← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 137

Sashe 86

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana fita ya ga makullin motarsa a inda ya yar d’azun tashi d’aya ya sa hannu ya d’auka ya d’auki wayarsa kawai ya fice gaba d’aya ko bi ta kan Daddy bai sake yi ba.
Yana fita ya shige motar ya kunna ya fice daga gidan…..

Test din HIV ya fara zuwa akayi masa
Negative
Daganan ya biya Bristol ya kama d’aki dan ba ma ya so ya je inda wani zai nemo shi…….Idan ya rufe idanunsa fuskar Manubiya kawai yake gani…”innalilla wa inna ilaihirrajiun” yake ta ambata a cikin ransa…idan ya b’oye mata ya ha’inceta amma kuma bai san ta Ina zai iya kallonta ya gaya mata wannan mummunan al’amari ba,ya san it’s the worst thing da za ta iya tolerating!
He almost die a lokacin da Abbakar ya shirga masa zantukan nan,ba dan su Najeeb sun wayar masa da kai ba ya san tsaf ciwon zuciya zai iya yin ajalinsa shiyasa he can’t even begin to imagine halin da za ta shiga idan ya gaya mata abunda ya faru tsakaninsa da Kausar besides bai ma san ta Ina zai fara had’a ido da ita ba balle ya yi mata bayani wani irin tsananin tausayinta da kunyarta yake ji….
Wayarsa ce ta d’auki k’ara a karo na hud’u dan haka ya d’ago da niyyar kashe wayar gaba d’aya amma sai yaga ‘Honey’ a kan screen d’in yana yawo….
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga bin fuskarsa hannunsa ya fara karkarwa k’irjinsa ya shiga dukan uku uku.
Har ta katse bai d’auka ba haka ta sake kira ta katse daga k’arshe ta turo masa message”Baby Ina wuni hope you are fine..d’azu ka kira Ina barci yanzu na farka..ba ka d’aukan wayar!hope all is well I need you I want to see you plss.”
Yana gama karantawa ya yi jifa da wayar ya mik’e ya fad’a toilet ya sakar wa kansa ruwan sanyi yana wani Irin huci kansa yana wani irin juyawa….

Ya fi awa d’aya a cikin band’akin da kyar ya yi wanka ya yi alwallah ya fito yana istighfari….jallabiyarsa ta riga ta jike tana band’akin shiyasa sai da ya jira ya yi order aka kawo masa tukunna ya mik’e ya tada ik’ama yana ta istighfari dan bai tashi tuna bai yi sallar Magrib da isha ba sai da ya gama wanka ya fara alwallah saboda bai tab’a kaiwa war haka bai yi ba shiyasa ya manta…..

Yana idar da sallar ya tashi ya fara jero nafilfili,ko da ya gama ma karatun Al’kur’ani ya zauna yayi sai wajajen 1 na dare tukunna ya d’an samu zuciyarsa ta fara sanyi…

Wayarsa ya d’auka…
Ya danna dial a number Manu ya kashe yafi sau shidda kafin daga baya kawai ya rufe ido ya danna ya runtse idanuwansa zuciyarsa tana wani kalar mahaukacin bugawa.

“Assalam alaikom”
Ya jiyo muryarta mai dad’in sauraro da kwantar da hankali.

A hankali ya lumshe idanunsa hawaye suka shiga zirara kafin ya ce”ameen wa alaiki assalam,ba ki yi barci ba har yanzu?”
A hankali
Cikin firgice tace”Ya Yash kaima kuka kake yi?har yanzu?
killace kanka da k’aurace mini ba shine zai yi mana maganin damuwar mu ba.
Na kasa nutsuwa hankalina a tashe! ban yi tunanin za ka gujemini a irin wannan lokacin da nake matuk’ar buk’atarka ba Ya Yash.”

Kuka sosai ta ji ya saka ya kashe wayar,yana kashewa ya yi switch off d’inta gaba d’aya.
Ta kira sa ya fi sau ashirin amma switch off dan haka hankali ta ya sake tashi!ta fara wasu Irin hawaye masu zafi…ta shiga tashin hankali da firgici matuk’a a lokacin da aka ce cikin jikinta ya fita amma dama ita 50%na damuwarta Yashjub ne…da farko ta d’auka fushi ya yi da ita bayan damuwar da yake a ciki shiyasa ya k’i zuwa gareta amma yanzu da suka yi waya tashi d’aya ta fahimci tsananin damuwa da tashin hankali ne suka sanya shi ya killace kansa ya k’i zuwa wajenta…ta san Yashjub yana sonta yana son cikin jikinta amma ba ta yi tunanin abun zai kai ga haka don wanda ya basu ya amsa ba.

Bayan ya gama waya da Manubiya da kamar awa d’aya da rabi lokacin ya san ta hak’ura ta daina gwada layukansa ya kunna d’ayar wayar sa ya kira Yahanasu,bai damu da dare ko kuma kar ya tasheta a barci ba haka nan ya yi ta kira yana sake kira har sai da ta d’auka cikin magagin bacci a d’an rikice tace”Assalam alaikom”
“Yash Ina ka tafi ne an je har gidanka ba ka nan kuma ba ka d’aukar waya?”

“Yaha ki taimakeni ki yiwa Manubiya bayanin abunda ya faru ba zan iya ba ba kuma zan iya b’oye mata ba..sannan mun riga mun yiwa juna alk’awarin babu b’oye b’oye a tsakaninmu…kuma na san ko yaya mutum ya kai ga iya b’oye sirri dole sai an samu leakage idan ta ji a wani wajen za ta karaya sannan ba za ta sake yarda da ni ba…ki yi mata bayani ki
Ba ta hak’uri ki fahimtar da ita on my behalf Ina son ganinta amma ba zan iya fuskantar ta ba i’m shy afraid disturbed and scared………”

A hankali Yaha ta share hawayenta tace”slow down Yash….!”
Kafin ta mik’e ta zauna ta na mai kunna bedside lamp tace”maganar b’oye mata kam dama bai taso ba dan na san ko da gangan sai an samu masu gaya mata!Tunda abu ne wanda kowa ya sani…
Ka kwantar da hankalinka InshaaAllah Manubiya za ta fahimceka na ji dad’i matuk’a da ka ce ba za ka b’oye mata ba saboda b’oye b’oye babu abunda yake janyowa sai b’arna sannan mai gaskiya yana tare da Allah ba zai tab’a tab’ewa ba.!
InshaaAllah gobe da safen zan shirye in je in sameta,ka kwantar da hankalinka Kausar za ta girbi abunda ta shuka Allah yana tare da kai…”
A hankali yace”inshaaAllah”
yana jin zuciyarsa tana wani irin tafarfasa…
Sai da ta sake kwantar masa da hankali tace”ya yi ta sallah da nafiloli idan ya kasa bacci komai zai yi daidai inshaaAllah sannan idan ya samu hali gobe da safe ya kira Daddy saboda hankalinsa a mugun tashe yake…….”
Daga haka suka yi sallama yana mai jin sassaucin abunda yake ji kafin su yi magana….Tabbas Yahanasu is one of the best gift da Ubangiji ya sako cikin rayuwarsa tana tsaya masa a akan komai tana son farincikin sa sannan ta yi trusting d’insa d’ari bisa d’ari!kalli yanzu he don’t even have to explain himself tashi d’aya ta san sharrin Kausar ne….Addu’a ya fara yi a cikin ransa Allah Ubangiji ya sa Manubiya ma ta kawar da kishi Yahansu tana yi mata bayani ta aminta da shi ta yafe komai……..

A b’angaren Kausar kuwa har chan cikin dare ba ta farfad’o ba.
Yasmeen ta yi mata duk abunda ya kamar ta yi dressing mata ciwukan fuskarta amma idan
ka ganta in ba cikakken sani ka yi mata ba tou ba lalle ka shaidata ba dan fuskarta ta kumbura ta yi sutu sutu ga ciwuka ta koina kamar ba ita ba.

In banda zubar hawaye babu abunda Mommy take yi…da kyar su Yasira suka lallab’ata aka bar Kausar a gida
dan Yasmeen tace musu”she’s fine kuma idan aka kaita asibiti a haka case ne sannan in akayi bincike aka gano Yashjub zai iya shiga matsala.”
Dakyar Mommy ta yadda
amma da cewa ta yi a kaita asibitin a haka ya shiga matsalar shi ya sani ita ba damuwar ta bace ba.”
Dan ba kad’an ba ta ji mugun mugun zafin halin da Kausar d’in ta ke ciki ba kad’an ba
dukda ta san maybe dagaske Yash d’in yake tricking d’insa Kausar d’in ta yi ya kwanta da ita amma sam ita ba wannan ne a gabanta ba! Bata ga dalilin da zai sanya ya illata mata Yarinya haka ba wannan ai rashin imani ne!Yarinya y’ar amana!yanzu inda za a tashi uwarta a nuna mata Kausar unconscious da fuskarta haka
ai batasan da wanne ido zata kalletaba ranar gobe k’iyama.

Da Mommy da Yassir sun fi kowa tashin hankali a cikin d’akin sai Yadira wadda yanayin Kausar d’in ya fara bata tsoro itama ta fashe da kuka junior yake ta faman lallashinta.

Yassir har ya fara shirye shiryen appointment dan yace “tana bud’e ido za su bar k’asar!”
Saboda tabbas yadda kumatunta da gefen idanunta suka fashe ya san sai an yi wani abun a wajen…dukda ba shi da enough kud’i but zai
ranta a wajen Abokan sa a
je a yi mata aiki kafin ya samu ta warke tukunna ya dawo ta kan Yash dan bai ma san ta Ina zai fara ba!
ya yi taking nashi by surprise sam bai yi tunanin zai
Illata masa Kausar har haka ba…dukda ya san end d’insa ya zo dan yanzu Manubiya da Daddy za su juya masa baya saboda ya gama shiryawa da kansa zai tura mata message ya gaya mata komai!amma dole Yashjub ya yi paying for dukan nan da ya yiwa Kausar wallahi,dole!…

Ummi ce kawai babu a d’akin sai Daddy amma kaff gaba d’ayansu suna d’akin.
Junior kawai kallon Yassir yake yi…a yadda ya d’aga hankalinsa tabbas ya tonawa kansa asiri ne a idanun Junior saboda bai kamata ace ba ya fushi da Kausar a yanzu ba bayan abunda idanunsa suka gane masa hours before now.
Chapter 86 · 0% Book details