bace ba kuma ba ta da wani mummunan hali,shiyasa ba su dasa ayar tambaya a kanta game da hakan ba kuma suka bar maganar ya wuce kamar yadda ta rok’a ta buk’ata.

A b’angaren Khadija kuwa,abubuwa da dama ne suka had’e mata!
Kenan har yanzu Imam bai yi bincike ya goge zarginta ba!bai yi nadamar abunda ya aikata mata ba?
Sannan ko kewarta
ma bai yi ba all this years bai nemeta ba bai nemi ta dawo garesa ba instead yana so ma ya yi cutting duk wani ties da suke da shi,y’ar cikinta ma ya raba ta da ita kenan yanzu.!
Abu na uku kuma ta san tana da gaskiya akan sharrin da Lawal ya yi mata amma kuma har ga Allah idan akwai Al’amari mafi k’ololuwar tozarci da Muni da masifar tashin hankalin da ba ta son
tunawa a rayuwar shine wannan incidence d’in,ita kanta ita kad’ai idan ta tuno ji takeyi kamar ta binne kanta tsabar tashin hankali ba don k’arfin addu’a ba da tuni ta zauce tsabar yadda abun yake addabar ta a ko da yaushe idan ta tuna,A yadda Imam ya zama wani irin mugun mutum ta san zai yi mata terere ne kamar yadda mai makarantar su Yahansun ta ce yace “kowa sai ya ji kansu shi da ita,har Yahanasu”.A ganinta idan ba ta samu damar shak’uwa da Yahanasu ta bata tarbiyya da kulawar da ta kamata ba bai kamata ta bada gudun mawa wajen goga mata bak’in fenti ba!Yahanasu mace ce aure za ta yi ta san muddin ta bawa Imam k’ofa ya tozartata tabbas abun sai ya shafi rayuwar y’arta.
Mommy Uwa ce ta gari kuma za ta iya rantsuwa a kan soyayyarta ta gaskiya ga Yahanasu shiysa ta zab’i ta bisu ta addu’a dama rayuwa ba a yi ta dan ka samu komai perfect yadda kake so ba…tsakaninta da lawal Allah ne kad’ai zai Isar mata dan ya cuceta ta koina,Imam kuma ya tarwatsa ta gaba d’ayanta!kaico!da rashin sa’ar Miji na gari wanda zai tsaya mata ya bugi k’irji ya yi shaidar ta ya kareta a gaban kowa,asalima shi harin rayuwarta da duk wani sauran farin ciki da darajarta yake yi…
ko maganar tozarcin da wannan rana ta k’unsa ba ta so ta tuna ballanta a yi mata terere a bainar jama a a gaban y’arta.
Dan haka ta zab’i ta bi y’arta da fatan alkhairi kawai tare da addu’ar samun Miji na gari dan tabbas duk macen da ta yi rashin sa’ar Mijin kwarai a rayuwa to ta yi babban rashi…..shiyasa tun jiya Hankalinta yake a tashe take addu’ar Allah ya kawo abunda zai tarwatsa maganar auren Jidda da Yusuf dan tabbas Yusuf bai dace da Jidda ba mutumin da ba a san silar arzik’in sa ba ta ya za a d’auki y’a a basa saboda Allah…………..

Sallamar su Manubiya ce ta katsewa Mama dogon tunanin da ta lula!a hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ta shiga goge hawayen da ita kanta sai yanzu ta san suna zubo mata.Sai da ta gama goge fuskarta tukunna ta d’ago ta kallesu tana mai amsa sallamar tasu.
Cikin tsananin mutuwar jiki Manu ta k’arasa inda take suka gaisa da Mama da Aisha da Anty Umma,ta gaida Ammi wadda daga ita har Siyama suka yi mamakin ganinta a parlourn nasu tukunna tace musu “Ina su Inna”
Aisha ce ta mik’e tace”mu je wajen nasu”
Daga haka ta yi gaba suka bi bayanta.

Su biyu kawai suka tarar a cikin d’akin,Jidda ta rame a cikin kwana d’aya tak ta fita a haiyyacinta..
Suna zaune Inna ta na yi mata nasiha a haka su Manu suka shigo suka tarar da su.
A gefen gadon suka zazzauna suka sakata a tsakiya kowa idanunta ya cicciko.
Bayan gaishe gaishe Inna ta yi sauri ta mik’e ta ce”ga su Manu Aisha ku yi mata fad’a kuma Baba yace ana d’aurawa za a wuce a kaita gidanta.”
Siyama ce ta iya cewa”Inna kuma babu abunda za a yi?”
Murmushin da ya ki fi kuka ciwo Jidda ta yi ta rik’o hannunta tace”ba komai Siyama,Allah ya sa hakan ne ya fi alkhairi”
Siyama na shirin yin magana suka had’a ido da anty Umma wadda shigowarta kenan dan haka ta yi saurin d’aura yatsanta a kan labb’anta alamun ta yi shiru kafin ta kalli Manubiya tace”Manu d’an zo”
Suna fita ita da Inna suka ce mata “tunda har Jiddan ta yi shiru ta hak’ura itama to kawai su ci gaba da kwantar mata da hankalli,kar wadda tace wani abun da zai d’aga mata hankali a cikinsu.
Baba ya riga ya yi nisa ba zai ji kiran kowa ba ga Ammi Chan a parlour har ita aka had’u aka dinga bashi hak’uri d’azu amma ya k’i hak’uri dan haka kawai su zuba mishi ido.Zab’in Allah suke nema a ko da yaushe ba su san meye a k’asa ba,su dai su ci gaba da addu’a kawai…”

Da “to” kawai Manubiya ta amsa su daga haka ta nufi d’akin da ke opposite na Jiddahn dan ta san watak’il shine na Inna,tana shiga ta mayar da k’ofar da rufe dan har ga Allah ba ta son had’a idanu da Jidda ba za ta iyaba,she can’t believe wai Jidda za ta auri Yusuf amma ba abunda za ta iya yi a kai.
Waya ta d’auko ta kira Yashjub,a tunaninta har yanzu za ta ji fushi a muryarsa amma sai ta ji sa wasai kamar ba ta yi masa laifi jiya ba har yana tambayarta akwai abunda take so ya siyo ya taho mata da shi?yana hanya Daddy ya d’an kirasa zai je ya dawo.”
“A’a”kawai tace.
Daganan ta tambayesa ya suka yi da Baba,komai ya gaya mata daga haka shima yace su yi ta addu’a he’ll call her back yana shiga office d’in Daddy yanzun”
Sallama suka yi ta ajjiye wayar tana tunani barkatai a cikin ranta.

K’arfe 10:30am guri ya cika taff da jama’a dan Yusuf da kaka mallan sun yi gayya ba laifi,cikin gida kuwa kowa hankalinsa a tashe yake suma su Ya Nafi’u hankali a tashe dan yanzu suka dawo daga kai gado shiyasa suka kuma tabbatarwa eh fa Jidda Yusuf za ta aura…kaff wajen daga y’an gaiyyar sod’i da suka ga anata sauk’e kulolin abinci da lemuka da snacks da kajii sai Yusuf da kaka mallan ne kawai suke farin ciki dan hatta Baba hankalinsa ba a kwance yake ba ba a son ranshi zai aurawa Jidda wanda ranta ba ya so ba especially ma yanzu da Baban Al’Ameen ya zo ya ja sa gefe ya basa hak’uri yace”a shirye yake ya aurawa Al’Ameen Jidda a yanzu.Ya yi trusting Al’ameen har ma da ita kanta Jiddan amman indai har zargin su yake yi kamar yadda labari ya iske masa to tabbas babu wanda ya fi chanchanta Jiddan ta aura idan ba Al’ameen d’in ba.”
“Ya je ya sake tunani,da shi da wakilin Al’ameen suna nan babu inda za su je,fatan Allah ya sa su ji alkhairi.”

Tun daga nan jikin Baba ya yi sanyi tun ba ma da Baban Al’ameen yace”ya yi trusting har ita kanta Jiddan” ba!
A take a lokacin ya ga rashin adalcinsa ga Jidda…..tabbas ya biyewa dokin zuciya ya yanke d’anyen hukuncin da har abada zai dinga damunsa dan ya san zuwa yanzu kam ba zai yiu ya chanja d’aurin auren nan daga kan Yusuf ya koma kan Al’ameen ba….
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 36

Yau dai ya shirya zai daure ya duba sannan zai daure ya je gida ya gaida su Daddy,yana kiransu kullum suna gaisawa amma ba ya zuwa yau sati biyu kenan dan tsantsar kunyarsu yake ji! a duk lokacin da ya tuna yadda suka gansa shi da Kausar sai ya ji kamar ya binne kansa,shiyasa sam ya gagara sake fuskantar su.
Chapter 97 · 0% Book details