← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 137

Sashe 129

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dama ta gama girki dan haka ta jere girke girken da ta yi akan dining…..gwaggo tana tafiya ta d’auko disposable plate mai murfi ta saka masa pt d’in a ciki ta rufe ta ajjiye kamar had’in baki dai dai nan ya turo k’ofa ya shigo…murmushi suka sakarwa juna kafin ya ware hannuwansa alamun ta zo garesa kamar jira take yi kuwa ta tafi ta fad’a jikinsa ya mayarda hannuwansa ya k’ank’ameta yana mai sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya a baiyyane dai dai satin kunnenta yace”I love you!irin sosai d’inna!!!”
Dariya duk suka yi,sun jima a haka kafin ta jasa zuwa dining d’in ta zaunar da shi..
Murmushi ya yi yace”yau kenan tun kafin in yi wanka za a bani abinci?”
Itama murmushin ta yi tace”Inada surprise ne”
Wani irin kallo ya shiga yi mata yana murmushi kamar zai cinye ta kafin yace”to bismillah,zuba mini.”
Waje ta nema ta zauna a kan cinyarsa ta zagaye wuyansa da hannayenta tukunna tace”special na girka maka…shi yana ciki ga kuma waenanna a kan dining…
A cikin kalmomi biyun da zan fad’a yanzu ka d’auki guda d’aya ‘Ni’ ko ‘Kai’”

Dariya ya yi sosai har sai da kyawawan hak’oransa suka baiyyana kafin yace”abun game ne kenan?yau babyna tab’ara take ji naga alama.
Shikenan ki gama taki nima zan yi tawa!”
Ya fad’i hakan yana mai kashe mata ido d’aya kafin ya sakata a jikinsa sosai tukunnan yace “na zab’e ki!”
Dariya tayi sosai tace”ka yi winning! Ka zab’i in kawo yanzun kenan!
Inda’kai’ ka d’auka da sai nan da dare tukunna zaka samu special d’in.”
Mik’ewa ta yi taje ta d’auko disposable plate d’in ta dawo ta
koma
Inda take zaune nan kan cinyarsa ta zaune rik’e da plate d’in tace “gashi”
Murmushi ya yi yana kallonta tashi d’aya ya sa hannu ya bud’e…
….
Shiruuu ya yi yana kallon pt d’in dake nan ajjiye a kan tissue wanda yake nuna masa positive….
Yadda ya yi shiruu ya k’ame ya sanya ta d’an d’ago ta kalli fuskarsa shima a dai dai nan ya kalleta da Idanunsa da suka yi jazir hawaye ya fara zirara bakinsa yana karkarwa yace”d-daaa g-ask-e??”
Jin jina masa kai ta yi ta kamu free hand d’insa ta d’aura a kan cikinta tace”Eh!!”
Bata Ida rufe bakinta ba a zafafe ya had’e bakinsu waje guda ya shiga kissing d’inta yana mai sake sakata a jikinsa kamar wanda zai mayar da ita cikin cikinsa…..

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cike da zallar farinciki….
Najeeb ya sauk’a ya mayar wa da Yash gaba d’aya companies d’insa da businesses d’insa dan shima aiyyukansa sun yi masa yawa dama kawai manage yake yi…Ummi da Mama kuwa shi kansa Daddy ya fad’a ya sake maimaitawa”ko a labari ko a film bai tab’a ganin kishiyoyin da suka had’e Kai suke shimfid’a rayuwar asalin zaman lafiya na tsakani da Allah da kwanciyar hankali ba!”.
Gashi sun rungumi su Yasira ta ko wanne b’angare sun zame musu Uwar da sukayi rashin sa’arta idan ka shigo gidan in ba fad’a akayi ba ba za ka tab’a sanin mahaifiyarsu bata cikin gidan ba dan su Ummi basu rage su da komai ba.

Tsakanin su Yasira da Manubiya ma haka abun yake dan sosai suke nuna mata da gaske fa sun shiryu..sosai suke kyautata mata suke mutuntata da nuna mata asalin k’auna da tsantsar tattali…hakanan suke girmama su Ummi da Mama ma sun d’aukesu iyaye suna zaune da kowa tsakani da Allah rayuwar gidan asalin jin dadin da farin ciki zallah gashi arzik’in Daddy da Yash sai sake bunk’asa yake yi.

Har islamiyya su Yasira suka koma saboda su samu su yi repenting da kyau su kama Allah dan da gaske sun shiryu shiryuwa ta tsakani da Allah sun yi danasanin abubuwan da suka dinga yi a baya….Miji ne dai ko saurayi har yau shiru apart from Yaha babu wadda take da mashinshini a kaff cikinsu.

Manu kam wani zubin har kuka take yi…saboda indai farin ciki ne da tsantsar soyayya ta miji da dangin sa to itakam ta samu tabba Ubangiji ba yadda ba ya iyawa ya kan chanja situation daga bak’ik’irin ya koma fari k’alll!!.
Bayan dangin miji da Miji ita kanta rayuwarta da rayuwar gidansu abun sha’awa ce ga kowa tabbas ta samu komai itakam,Alhamdulillah.

Daddy ya so su Manu su tashi su yi gidansu a daban dan shi gani yake yi kamar an takura musu amma ita da su Yasira suka ce sun fi jin dad’in zaman taren dan haka aka sake gyara mata side d’in Yash suka ci gaba da zama.

Yahanasu itama an saka ranarta da Dr Engr Kamal haka Hadiza itama an bayar da ita a Ya Musbah har an saka rana suma.
…………

Bayan shekara bakwai.

Babu zancen Yusuf babu labarinsa har gobe an gagara amsoshi.

Company da businenss d’in da Yashjub ya so ya d’aura Yassir akai shi ya bawa Ya Musbah kuma abun ya bunk’asa ya yi albarka fiye da tunanin mai
tunani….
Ya kammala degree d’insa a buk yayi masters d’insa a cairo duk a fannin business admin
Allah ya dafa masa kasuwanci duk wanda ya tab’a sai ya yi albarka yanzu haka a kaff layin nasu babu wanda ya kaisa bud’i da arzik’i jama’a har maula suke zuwa wajen Ya Musbah haka masu buk’atar taimako suma…daga ya dawo daga tafiya zaka ga ana layi a kofar gidan duk ana son ganinsa….
Ya gyara musu gidan nasu ya mayar musu hawa biyu ya kyalkyalce musu shi ta koina kana shigowa cikin layin gidan ne zai fara d’aukar idanunka.

Shekaru uku baya da suka wuce su Baba habu suka yi wata mummunar gobara babu dai wanda aka rasa duk an fitar dasu on time ammafa ko cokali basu samu sun d’auka ba komai sai da ya k’one….a lokacin ya Musbah ya fara tashen arzik’insa shi ya kwashessu ya kama musu haya na shekara d’aya…a cikin watanni tara aka gina musu gidaje masu bene hawa d’add’aya part uku har da anty umma da babban parlourn kaka mallan….
Sai da su Baba Habu suka yi da gaske tukunna kunya danasani da nauyin Baba suka barsu suka zo gidan suka yi godiya suna kuka sosai suka nemi yafiyar Baba bisa ga abunda suka dinga yi masa!!….murmushi kawai Baba ya yi ya ce musu komai ya wuce burinsa kawai shi a yanzu a yi zumunci bai rik’e kowa a cikinsu a rai ba!
A rayuwa kowa ya kanyi kuskure the best part shine idan mutum ya gane kuskurensa ya gyara shi kuma wanda aka yi wa laifi ya yi k’ok’ari ya yi hak’uri kar ya ce zai rama ta hakan ne za a ga dai dai komai ya tafi bisa tsari.”

Ai kuwa Baba ya ga zumunci ganin idanunsa kuma yana kan ganin zumunci saboda a halin da ake ciki Hatta d’inki tare Baba Habu da Uncle suke yi da shi komai iri d’aya wani zubin har agogo iri d’aya suke sakawa gidansa kuwa suna yawan zuwa kasancewarsa k’aramin cikinsu ya sanya shima yake zuwa nasu gidajen sosai dan ya hutashshesu.

Anty Umma kuwa tun da akayi gobarar da ta dawo gidan Baba har yau su Inna sun ce kawai ta zauna tare da su…Gwaggo Suwaiba ma tana yawan zuwa Mijinta har yau yana nan amma fa ciwo ya ci ya cinyesa ko tafiya ba ya iya yi haka nan take fama da jinya.

Kaka mallan shima yanzu kam tun shekaru shidda baya ko bakin magana ma babu yanzu kuwa ba ma ya sanin waye a kansa.ciwo ya ci ya cinyesa sosai.
…….
Hannun Ya Musbah a bud’e yake sosai shiyasa yake dad’a samun bud’i kwata kwata bashi da rowa bashi da kyashi…Ya Nafi’u ma ya samu chanjin aiki yana da rufin asirinsa amma duk da haka Ya Musbah sai da ya siya masa gida ya chanja masa mota tukunna hankalinsa ya kwanta sannan har gobe kayan abinci kayan sakawa na sa da Yaransa biyu mace da Namiji da na matarsa kullum ya Musbahn ne yake siya k’iri k’iri ya hanasa yin duk wata hidima ya d’auke masa komai dan idan duniya da alk’awari ba zai tab’a mantawa da Nafi’u ba.!
Duk wani business da yake yi sai ya san yadda ya yi ya saka Nafi’u a ciki shima ya samu abunda ya samu.
Sosai rayuwa ta chanja tables suka juya Yaransa uku a halin yanzu duk maza dan Hadiza ta Haifa masa Yashjub da Naf’iu.

Jidda itama suna zauna cikin Jin dad’i dukiya da daula da tsananin k’aunar juna suna son juna ita da Ammi Sosai suke zamansu lafiya….Yaranta uku biyu mata d’aya Namiji ta kammala karatunta a northwest yanzu haka tana businesss.

Siyama ce mai Yaro d’aya saboda sai da ta haihu tukunna ta dumfari karatu shiyasa suka tsayar akan sai ta gama sai ta d’aura daga inda ta tsaya sosai suma suke zaune lafiya dan shima Najeeb mijin marainiya ne ma sha Allah.

Yahansu ta auri Kamal wanda a yanzu shine governor na Jahar Kano state dan shekara d’aya asalin governor d’in ya yi ya yi ya rasu shi ya maye gurbinsa aka basa ruk’on kwarya da aka zo zab’e kuma jama a suka sake zabaar sa.

Yasmeen ta yi aure.

Munirat ma ta auri Alhaji bashir (asalin saurinta)matarsa ta rasu ata sanadiyyyar ciwonta da ya motsa mata haka kurum..ta yi jinyar sati biyu Allah ya karb’i ranta. Ko da ya dawo yace zai auri Munirat su Ummi basu b’oye masa komai ba nan yace ya ji ya gani ai k’addara tana kan kowa kuma har Yaron zai rik’e..Aikuwa ya rik’e amana dan shekara ta hud’u suke a ciki amma bai tab’a nuna mata rashin mutunci ko
gori ko banbanci a kan d’anta ba sosai ya had’a da Yaronta wanda ta Haifa masa da y’ay’ansa na wajen uwargidansa marigayiya da d’an gidan Yassir d’in yake kula da su tsakani da Allah itama kuma Munirat ta rik’e masa Yara bilhakk’i da gaskiya….

Ya’isha da Junior sun koma Uk da zama d’ansu d’aya yanzu take da cikin na biyu,suka zamansu Alhamdulillah.
Hajiya Mama kam k’iri k’iri Ummi da Mama sun yiwa Mom wayo sunce suma ta bari su samu nasu ladan.
Chapter 129 · 0% Book details