← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 137

Sashe 39

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace
“Ki yi hak’uri wallahi d’azu shiyasa da suka zo chanja kaya na k’i yarda in shigo
saboda banaso in baki mugun labari….so na yi idan aka tafi kaita ko da ace ta riga ta shiga gidan ne in samu in yi dan da babu gara ba dad’i to sai kuma Yash d’in ya hanamu kai amarya.
Amman kar ki damu,na hango mana wata hanyar da za mu iya bi cikin sauk’i mu yi nasara a kanta,shiyasa ma kika ga na hawo da kwarin guiwa ta.”
Ba ta jira jin me zata ce ba ta d’aura da cewa”Yanzunnan yanayi da mood d’in da Daddy ya shiga daga jin bayanin su Yassira ya sanya na fahimci idan akace Yashjub da matar sa su dawo cikin gidannan da gudu zai yarda…Daddy yana son Yash matuk’a na san ba yadda zai yi ne shiyasa tun farko ya barsa ya je ya tare a wani waje daban amman in ta shine bai k’i su zauna a nan a bangaren Yashjub d’in ba kusa da shi tunda akwai space……yanzu a yadda na lura da shi ya fusata all we need to do shine mu kuma d’aura sa akan ‘idan ya yi sake to Manubiya da y’an uwanta za su kwace masa d’a!’,ke kuma sai ki tado da maganar dawowar ta su nan,daganan inshaaAllah za ki ga yadda al’amari zai chanja,ni kuma daga nan zan karb’i aikin kuma muddin ta dawo nan d’in wannan karon kam InshaaAllah bazamu samu failure ba.Dan zaman ta a kusa da mu kamar k’arshen ta ne…”

Ita dai Momy da “to”kawai ta bi Baaba larai dan ba kad’an ba ta ji haushi kuma ta tsorata da ta ji tace “ba su yi komai ba”a ganinta tunda har basu yi d’in ba kuma ga abunda ita kanta baba larai d’in ta fad’a da farko akan abun to fa babu wani abu da zasu yi daga baya wanda zai yi tasirin da za su samu nasarar cire Manubiya a gidan….da sauri ta kawar da tunanin gudun ma kar tunaninta ya tabbata dan idan ya tabbata bata san kuma ya zata yi ba….cikin son bawa kanta kwarin guiwa ta d’aura gaba d’aya hope d’inta akan zancen dawowar Manubiya da Yash kusa da su.Sannan tana addu’ar Allah ya sa kar Manubiya ta samu ciki kafin ta dawo cikin gidan da zama...
Tana cikin wannan tunanin ta ji Baaba larai tace”sai kuma maganar Yahanasu itama ya kamata asake..”
Dasauri Mommy ta katseta ta hanyar cewa “Larai mu bar maganar Yahanasu tukunna”
Cikin tarar numfashi ta Baba larai tace”She is out of control
Yahanasun da na sani ko
shegen duka su Yassira sukayi wa Manubiya bai kamata ace ta yi magana ba,kar fa Yarinyar nan ta zo ta yi miki b’aramb’atama wata rana.!”

Kallon da taga Mommy tana yi mata ne yasa ta had’iye maganar ta ta kasa ci gaba da cewa komai.
Ahankali Mommy tace
“Dan girman Allah ki yi min uzuri akan case d’in Yahansu Larai,ko me za ta yi kiyi min alk’awarin za ki tsaya akai mu gyara b’arnar da ta yi kawai
dan abunda kike tunani bazan iya sake bada goyon baya akai ba…na ga illar hakan!.
A ganina Yahanasu k’aramin alhaki ce a halin yanzu da ke kanki kin san idan ba mu tsayawa kanmu ba komai mai iya faruwa ne,dan haka mu ajjiye batun Yahanasu a gefe mu yi focusing akan abunda yake most important.”

Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin ta mike tsaye
tukunna ahankali tace “inshaaAllah,as u say…sai da safe.”………
…..
Motar Najeeb ce ta k’arshe
shiyasa basu samu damar yin parking a cikin gidan ba,sai
a waje a bakin titi.

Yana sane ya k’i bud’e side d’in Siyama,ita kanta ta fahimci shine ya k’i bud’e mata dan tare suka fara kokawar bud’ewa ita da su Jidda
amman duk na su ya bud’u nata kuma shiru.
Ganin tana ta bawa kanta wahala ne ya sa ta hak’ura
da niyyar Jidda na fita itama za ta bi bayanta ta fice.
Munira ce ta fara fita
Tace”mun gode”
Da murmushi ya amsata dan ba k’aramin farin ciki yake ciki ba dramar Siyama burgesa takeyi yadda ta had’e rai ta chuno baki abun ba k’aramin dad’i yake yi masa ba.

Jidda tana da sauk’e k’afafunta k’asa ta juyo ahankali cikin nutsuwar ta tace masa”Mun gode”daga haka ta sauk’a a motar.Ganin Siyama har ta matso tsakiya yasa ya yi
sauri ya juya ya sa hannun sa ya janyo murfin motar yana me cewa “Ba komai Jidda”
Yana dariya k’asa k’asa yana kallon Siyaman,bayan ya tabbatar ya sake saka lock a duk k’ofofin.

B’ata rai ta yi sosai kafin tace”
Zan fita”.
Murmushi ya yi tukunna yace
“Ashe Inada aiki a gabana sosai ni ban saniba,dan handling mace mai kishi
Is not an easy task!”.
Da sauri ta d’ago ta kallesa
sai kuma ta kau da kanta kawai.
Ganin tak’i cewa komai ne yasa yace “Amman naki yayi tsauri sosai,ya yi yawa pls a d’an rage,atleast a bani chance inyi explaining kaina”.
Cikin tarar numfashinsa tace
“Ni fa ba kishi nake yi ba besides i just knew you,yau kad’ai fa na sanka ta ya zan yi
kishi??infact ba wani abu a tsakanin mu!,kuma na riga na sani
Ya’isha girlfrnd d’inka ce
Ita zaka aura kowa ya sani…bai
shafe ni ba sannan It’s fine
dan kayi hugging d’inta saboda ba hurumina bane
tsakanin ku ne ku da ubangijinnku,so pls dan Allah ka daina cewa ina kishi saboda babu komai tsakanina da kai sai mutuncin da muka yi a iyaka yau!
Ba ruwana da relationship d’inka Kai da Ya’isha!
Bud’e min k’ofa in fita
Pls.”
Ta fad’i hakan tana mai sake matsawa kusa da jikin k’ofar dan ta samu ya d’auke hannunsa yanzu.

Ya d’an ji zafin yadda ta ce”ba ta kishinsa amman sai ya kawar yace
“Okay!In yi miki tambaya guda d’aya zaki amsamin?”
Kamar ba za ta ce wani abun ba sai kuma ta d’aga masa kanta alamun ‘yes’
ba tare da ta kalleshi ba.

Sai da ya sake juyowa ya fuskanceta sosai kafin yace
“D’azu,you were nice to me,amman tunda kika ganni da Ya isha ki kalleni ma aiki ne a wajenki kuma it’s obvious haushina kike ji,ta ya zaki yi min explaining hakan ba a matsayin kishi ba?.”

This time around murmushi ya ga ta d’an yi…tabbas idan ba ta yi da gaske ba to mutumin nan ba barinta zai yi ba and there is something about him wanda ta san idan har ba ta yak’i ta fatattaki tunanin sa da shi kansa daga rayuwarta ba
tou tabbas akwai matsala…kar ta je ta jangwalowa kanta abunda ba za ta iya ba dan haka ta d’ago ta kallesa kafin tace”Bana kishinka!like I just said ban ma sanka ba ballantana har in shak’u da kai
wanda shak’uwa ce za ta janyo abunda zai sanya in yi kishin naka,kawai dalilin da ya sanya ka ga Ina avoiding d’inka shine har ga Allah I’m sorry to say sam ba na shiri da Abota ko kirki ba na yadda in yi da Namiji irinka.”

Shiruu ya d’an yi kafin yace “Namiji irina?,menene ni d’in??”.
Itan ma sai da ta d’an yi shiru tukunna tace”Masu double dating!waenda a fuskar duniya ake yi musu kallon mayaudara!”.

Kamar zai fashe da kuka yace
“Siyama ni ba mayaudari bane ba,can you pls allow me to explain myself…”

Cikin katsesa kanta tsaye tace”a yadda ka karb’i number na da kuma yadda kake treating d’ina throughout today,da ni da kai duk munsan inda zancenka zai sauk’a,bayan kuma ka riga ka san kana da wadda za ka aura
wadda kake so itama take sonka.Menene hakan kake shirin yi min idan ba yaudara ba?

Ko mata biyu zaka aura a lokaci daya?besides na san ma itan zaka aura tunda itace type d’inka ni kawai a side kake da shirin ajjiyeni ka b’ata min lokaci”

Da sauri ya ce “in dan za a bani zab’i ke zan zab’a ke kad’ai!”
Da sauri ta d’aga masa hannu tace “Plss…dan Allah,banaso in ci gaba da gaya maka maganganu masu zafi
saboda despite abunda kayi
min still Ina respecting d’inka,na cire kunya na cire komai na gaya maka abunda yake raina da abunda na fahimta a kanka
which is the thruth
therefore dan Allah inaso ka fita hanya ta kwata kwata.
Bana son case da su Ya’isha
bawai tsoron ta nakeji ba amman duk inda nakai ga iya fad’a bazan iya had’a kaina fad’a da mutanen da basusan darajar d’an Adam daidai da kwayar zarra ba.
So pls
For the last time
Ka fita a hanya ta
sannan ka bud’e min k’ofa in fita.”

Shiruu kawai ya yi ya tsura mata ido…bai ma san me zai ce ba bai san ta Ina zai fara fita a hanyar tata ba,shi da yake son shiga cikin rayuwarta tashi d’aya tace masa ya fita a harkarta ma gaba d’aya which is the last thing da zai iya yi arayuwarsa,dan shi kansa ya san ba zai iya rabuwa da ita ba he’s sure of that,ba ta san yadda ya dinga fama da soyayyar ta sama da wata uku ba,ba zai iya yi mata alk’awarin fita a harkarta ko rabuwa da ita ba dan ya san ko ya yi alk’awarin to ba za ya cika ba.

Ahankali cikin son ta fahimce sa yace “Siyama ba zan iya rabuwa da ke ba,ki yi hak’uri ki fahimce ni ki bani chance ba zan tab’a yaudararki ko in cutar da ke ta ko wacce hanya ba,I promise!”

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “me ye tsakanin ka da ita
Ya’isha?just the truth!
dan Allah”

Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna yace
“She s my girlfriend”.

Yadda kalmar
‘She’s my girlfriend’
ta daki k’irjin ta
Ita kanta sai da ta yi mamaki.
Da kyar ta iya cewa “kuma har yanzu kuna tare ko?”

Still sai da ya d’an runtse idanunsa na y’an sakanni
tukunna ya bud’e yace
“Yea!but Siyama wallahi ke
nakeso kuma ba wai double dating zan yi ba,soon zan yi mata bayani ta yadda za ta fahimce ni cikin sauk’i zan yi setting nata free InshaaAllah
Ni da ke
we are meant to be,ki d’an ba ni time I’ll explain things to her….”
Chapter 39 · 0% Book details