← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 137

Sashe 135

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A take ta sake tura masa kud’in ya cika tace ya yi
hak’uri ta san yayi mata halaccin da bazata iya k’irgawa ba amma dole ta yanke alak’arsu har abada ta yi saving aurenta,idan yana buk’atar wani abun ya gayawa Muhsin shi kuma zai gaya mata”
Hakanan suka rabu yanata jera mata godiya zuciyarsa k’all dan chan ya hango Yashjub ya danno kan motarsa tun d’azu amma da ya gansu sai ya tsaya ya ja ya yi parking ita kuma Manu sam ba ta lura da shi ba.
Tunda ta fito yake ta addu’a Yashjub ya zo dan Kausar tace masa mai gadin yace”tun d’azu ya fito……”
Tun a jiya ya tura masa mesaage ta inda yake cewa”a tunaninka sharri na yiwa matarka ko?to yanzu haka halinda ake ciki kud’i take bani nake tarawa zan siya mana gida,mu ja jari kafin ta ta rabu da kai.Manubiya ni take so ba Kai ba za ta iya yin komai saboda ni….idan Baka yarda da maganata ba ka duba alert a wayarta.”
Shiyasa tunda Manu ta fito yake ta addu’ar Yash d’in ya zo saboda ya samu ya sake k’ulleta idan Yash d’in ya gansu tare.

A b’angaren Yash kuwa kwata kwata bai yarda da maganar Abbakar ba! Haba mana!!abu kamar wasan Yara,amma fa da ya gansu tare ya kusan suma a cikin motar dan ko last week sai da ya ce mata ba dai ta kula Abbakar ba ya fakewa da zuwa musu gaisuwa ko?ita kuma tace masa “eh”
Sai gashi yau ya gansu tare a tsaye a waje ba ma a cikin gida ba kamar wasu masu zance!!!

Su Siyama sun tafi Umrah Jidda kuma bata da lafiya shi kuma Muhsin da shi ake aikin kimtsa gida ga aike shiyasa ba ta samu me rakata ba…Bata dad’e da komawa cikin gidan ba Yash ya kirata yace”ta fito ya zo!”
Peach colour lace ne a jikinta da white vail takalmi da y’an kunne da agogo…Bata yi kwalliyar komai ba amma sosai ta yi kyau shiyasa da ta fito ya tuna a haka fa ta ga Abbakar ya ji zuciyarsa kamar zata fashe….
Tana fitowa ta bud’e motar ta shiga suka gaisa sama sama ya kunna motar ya ja suka yi gaba fuskar nan a tamke kamar bai tab’a yin dariya ba,wanda hakan ya d’aure mata kai matuk’a…ya kan yi shiru ya yi ta tunani amma bai cika had’e rai kamar haka ba..

Duk da alhinin rasuwa da take a ciki haka ta daure ta dinga yi masa magana..wanda daga um sai um um kawai ya dinga binta da shi…..
A haka har suka k’arasa wajen..
iPhone d’inta ta zaro ta jona a jikin motar tasa dan ta ga bashi da niyyar shiga ita kuma ta d’auki purse d’inta ta fara k’ok’arin fita bayan tace masa ta gode
Kamar da ga sama ta ji yace”muga wayarki!”

A hankali tace”gata nan tana charji wanna kuma ta Muhsin ce na saka layi na a ciki”
Ta yi maganar tana mik’a masa wayar”
Karb’a ya yi kanshi tsaye ya shiga message ya duba.
Yadda ya mik’o
Mata wayar sai da ta tsorata tana karb’a yace mata”jeki!!”
da d’an k’arfi!
A ransa yana ji inama bai duba ba…shiyasa fa tun d’azu yake ta tausar kansa amma zuciya ta tunzurashi sai da ya duba!!!
Ya san maganar abbakar k’arya ne dayace tana basa zai siya musu gida to amma kuma meyasa ta tura masa kud’i ba tare da ta tambayesa ba sannan meyasa ta fita waje wajensa……
iPhone d’inta da ta kawo haske ya shiga ya duba nan ma yaga ta tura masa..
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun me yasa manubiya zata yi masa haka??”
Ba shi da mai basa amsa a take kawai ya ji hawaye sun b’alle masa dama ga masifar dayake a ciki tun kwanaki talatin da bakwai baya yanzu kuma ga kishin da yake shirin tarwatsa masa zuciya da kwakwalwa.shiyasa kawai ya kafa kansa a kan sitiyarin motar ya fashe da wani irin kuka.

Ya jima yana kuka kafin ya shiga jero istighfari ya goge fuskarsa ya d’ago yana maida numfashi dai dai nan ya ji ana knocking masa gilashin motar tasa….

Ba k’aramin mamakin ganin Aslam M T ya yi ba (Abokinsa da suka yi karatu tare a Uk)
Abunda bai sani ba kuwa wajen taff!! cike yake da Abokansa dan Kausar diary d’insa ta tsinta a d’akin Mommy hakanan ta turawa kaff friends d’insa da invitation na ranar sunan!!!

Yana fitowa Aslam ya yi murmushi yana kallonsa yace”Yash ya akayi ka yi aure?”
D’an guntun murmushin da ya fi kuka ciwo Yashjub ya yi kafin ya d’aura kwayar idanunsa a kan matar da ke gefen Aslam d’in yana rik’e da hannunta yace”kai ya akayi ka yi aure?!”
Duk dariya suka yi har ita Hudan..dai dai nan wasu friends d’insu su biyu suma suka k’araso wajen d’ayan yana cewa “da ikon Allah Yash da Aslam sun rigani aure gaskiya ku nema mini mata”
Dariya d’ayan ya yi kafin yace”ai Yash matansa har biyu amaryar ce ma ta haihu!!”
Ai kuwa nan suka tusa shi a gaba har Aslam wanda duk suka yi mamakin magana da walwalar sa dan hakan ba d’abiarsa bace ba kowa ya shaida…sun d’an jima a wajen suna ta tsokanar Yash kafin suka yi masa murna suka nufi cikin hall d’in gaba d’ayansu..
Shi dai Yash bai so shiga ba sam amma haka suka tilasta masa gashi ba zai yiu ya yi musu bayani ba,ga tashin hankalin da yake a ciki shiyasa ya ji kamar ya d’aga Hannu ya d’aura a ka ya yi ta kurma uban ihu….

Sai da ya shiga cikin ma tukunna ya had’u da ragowar friends d’insa hakanan aka had’u aka yi ta murna kowa yana cewa Yash ya kyauta da ya had’a musu wannan reunion d’in dan sun dad’e basu had’u ba.
…

Hannu bibbiyu su Mommy suka amshi Manubiya kamar za su goyata daga ita har Kausar d’in…ita dai Yassira binsu take yi da ido amma wallahi tsaf sai ta tona musu asiri saboda ta gaji gashi zargin Mommyn ma ita takeyi da rufe musu Baki dan kwata kwata ta gagara yin maganar Ya’isha a kowa.

Bayan sun shiga ne Yash ya nuna musu Manu wadda ke zaune a chan gefe yace musu “ga wife d’insa chan!”
Huda dama she’s uncomfortable a tsakaninsu shiyasa tace masa bari ta je wajensa….
Mommy d’ayan Abokin nasa ya hango dan haka suka je suka gaida ita suka dawo suka ci gaba da tsokanar Yash wanda shi ya k’i yarda ko kallonta ma ya yi….hakanan itama Kausar ya k’i amincewa su je wajenta ko jaririn ma ya k’i basu fuskar su d’auka saboda shi har yau bai ko kalli fuskar Yaron ba hud’uba ma Junior ne ya yi masa…su Daddy kuma basuce komai ba har yanzu wanda hakan ya sake fusata Kausar ta san duk dan Manubiya ne hakan take faruwa da ita shiyasa da ta tuna a yau zata kawo k’arshen ta sai kawai ta basar ta d’an ji sanyi a cikin ranta.

Manubiya tana zaune Huda ta zo ta zaune a kusa da ita suka gaisa tace mata”sunan ta Huda matar Abokin Mijinta Aslam”
Itama Manu ta ce mata sunanta Manu daga nan suka sake gaisawa suka zauna tare suna kallon masu rawar k’oroson da aka d’auko suke ta chasewa…
Ita dai Huda har ga Allah kwata kwata Kausar ba ta yi mata ba..ta wani zauna a kan kujerar alfarmar ta had’e rai kana ganinta ka san bata da mutunci gashi ita da Manubiya sam babu had’i shiyasa take ta tunanin dalilin da yasanya Yash ya auri Kausar bayan Allah ya basa Manu a matsayin mata……

Suna zaune aka kira Hudan a waya akwai kid’a sosai ta san ba za ta ji ba shiyasa ta mik’e tacewa Manubiya bari ta amsa call ta dawo……ba ta yi mintuna uku da fitan ba ta dawo kusan a tare suka shigo ita da Kausar wadda ta shigo ita kuma ta k’ofar kusa da seat d’inta…tun kafin ta fita ta ga Kausar d’in ta mik’e ta fita kuma bata ga lokacin da ta fita da jaririn ba amma tabbas yanzu da Yaron ta ganta ita da wata maid a wani dogon lungu inda ta je zata amsa waya itama…bata ma yi wayar a wajen ba ta chanja waje saboda kana ganinsu ka san basu da gaskiya kuma ba sa so a gansu sannan tabbas indai har she’s not mistaken to kamar a buhu ta ga suna shirin saka Yaron!
Noo it can’t be!babu uwar da zata saka jaririn d’anta a buhu ba bu ita!amma kuma what are they up to???”
Ta yiwa kanta tambayar kanta yana sake d’aurewa…..

Ita kam Manu al’amarin Yash damuwa alhini da kuma halin da take a ciki ne suka sanyata a gaba ta ma kasa magana ga kuma ciwon cikin period d’in da take yi sannan gashi ta ji kamar har ta fara b’ata jikinta tsabar yadda pad d’in jikinta ya jik’e!
Ba ta k’aunar chanjin pad a unguwa Idan ta fita amma ya zame mata dole!
Allah ya so ta ta zo da pad d’inta dan haka a gaban idanun Huda ta bud’e jakarta ta d’auka bak’ar ledar mai zip da ta sako pad d’in a ciki ta mayar ta rufe ta bata tace ta rik’e mata jakar bari ta je ta dawo….
Ba ta dad’e da fita ba itama ta dawo…tana zama baba ya kirata suka yi magana sai da ta kashe tukunna ta cewa Huda jibi sadakar arba’in d’in Mahaifiyarta
Sosai Huda ta tausaya mata nan ta yi mata gaisuwa tanata bata Baki…

Kwatsam y’an sanda da sojoji tare da masu gadin event centre d’in suka danno kai cikin hall d’in gadan gadan wanda hakan ya tada hankalin kowa matuk’a…gasu kuma rik’e da jaririn da ake sunansa wanda jama’ar wajen kaff basu ga lokacin da aka fita da shi ba a tunannin kowa Yaron yana chan a cikin gadonsa ne.
Chapter 135 · 0% Book details