← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 137

Sashe 84

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suma shiruu suka yi su Yasira tun suna magana da suka ga su Siyama da Manubiyan sun k’i sake wa sai kawai suka d’aga k’afa suma suka yi shiru.
Suna a haka suna jimami Ya Nafi’u ya kira su Jidda yace”mutum biyu su fito a bar mutum d’aya a gidan za su wuce gida su fara tartara kaya an sallami Baba..

Siyama aka bar mata,Jidda da Muhsin kuma suka tafi dan idan zai yiu a yau suke so su tashi daga gadon k’aya su koma sabon gidansu dake a gandun albasa wanda Yashjub ya basu.Ba su yi ma tunanin za a sallami Baban yau ba da tuni sun yi parking d’in.

Ita Aisha Mama Anty Umma da Inna ne suka tartare komai kafin dare sun kammala komai ya Nafi’u da Muhsin kuma su sakayi ta zirga zirgar kai kaya a motarsa da motar kai kaya.

Sai da suka gama kammala kai komai gidan tukunna suka d’auko Baba daga asibiti suka nufi tsohon gidan nasu dan su je su yiwa su Uncle sallama saboda Baba dagewa ya yi yace”shi fa sai ya yi musu sallama.”
Suna zuwa Baba da Ya Nafi’u suka nufi wajen su Uncle d’in Inna da su Mama kuma suka nufi wajen matayensu.…yunwa Jidda ta ke ji dan ba ta tsaya taci abinci sosai ba,shiyasa ta je kitchen ta d’aura ruwan zafi da niyyar ta je ta siyo milo da madara ta sha tea…
Sai da gabanta ya yanke ya fad’i sakamokon k’amshin turaren da hancinta ya fara jiyo mata,a take a ranta tace “nooo..it can’t be,ta ya ma zai shigo nan.”daga haka ta mik’e bayan ta gama saita murhun ta juya za ta fita ta ga mutum a tsaye kyam!…..
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”tace a fili kafin ta d’an d’ago wayarta ta d’an haska dan ta samu ta tabbatarwa kanta da shi d’in ne…

Suna had’a ido ta fashe da kuka tace”dan girman Allah ka fita Ya Al’ameen kar ka janyo mana masifa”

Ahankali ya yi taku d’aya ya matso gareta muryarsa har tana d’an karkarwa yace”D’azu na ji Mama tana gaya wa Ammi cewa za ku tashi…”

Cikin sharar hawaye tace”eh,mun ma tashi..dan Allah ka fita…”

A hankali yace”Jidda ni da ke fa?ba za ma ki tsaya ki ji uzuri na ba?tun safe nake ta faman zirya Ina lek’en gidan nan Jidda duk dan saboda ke amma kora ta ma kike yi?”
Bai jira jin amsarta ba yace”a lokacin da na tafi,wallahi wallahi tun a kwana biyu da na kirawo wayarki na ji ba kya picking na had’o kayana na biyo jirgi na sauk’a a garin Abuja,inaga cousin d’ina da muka tafi tare da shi ne ya kirawo su Ammi yace musu na taho dan flight d’ina yana shirin boardn zuwa Kano Mahaifina ya kira ni yace idan na zo sai ya tsine mini tunda bani da hankali. Kalar fad’an da ya shiga yi min a wannan lokacin ni kaina na san akwai abunda Ammi ta gaya masa mai muni shiyasa ya yi fushi sosai ya ji haushi dan ko fad’a bai cika yi mini ba.A wannan lokacin babu yadda ban yi da shi ba amma ya k’i saurarona yace in juya in koma. Tun daga ranar ya daina kulani ya yi fushi da ni yace kuma wallahi idan ya ji labarin na zo Nigeria ba tare da na gama abunda ya tura ni ba sai ya bani mamaki yace kuma ko waya na yi miki bai yafe ba. Sai da na dawo tukunna a cikin maganarsa na fahimci Ammi ce ta ce masa saboda ke na rubuta letter na bar course d’in da ya tura ni in yi saboda kince ‘Baba zai aurar da ke a Yusuf idan ban dawo an yi auren da ni ba’.

Jidda Course d’in duk yawansa na san ba zai kai wata hud’u ba shiyasa na hak’ura na yi masa biyayya akan idan na dawo sai a yi komai amma ko a wannan lokacin sai da na saka mai gadin mu ya sa mini ido gudun kar Ina chan Ina shirya ta yadda zan shayo kan iyayena ke kuma a aura miki Yusuf.”

Shiruu ya yi kafin ya d’aura da cewa”wannan shine abunda ya faru Jidda shiysa kika ji ni shiru na san waye mahaifina yana son duk abunda nake so kuma zai tsaya mini a kai amma muddin na yi masa taurin kai na san tsaf za a samu matsala kuma na san halinsa da bin diddigi yadda yace”kar in kiraki wallahi da ace na kiraki sai ya sani ni na san waye shi”” na san kuma ya yi hakan ne saboda ya ga zan yi masa biyayya ko akasin hakan.
Cikin sake yin taku d’aya zuwa gareta yace”I love you!always and forever ba zan iya hak’ura dake ba Jidda gara ma tun wuri ki yi saurin karb’ar uzuri na ki yafe mini mu fara nemawa kan mu mafita!”

Shiruu ta yi a ranta ta ji matuk’ar sanyi da dad’i da ta ji ba banzatar da ita ya yi ba,a fili kuma sai tace”Ya Al’ameen ni kam na dad’e da hak’ura da kai,ka duba fa ka ga Mahaifinka ma ba so yake yi ba tunda shi ne yace kar ka ki…”
Cikin tarar nufashinta yace”noo Jidda wallahi ba da ke ya ke fushin ba da ni yake yi kuma na saboda ya ji batun aurenku da Yusuf ya taso da zai yi wani abun …a ranar da zan tafi a airport na yi masa bayanin komai na ce masa Ammi ba ta so,shi da kansa a wannan lokacin ya tabbatar mini da cewa”inshaaAllah ina dawowa za a yi auren mu kuma kafin ma in dawo za a yi tambaya batun Ammi kuma kar in damu ya san yadda zai yi da ita ba matsala inshaaAllah,but for now in yi k’ok’ari in yi concentrating a kan abunda na je yi saboda it’s very important for our business”
Shiysa da ya ji na shallake sa na bar ma makarantar ya ji haushi ya yi mini haka,amma wallahi ko yanzu Mahaifina a shirye yake ya d’aura mana aure ko a yau!ita ma Ammi ta amince this time for real saboda halin da na shiga ta tsorata ta yi nadama ta gaskiya ba kamar wanchan lokacin ba da ni kaina ban san linke ni ta yi a baibai ba”

Babu wani ragowar reason d’in da Jidda za ta d’aura laifi a kan Al’ameen saidai ta san su Baba ba za su tab’a fahimtarsa kamar yadda ita ta fahimce sa ba,shiyasa kawai ta d’an ja da baya cikin sharar kwallah tace”ka yi hak’uri Ya Al’ameen mu yi hak’uri kawai”
Ta fad’i hakan tana mai fashewa da kuka.
Da sauri ya sake matsowa yana mai cewa “noo Jidda kar ma ki fara cewa mu yi hak’uri wallahi ba zan iya ba”
Ganin sa daff da ita ya sa ta yi sauri ta sake ja baya ita shaf ta ma manta da murhu da ruwan zafin da ta d’aura,shi kuma abunda ya hango kenan dan haka ya yi saurin ruk’ota zuwa jikinsa ganin za ta afka kan murhun yace”careful!wuta a bayanki”
Salatin Ya Yusuf wanda ya hakse su tarr da wayarsa da kuma”Jidda”d’in da Baba yace ne ya fargar da su.
Da wani irin sauri ta ture Al’ameen shima da mugun sauri ya cikata ya matsa ya shiga ambaton”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
a cikin zuciyarsa
Juyawa kawai Baba ya yi ransa a mugun b’ace ya fice daga gidan yayin da Yusuf ya yi kansu zuciyarsa tana wani kalar mahaukacin tafasa..kamar wani mahaukaci sabon kamu haka ya koma yana zuwa ya rarumi wani k’atoton iccen ya makawa Al’ameen a kai da mugun sauri wanda hakan ya yi sanadiyyar fad’uwarsa a wajen gefen kansa ya shiga zub da jini.
Wata razananniyar k’ara Jidda ta buga ta yunk’ura da niyyar yin kan Al’ameen d’in dake nan kwance kamar gawa amma tashi d’aya itama Yusuf ya d’auketa da wani irin gigitaccen mari ya shak’o ta da dukkannin k’arfinsa ya buga ta jikin bango,dai dai nan su Anty Umma waenda k’arar Jidda ta Isar musu suka afko cikin kitchen d’in,da gudu anty Umma ta k’arasa ta shiga k’ok’arin kwatar Jidda wadda zuwa yanzu idanuwanta suka fara lullumshewa kafin duhu ya maye gurbin ganinta jikinta ya saki a take ta sume a wajen……

A hankali take bud’e idanunta da suka yi mata rauni..dishi dishi ta ke gani kafin ta fara gani da kyau kad’an kad’an..ba ta gama tantance a inda take ba…cikin fushi ta ji Baba wanda ta ga ya juya mata baya suna magana shi da Inna yana cewa”saboda su Uncle sun yi mini abu sai in d’aura karan tsana a kan Yusuf in rufe idanunwa na in k’i in bi bayan gaskiya?fad’a da su Uncle mu ka yi ba da Yusuf ba kuma suna d’in inshaaAllah wata rana za mu shirya amma ki daina saka Yusuf a cikin fad’an mu,ke ko irin karar da ya yi mana ma ba kya gani?wanne d’a ne kika tab’a gani ana fad’a da mahaifinsa amma ya rufe idanuwansa ya bi bayan k’anin mahaifinnasa da ake fad’an da shi? ki duba ki ga yadda ya dinga bin bayan mu a gaban Baba Habu har kusan marin sa fa ya yi suka samu sab’ani duk a ta dalilin mu amma duk da haka ke Yusuf bai kwanta miki ba?…….a da gaskiya na sa a raina ba za ta auri Yusuf ba amma kuma abunda idanuwa suka gane mini yau ya sanya naga dole fa in yi abunda na ga ya kamata a matsayina na ubanta ko so kike mu zuba mata ido Al’ameen d’in ya gama lalatata?ba ri ki ji abunda ba ki sani ba hatta makaranta wasu lokutan shi yake kai ta ya d’auko ta Yusuf ya dad’e da gaya mini hakan,ido kawai na zuba mata dama ina jiran ranar da zan kamata tana kulasa ashe abun nasu ma ya zarce misali!…”

Cikin kuka inna tace”yanzu zargin Jidda kake yi ba tare da ka tsaya ka ji bayanin ta ba??”
Cikin tarar numfashinta yace”tabbas!tabbas zargin ta nake yi..idan kuma za ki iya gaya mini uban me ta ke yi a ruk’umk’ume a jikinsa a kitchen cikin dare inda ba a tab’a tunanin ganin Al’ameen d’in ba to Ina sauraronki…”
Chapter 84 · 0% Book details