← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 137

Sashe 137

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zasu yi mata musu Daddy yacewa Ya Musbah ya tafi da ita…..dan shi kansa ya ji mugun mugun haushi abunda ya ji Manu tana gayawa Yahanasu Yash d’in ya yi mata…ko a wanne irin Hali kake a ciki ai bai kamata ka bari a tafi da matarka a gaban idanunka ba!.

Duk watsewa suka yi aka barshi da Aslam a wajen…sai a lokacin Aslam ya dafa kafad’arsa yace”Allah ya kare gaba”
daga haka ya juya ya wuce ya tafi dan tabbas Yashjub yana buk’atar space!…ya san menene damuwa da k’unci shiyasa suna yin ido biyu tun d’azu ya fahimci Yash yana cikin masifa..dan haka ya tafi yana mai yi masa addu’ar Ubangiji ya yi masa maganin damuwarsa……

Shi Yash bai ma lura da Abbakar ba sai da aka gama watsewa chan ya hangesa a zaune ya yi shiruu ya yi tagumi..kafesa kawai ya yi da idanuwa suna had’a idanu ya mik’e ya nufosa,a zuciye Yashjub shima ya nufi Abbakar d’in tabbas yau kam ko shi ko Abbakar…..
…..suna zuwa kusa da juna Abbakar ya yi sauri ya durk’usa a gaban Yash ya rik’e k’afafuwansa da hannu bibbiyu ya fashe da kuka…
Da farko Yashjub ya d’auka wani sabon plan d’in Abbakar d’in ne yin hakan,shiyasa a zuciye ya fara k’ok’arin wafce k’afarsa sai da ya ji Abbakar d’in yana kuka yana neman yafiyarsa ya na zaiyyano masa dukkannin abunda suka yi shi da su Yasira da Kausar tukunna ya fahimci nadama ce ta zowa Abbakar d’in dan haka zuciyarsa ta d’anyi sanyi jikinsa ma haka…..

Babu abunda Abbakar ya b’oye bai gaywa Yashjub ba ya kuma nuna masa proof a wayarsa sannan ya gayamsa yadda suka yi da Manu d’azu komai ya fad’a tun daga farko har zuwa k’arshe…
Dare ya yi sosai amma hakanan Yash ya tisa k’eyar Abbakar suka nufi gidansu Manu…….
Da farko cewa ta yi bazata sauraresa ba Allah ya so Baba ya ji lokacin dan haka ya fatattake ta zuwa parlourn Bak’i wajensu…ta yi mamakin ganinsa tare da Abbakar amma sai kawai ta zauna ta juya kai ba tare da ta kula ko wannen su ba….

Kamar yadda Abbakar ya yi masa bayani hakanan ya maimaita sak a gabanta ya tashi ya kaimata proof ya nuna mata a wayrsa yana kuka ya durk’usa a gabanta yace”dan Allah dan Annabi ta yafe masa!!!…….”

Manubiya ba ta iya kallonsa ba da kyar tana kuka sosai ta mik’a masa wayarsa tace”ya tashi ya fita ba ta son ganinsa!”
Dama ya yi expecting hakan daga gareta amma ya ji dad’in nauyin da ya sauk’e a kansa dan haka ya mik’e ya yi musu addu’ar Allah ya barsu tare ya kawar da idanun mak’iya daga kansu daga haka ya sa kai ya fice….
…..sometimes we have to live with the fact that ba fa komai ne abunda muke so zai zama mallakinmu..asalima wasu lokutan abun kwata kwata ba alkhairi bane a rayuwarmu!sannan idan muka tilasta muka nace akan sai mun samu abunnan to fa in banda koma baya da dak’ile kai babu abunda muke yiwa rayuwarmu!!
Tabbas inda ace ya raba Manu da Yash da ya tarwatsa rayuwar mutane uku da shi da ita da Yash har gaban abada kuma ba zai tab’a samun farin cikin da yake nema ba.Ya godewa Ubangiji da ya wayar masa da kai ya nuna masa gaskiya..ya san yana son Manu amma zai yi k’ok’ari ya manta da ita ya yi moving on a rayuwarsa ya nemi farin ciki ya daina mayar da kansa baya yana b’atawa kansa lokaci.

Abbakar yana fita Yash ya mik’e ya k’arasa inda Manubiya take nan a zaune tana kuka….a hankali ya sa hannu ya dafa ta wanda hakan ya sanya ta juyo da sauri ta fad’a jikinsa ta fashe da wani irin kuka..cikin kukan tace”yanzu ta tabbata ba zan haihu ba kenan??”

Da sauri ya sa hannu ya toshe mata Baki yace”fad’arsu ba fad’an Allah baceba sannan abunda suka yi miki bai isa ya hanaki haihuwa ba sai da izinin Ubangiji..ki kwantar da hankalinki tun a wanchan lokacin na fara shirye shirye akwai Doctor d’in da za ki gani a Berlin anytime from now zai bamu Ap soon na sani…ki daina kuka Manu na san Ubangiji zai bamu haihuwa InshaaAllah Allah ba zai barmu haka ba..na dad’e da yin believing akan zaki haifa mini Yara inshaaAllah zamu zama parents muma...”
Sosai ya ci gaba da kwantar mata da hankali har sai da ya ga ta daina kuka hankalinta ya d’an kwanta tukunna ya kyaleta.

Cikin sharar hawaye ta d’ago ta kallesa tace”inaso insan abunda yake damunka tun kwanakin baya..kar ka b’oye mini dan na san kana da damuwa bayan wannan!!”

Shiruu ya yi ya d’an k’ura mata ido kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace”Ya’isha ta rasu!rana d’aya suka rasu ita da Inna..ban san wanne tudu wanne gangare ba amma Mommy ce sila,a jeji ma taje zata binne ta ko sutura ba ta yi mata ba….
kuma har yau bata gayawa kowa ba…
Tun a ranar nake k’ok’ari nake so in d’auko y’an sanda a tafi da ita amma na gagara kulle mahaifiyata da Hannuna..kuma shirun nan da na yi ni kaina na san ban kyautawa Ya’isha da kaina da kowa ba!!!….”
Kukan da ya ci k’arfinsa ne yasanya sa yin shiruuu…kafin chan yace”Mannubiya na tsorata da lamarin Mommy na firgita sosai Mommy ta firgita ni al’amarin ya gigitani da yawa….”
Yadda yake kuka yana magana ne ya sanya ta rungumesa itama tana kuka kamar ranta zai fita…..
Sun fi awa d’aya a parlourn kafin ta je ta samu Baba Allah ya so ta bai yi bacci ba nan tace masa”za su tafi!”
Dare ya yi sosai sosai amma bai Hana ba dan ya ji dad’in shiryawar da suka yi tunda har tazo ta ce zata tafi ya san komai normal dama bayaso ta yi yaji ta zo ta kwana masa a gida….hakanan ya je suka yi sallama da Yash ya sanya musu albarka..suka wuce gida tare…..:

Washegari da sassafe su Manu suka hau shiri dan za su fita su fara shirye shiryen tafiyar da ta taso musu saboda jiya cikin dare suka yi receiving letter daga babban likitan da zata gani a Berlin..zai gansu in the next ten days.

Tun a masallaci ya sanar da Daddy yace masa”Manu tun jiya ya dawo da ita yau kuma zasu fara shirye shiryen tafiya zataje ta ga Doctor”…
suna gama shiri sun fito kenan Yashjub yana reverse kawai suka ga Munirat ta kutso kai cikin gidan sanye da baban Hijabi ta yi k’iba sosai fuskarta ta kukkumbura dan da kyar Yash ma ya iya ganeta Manu ce dai tana ganinta ta ganeta.

Fita duk su biyun suka yi suka tsaya suna kallonta har ta k’araso garesu…….

Jiya su Junior basu koma gidansu ba direct daga wajen Manu gidan Daddy suka wuta kawai suka kwana a nan!
Suna zaune da shi da Daddy Yasmeen Yahanasu da Ummi suna breakfast Yash da Manu suka shigo….
Murmushi Daddy ya yi haka itama Ummi da suka gansu
Suna shirin yin magana Yash ya k’araso cikin parlourn ya ware murya ya shiga kwala kiran “Kausar!!!”
Da mugun k’arfi.
Chapter 137 · 0% Book details