← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 137

Sashe 58

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin ya koma ya zauna ya yi shiru bayan sun gaisa ne ya sanya Inna ta ajjiye kayan dake hannunta ta mik’e ta k’arasa inda yake ta zauna.A hankali tace”Da!na ce ba zan yi maka magana ba nima,amma kuma na ga abun naka kullum k’aruwa yake yi.Jiya dai Baba ya ce mini yana tunanin matsala kuka samu kai da Nafi’u kwana biyu duba da yadda kukayi jiya kai da shi a gabanmu,sai dai kuma ni ina kokwanto.
Dan haka inaso Musbahu ya gaya mini meye ne yake damunsa kwana biyun nan?ko ya fara b’oyewa Innar sa abu ne bata sani ba?”.

A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa kafin yace
‘’Inna kunyar ki nake ji shiyasa kika ga na kasa gaya miki,”
da sauri ta kamo fuskar sa da hannu biyu ta d’ago da shi kafin tace”kunya ta kuma Musbahu?ni ce ma kenan silar damuwar taka?.Gaya mini kar ka d’auki lokaci, Ina sauraron ka, ka gayamin ko ma menene yanzunnan.’’

Ahankali ya Musbah ya kama hannayen nata duka biyu yana jin wani nauyin ta da kunyar ta
tukunna da kyar kamar wanda dama chan jira yakeyi a tambayesa yace
“Idan na ce inaso in dawo da Baraka inna za ki iya yafe mini?’’
Ya fad’i hakan kwayar idanun sa suna kallon k’asa.

Ahankali ta zame hannunta daga fuskar sa ta kawar da kanta gefe.

Da sauri yace
‘’ki yi hak’uri inshaaAllah ba zan sake yin maganar ba‘’

Ahankali ba tare da ta kallesa ba tace
‘’Musbahu mai ka d’auke ni?”

Da sauri ya sake cewa
‘’Ki yi hak’uri Inna inshaaAllah ba zan sake yin maganar ba har abada,dan Allah ki yi hak’uri’’
Ya fad’i hakan yana mai k’ok’orin mik’ewa.
A hankali ta ruk’o hannunsa ta d’ago da fuskarta ta kalle sa kafin tace‘’Ba ka bani amsata ba!.
Mai ka d’auke ni?”
Ganin ya yi shiru ya sunkuyar da kansa k’asa ne ya sa tace”A tunanin ka idan uwar Mijin Jidda ko Manubiya ta bayar da gudunmawa wajen kashe musu aure murus zan ji dad’i?.
Sannan kana tunanin dama chan Ina farin ciki ne saboda ka hukunta Baraka a ta dalilina?
Bari kaji..Baraka ta yi mini k’ololuwar rashin mutunci amman a ko da yaushe idan na tuna da mai sunan baba na tuna cewa a ta dalilina iyayen sa suka rabu gaba d’aya sai in ji babu dad’i.
Dukda na ji dad’i kuma ka zame mini abun alfahari Musbahu saboda yadda ka nuna b’acin ranka a lokacin da aka wulak’anta ni,na ji dad’i!na ji dad’i matuk’a! kuma har gobe Ina sanya maka albarka amma kuma idan ka ce za ka dawo da matar ka ba zan ji haushi ba dan Babban burina a yanzu shine in ga kai da k’annenka zaune lafiya a gidajenku..”

Hawayen farin ciki da k’aunar mahaifiyar tasa ne suka shiga sintiri a kan fuskarsa bai san lokacin da ya rungumeta ba yace”Amman Innaa sai nake gani kmr ban kyauta miki ba…”

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta saki murmushi ta d’ago ta kallesa tace
‘’ ka dawo da ita na san yanzu ta ku san fita daga idda ma ko?”
Ba ta jira jin amsar tasa ba ta d’aura da cewa”ni kaina ba son zaman nan naka nake yi a d’aki gabjeje da kai ba.Ka dawo da ita ku koma gidan ku ku ci gaba da rayuwar ku Allah ya yi maka albarka.”
Tana gama fad’in haka ta mik’e ta fice daga d’akin ta nufi kitchen bayan ta d’auki mayafin ta.

Ya Musbah bai tashi a wajen ba sai da ya maida Baraka
Cikin tsananin jin dad’i ya mik’e ya fice…wajenta ya fara zuwa ya sanar mata ta yi masa iso cikin gidan su ya sanar da Mamanta aka kira kawunta a waya dake ba a garin yake ba shima aka sanar masa…tukunna ya wuce aiki daga baya,suna ta murna shi da Baraka.

Sai dare tukunna Innaa ta samu Baba ta gaya masa yadda sukayi da Ya Musbah.
Dama ta san zai yi fad’a shiyasa ta bari sai dare..ai
kuwa ta sha fad’a dan rabon da Baba ya yi mata irin haka har ta manta.
Jidda kanta ba ta ji dad’i ba
dan ita har ga Allah a tunanin ta Baraka ta tafi kenan..wacce iriyar zuciya ce da Inna haka?ta ya za ki bayar da goyon baya d’anki ya dawo da matar da ta yi miki wannaann kalar wulak’ancin….
Kuma ta san Innar ta san Baba ba zai yarda ba shiyasa ta k’i tsayawa a yi shawara da shi ta yanke hukuncin ita kad’ai.

A b’angaren Baba kuwa….ya san idan har zama bai k’are ba to ko yankasu Baraka take yi a da! sai ta dawo.
Dan haka dama shi basa da m burin raba aurenta da Musbahu murus rabuwa ta har abada kuma shi ba wai yanaso ta dawo baneba kawai dai a nasa b’angaren duk abunda Allah ya tsara tou zai yi maraba da shi…Kawai shi babban abun da ya b’ata masa rai shine yadda aka dawo da ita da wurwuri ba tare da ta gama gane mutuncin iyayensa ba
dan yanzu ba ta horu ba ya tabbatar ko da gidan gyaran Hali aka kaita bai ci ace ta yi hankali a cikin wata uku da y’an kwanaki ba.
Saboda Allah tsabar rashin lissafi ace wai duk kalar tujarar da Baraka ta yi amman Musbah ya maido da ita ko idda ba ta fita ba sai kace er gwal!.

Ba kalar fad’an da Baba bai yi ba,daga k’arshe ma kawai ya mik’e zai fita dan takaici yasa yake ji ba zai iya ci gaba da zama a cikin d’akin ba.
Yana Isa bakin k’ofa ya ci karo da Ya Musbah da mai sunan baba.Bai gama k’are musu kallo ba ya ga Baraka a bayan su…da farko so ya yi kawai ya zagayeta ya wuce amman kuma sai ya koma ya nemi guri ya zauna..
To dai Allah kad’ai ya san kalar turare da rubutun da Baraka ta yi ta sha dan tashi d’aya zuciyar Baba Inna da Jidda har ma da Muhsin wanda shigowarsa kenan daga d’akinsu ta yi sanyi.

Har k’asa da durk’usa ta bawa Inna hak’uri tana kuka tana cewa sharrrin shaid’an ne
haka shima ma Baba ta basa hak’uri.
Har Jidda sai da ta bawa hak’uri Akan abubuwan da ta yiyyi.

Daganan d’akin ya d’auki shiru
kafin Baba ya kalli Ya Musbahu yace “ka riga ka maida ita ko?”

Jin jina kai ya yi alamun ‘eh’
ya na mai jin kunya da nauyin Baba.
Ajiyar zuciya Baba ya sauk’e kafin ya ce”Sai ku tare da wuri,
Allah ya so naga gidan naka babu kowa a ciki”
Daga haka ya fara k’ok’arin fita.

Kamar Ya Musbah ba zai ce komai ba sai kuma ya d’an yi gyaran murya yace
“Wai da sai nan da sati biyu tukunna dan itama ta samu ta bayar da kayayyakinta gyara nima kuma akwai y’an gyare gyaren da zan yi a gidan.”

Jin jina kai kawai Baba yayi daga haka ya mik’e ya ce “Allah ya yi albarka.”
Yana gama fad’in haka ya sa kai ya fice.

Sai chan dare tukunna Baraka ta tafi ta barsu da abubuwan mamaki…ko magana za ta yi da Inna sai ta sunkuyar da kai k’asa
Hatta Jidda yadda take janta a jiki abun sai da ya basu matuk’ar mamaki
Gashi tace za su tare ne tare da Muhsin
Shi dai Muhsin ya bita da to ne amman har ga Allah in ya tuno halayenta sai ya ji baya son bin su,matar da ada kwata kwata ko dariya ba ta yi masa bata jan sa a jiki yanzu kuwa tashi d’aya ta dawo kamar za ta goya sa dukda Yarone amma ya saka a ransa watakil dan ta ga Innaa ne kuma dan taga Gidan su ta zo shiyasa take ta faman lallab’asa ya san yana zuwa gidan ta zata fara cin k’aniyar sa.
Dukda yadda yanzun yake jinta har cikin ransa amman still yana iya tuno halayen Baraka a gidan ta….

Jidda kuwa Allah Allah takeyi Baraka ta tafi ta samu ta kira Manubiya,dan kanta ya rabu biyu
It’s either
Fad’a akayi mata a gida da kuma yanayin duniya da ta gani ta gane gaskiya ta yi dana sani ta shiryu da gaske
Ko
kuma dai
Wani abun ne a cikin zuciyarta dan Barakar da ta sani ba zata nutsu irin haka a lokaci guda ba tare da kwakkwaran dalili ba……

Sai chan dare su Manubiya suka isa Gida dan sai da suka biya suka ci abinci suka d’an zagaya suka fara rage siyayyar su tukunna suka nufi gida kowa a gajiye.Suna zuwa Yashjub ya cewa Yadira “ta zab’a d’aki”

Na nan saman opposite d’akin Manubiya ta nuna dan haka ya cewa drivern gidan da ya tayasu hawowa da kayayyaki “ya saka mata kayan ta a ciki”.

Wanka kawai ta yi ko sallah ba ta nutsu ta yi ba ta d’auki abunda su Mommy suka bata ta fito.
A zaune ta sami Manubiya tana waya da Jidda tana bata labarin Baraka.
Kamar Manubiya za ta had’iyi zuciya kuwa haka taji..ashe dama shiyasa ta ga yanata tunani for the past few weeks,d’azu kuma ita a tunanin ta ma ko kukan da ta yi ne ya b’ata masa mood d’in sa ya saka shi a damuwa ashe shi tunanin shegiya Baraka yakeyi.
Taya Ya Musbah zai so Baraka ta dawo wanne irin abu ne haka!…a hankali ta lumshe idanuwanta ta bud’e kafin ta d’ago ta kalli Yadira tace “zauna mana”
Sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tace “zan kiranku Jidda”daga haka ta katse wayar,tana mai jin kanta yana wani irin juyawa tsabar takaicin Baraka da Ya Musbah.

Tsaki Yadira ta yi kafin tace
“Ai ko ba ki fad’a ba!”
Sai kuma ta zauna tace”duk fushin da mutum zai yi nan gani nan bari..zama daram babu inda zanje”

Ahankali Manubiya ta d’ago ta kalle ta har za ta bata amsa sai kuma kawai ta mayar da kanta k’asa.
Chapter 58 · 0% Book details