← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 137

Sashe 98

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Also,yana son ganin Kausar ya fahimci ba ta mutu ba dan bai ji ana zaman makoki ba dan haka yanada tambayoyin
da yake buk’atar ta amsa masa…kafin ya san abunda zai yi mata next,dan wallahi sai ta zab’i mutuwa a kan rayuwa
Tun bayan kwana biyu da faruwar al’amarin ya fahimci wani Abu da yake adduar Allah ya sa hakan ne ‘in banda coconut oil d’in da ya ji a jikinsa ya kuma gani a ranar da tace wani Abu ya shiga tsakaninsu bai ga komai ba sannan da ya zauna ya yi lissafi time duration d’in is very short shiyasa kwakwalwarsa ta basa babu abunda ya shiga tsakaninsu! To amma a yadda take son shi me ya sa hakan ta kasance?me ye ribar ta idan ta bari aka kamasu kawai ba tare da wani abun ya shiga tsakaninsu ba??’
Ita kad’ai ce za ta iya amsa masa wannan question d’in kuma a yadda ta daku a hannunsa ya san ta d’an shiga saiti ta tsorata shiyasa ya yanke shawarar ya tunkare ta akan batun.Idan ma wani abun take shiryawa tun wuri ya datse !,shi ya san yadda zai bi da ita ta fad’i masa komai cikin sauk’i.

Hajiya Mama kuwa babu tambayar da ba ta yi ba amma aka k’i gaya mata asalin menene ya sami Kausar…Daddy ya lallab’a Ummi ta yi mata k’arya ba don ta so ba tace”daga bene ta fad’o”
Abhi kawai Daddy ya gaya wa wanda shima sai da Daddyn ya yi da ya sanin gaya masa dan cewa ya yi wallahi sai ta bar gidan a ranar da kyar Daddy ya rik’esa ya gaya masa komai yadda suka yi da Hajiya Mama da kuma abunda itama Mommyn tace masa a ranar da case d’in ya faru.Ya san idan suka kori Kausar kamar yadda ta fad’a zata tona masa asiri kuma ta kwashe gaba d’aya y’ay’an sai dai a yi gida biyu…sam abun ba zai yi kyau ba.

Tunda Abhi ya ke bai tab’a jin tsanar Mommy da Kausar irin na ranar ba don sai da ya yi kwana biyu tukunna ya d’an sauk’o…Shiyasa shima ya bayar da goyon baya aka b’oyewa Hajiya Mama saboda sun san idan ta sani babban tashin hankali zata kunnowa kowa.Ta d’agawa kowa hankali har ita kanta ba tare da anbi komai a hankali ba an gano Mommy an tona mata asiri ba.

….
Sai da Yashjub ya tabbatar Manubiya ba ta buk’atar komai ya kira mata Siyama ta zo tukunna ya ce bari ya je ya gaida su Daddy ta basa One hour yanzun zai dawo inshaaAllah…..

Dama ya lura da yanayin Mommy kamar tana fushi ne da shi Aikuwa yana zuwa ya tabbatar dan ganin sa a zahiri da tayi ya sanya ta kasa b’oye takaicin da haushinsa da take iya yi ta waya…da kyar suka gaisa daga haka ta mik’e ta fad’a d’akinta ta barsa shi da Baba larai.
Shima d’in a wuya yake da ita dan Wallahi da kyar ya danne zuciyarsa ma ya shigo side d’innata ko ganinta ba ya son yi daga ita har Baba larai d’in tata,dama a gis gis suka gaisa tana shigewa shima ya mik’e ya fita ko sallama bai yiwa Baba larai d’in ba.

Side d’in Daddy ya je ya tarar dasu su biyar shi Yahansu Ummi Hajiya Mama da Abhi sunata hira ana raha gwanin ban shaawa yana shiga shima suka ja sa da hira duk yadda yake jin kunya da nauyin Daddy Yahanasu da Ummi sai da ya d’an ware aka sha hira da shi..kafin a shiga bawa Ummi kwarin guiwa aka d’an kwantar mata da hankali tare da jaddada mata suna nan suna bincike za a nemo Munirat inshaaAllah…..
Ya jima sosai kafin ya mik’e yayi musu sallama ya tafi.

Yana sauk’owa daga stairs d’in Daddy ya hango Kausar da Yassir suna hawowa saman tsakiya daga chan k’asa.
Gefen fuskarta ta wajen idonta na dama har yanzu da y’ar guntuwar plasta ragowar ciwukan kuma sun fito rad’au!kasancewarta fara ya sa suka yi tambari kana hangota za ka hangosu.
Bai tab’a ganinta da Hijab ba sai yau!
A take ya ji gaba d’aya ransa ya yi wani irin mugun b’aci hankalansa ya tashi
Duniyar sa ta tsaya chak!

Wani irin kallon tsana ya shiga binta da shi…magana take yiwa Yassir amma sai maganar tata ta tsaya sakamokon jikinta da ya bata kamar yana wajen ne…..

Da sauri ta d’ago ta kalli direction d’in da ta ga kmr inuwar mutum.

Sanye yake da caftan
Nude colour da black hula d’inkin ya yi masifar yi masa kyau…ya d’an rame amman ya k’ara haske hancin sa ya k’ara tsayi sannan sumar sa ta d’an k’aru both fuskarsa da kansa wanda hakan ya sake fito da ainihin kyawun sa da kuma ramar da yayi..so da k’aunar Yasjub a jininta da ruhinta yake! ba ta ji akwai wata y’a mace da take yiwa wani namiji kwatankwacin k’aunar da take yi wa Yashjub,babu ita a kaff fad’in duniyar nan!,kallonsa take yi kamar wadda za ta had’iye sa ne Yayinda shima yake jifanta da nasa kallon na tsantsar tsana da kyama..idanunta har ciccikowa suka yi tsabar tsantsar k’auna a take ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere…
Sai a sannan ne Yassir ya gansa tsaye.
D’auke kai kawai yayi ya wuce gaba kafin yace mata
“Muje”
Ya fad’i hakan yana mai nufar side d’inta.
Har ta d’an d’aga k’afa zatayi gaba ta ji Yashjub yace
“Kausar!”.
Gaban tane ya bada wani dumm!!da mugun k’arfi,shauk’i da tsoro suka yi mata k’awanya kafin jikinta ya d’auki karkarwa a take.!
Kad’an ta d’an juya ta kalli direction d’insa ta ga ya nufota gadan gadan!
Tabbas sun shirya komai itada Yassir kuma ya tafi yadda suka tsara yadda ya kamata amma sai yanzu ta san ta yi kuskure
da ba su tanadi abunda za ta
fad’a masa a yanzu ba.
Sannan ta san Yashjub yanada kwakwalwa kuma ta san duk yadda ta yi k’ok’ari ta kawar da duk wani shakku dole akwai wani abu da zai d’an fahimta.Sam ba ta shirya wa wannan lokacin ba kawai ita idonta ya rufe ta fi karkata a kan ranar da abun ya faru kawai ita
kowa ya yarda akwai abunda ya faru tsankaninsu…
Tana wannan tunanin ya k’araso daff da ita ya tsaya.

Yassir ma ya d’an tsorata
dan ya lura da yanayin Yashjub d’in da kuma kallon rashin yardar da ya ga yana yi wa Kausar tun d’azun…a hankali
ya matso yace masa
“Yash batada lafiya!daga asibiti muke
Doctor ya bata pain reliever
yace kuma ta huta sosai.”

“Wuce ka tafi side d’inka!”
Kawai ya ce ba tare da ya kallesa ba.
Cije labb’ansa na k’asa ya yi yana jin wani tsananin takaici da tsanar Yash d’in tana ratsashi….Cikin d’aci yace”Doctor yace ta huta saboda
dukan da ka yi mata ba na wasa bane har yau bata gama warkewa ba….”
Ya fad’i hakan yana ji kamar ya rufesa da duka,a duk lokacin da ya tuna dukan da Yash ya yi mata on top of that da cikinsa a jikinta
ya yi mata wannan dukan sai ya ji kamar ya yi hauka!.

D’agowa kawai Yash ya yi ya zuba masa lumsasssun idanunsa da suka fara kad’awa sukayi ja kad’an.
Yanayin kallon da ya ga yana yi masa ne yasa ya fahimci akwai matsala idan ya biye sa saboda shima a zuciye yake kamar yadda shima yake a zuciye ya san idan ya ci gaba da tsayuwa za a yi b’arna dan haka kawai ya juya fuuu ya nufi k’asa yana ji kamar zuciyarsa za ta tarwatse.

Kasa d’agowa tayi ta kalli Yash
bayan wucewar Yassir…duk
wani audacity d’inta yau sai ta nema ta rasa.Gaba d’aya ta rud’e ta rikice har yanzu jikinta karkarwa yakeyi kad’an kad’an.

Ji yake kamar ya rufeta da wani sabon dukan amman sai ya danne zuciyarsa..babu alamun wasa ko tantama a hankali yace”Inaso inji gaskiyar komai daga bakinki.
Na farko ki gaya mini me kika bani na sha,na biyu inaso da bakinki ki gaya mini cewar babu abunda ya faru tsakaninmu…Kausar kin san ni ba Yaro bane kuma da aurena so na riga na fahimci komai…
But I want to hear it from you Ina so da bakinki ki fad’a mini komai!
kuma ki sani hakan shine zaman lafiyarki.”

A kaff cikin maganganunsa inda yake cewa”kuma inada aure”ya fi komai d’aga mata hankali da b’ata mata rai dan tashi wani sabon kishinsa ya dirar mata.
Wasu hawaye ya ga sun hau sintiri a kan farar fuskarta….
Ranta ya riga ya b’aci kishinsa ya fusatata shiyasa ta kai iya wuya ta k’ulu ta k’ule kuma ta riga ta fahimci tabbas fa idan ta bari ta yi laushi to kwab’arta za ta yi ruwa!dan haka ta dake ta murzawa idanunta toka ta sake matsowa daff da shi tukunna ta fara magana”Yash!!Ina sonka!
Ni kaina bansan yawa da adadin son da nake yi maka ba
amman ko da ace sonka zai kashe ni ba zan tab’a aikata abunda kake tunanin na aikata ba!
Saboda na san ranka ba zai so ba kuma ni a ko da yaushe farin cikin ka shine priority d’ina.
Tayaya kake tunanin zan so ka ji kunya?Tayaya kake tunanin zan so Mommy ta ganmu bayan na san idan hakan ta faru zan yi loosing trust d’inta
Tayaya kake tunanin zan yi playing role d’in prostitude a idanunka bayan ni a ko da yaushe burina shine in gyarru in shiryu ko Allah zai sa ka yarda da ni ka amince ka bani matsayin matarka!

I’m honored and happy for that night amman wallahi Yash ka yarda da ni ba haka na so ba!babu yadda zan yi ne a wannan daren I kept on sayin No! to you amma ba ka saurara mini ba ni kaina na yi mamakin ka shiyasa nake tunanin watak’ilan a office asibiti ko wani gurin ne aka yi mixing drink d’inka ko aka shaka maka wani abun baka sani ba
Dan wallahi tallahi nikam ban san komai ba kuma ban yi maka komai ba.”
Chapter 98 · 0% Book details