← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 130 OF 137

Sashe 130

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Za ku sha mamaki idan na ce muku Abbakar Yusra ya aura.
Wanda itance ta ce ta ji ta gani duk duniya ita shi take so…da farko farko ma b’oyewa tayi sai da ta ga k’aunarsa ta na shirin yi mata illah tukunna ta fito ta fad’a…da farko su Manu k’in yarda suka yi amma da suka ga k’anwar tasu ta mato da yawa kuma Abbakar ya yi nadama sai kawai suka nemi zab’in Allah ai kuwa tunda aka fara maganar har aka d’aura aure komai sumul…yanzu haka Shekarar su biyu da aure suna zaune a garin Abuja inda yake aiki d’ansu d’aya mai sunan Daddy.

Muhsin ma yana Abuja yana karanatar English a nile university level 1.

Yasira ce dai Allah ya d’aura mata jinkirin aure dan sai yanzu tukunna Allah ya fito mata da miji alhaji isma’il matansa biyu itace ta uku…yanzu haka an saka rana wata uku….

An yankewa Mommy hukuncin d’aurin rai da rai….kisan da suka saka aka yiwa mallan lawal..mutuwar Ya’isha da kuma d’an Khadija na farko wanda ita da Baba Larai suka dinga d’urawa mata magani suka kashe tun a ciki.

Dama tun kafin y’an sanda su tafi da ita ta daina gani…Shekarar ta d’aya a prison mugayen prisoners suka jefa mata bonk gado na k’arfe a k’afafuwanta,ba a bata kulawa da wuri ba
har sai da k’afafun suka rub’e hakanan tana ji tana gani sai yankewa aka yi..kuma har yau an gagara a samu yadda aka yi akai mata transfer zuwa gidan gajiyayyun hakanan take fama a prison ba ido ba k’afa.

Manubiya da Yashjub Yaransu uku..ta farkon mace takwarar Hajiya Mama ‘Yahanasu’ suna ce mata Noor sai maza biyu masu sunan Baba da Najeeb,
Yaran Masu tsananin shiga rai kamannin Manu duk suke d’aukowa gasu da k’ok’ari da wayo tubarkallah.
Itama ta kammala karatunta ta yi masters yanzu haka PhD takeyi kuma tana lecturing a buk…..
A ko da yaushe idan Manubiya ta kalli rayuwarta sai ta yi kwallah….Duniya rawar y’an mata
Kasancewarta y’ar talaka talakan ma maskini hakan bai hana Ubangiji yin ikon sa a kanta ba dan gashi abunda mutane wasu suke gani impossible ita ya faru a kanta kuma tana rayuwa a cikinsa…ta samu mai masifar sonta wanda sam ba class d’insu d’aya ita da shi ba! ta aura kuma ya sota yana kan sonta tsakaninsa da Allah

Tabbas komai yayi farko zai yi k’arshe farkon rayuwarta da kuma tsakiyar rayuwarta (lokacin da su mommy suka sakota a gaba kowacce hanya ta kulle) inda ace wani zai ce mata za ta ji wannan dad’in da take ciki a yanzu ta samu wannan kwanciyar hankalin a gaba da ba zata tab’a yarda ba..amma with du’a everything find its place perfectly…tabbas in da Rabbana komai ba wahala.

Mugu ba shi da riba,musamman ma mugun da yake zalinci yake cin riba baya tuba kullum ribar kawai yake gani!Tabbas irin su a rayuwa sun fi kowa wulak’anta daga k’arshe sannan kuma azabar su ta fi tsanani ranar gobe k’iyama.

A ko da yaushe idan mutum ya yi hak’uri ya dogara da Allah Tabbas komai mai wucewa ne kuma komai akwai lokacin sa.

A bangaren Yashjub shima babu abunda zai ce sai Alhamdulillah!!ga matarso Allah ya basa ga Yara Alhamdulillah ga Mahaifiya ta gari ga mahaifi mai k’aunarsa ga y’an uwa masu sonsa ga arzik’i dukiya farin ciki da jin dad’i da tsantsar kwanciyar hankali ya samu yana kan samu ta koina!!tabbas a ko da yaushe bashi da kalmar da ta fi dacewa yacewa Ubangiji sai ‘ALHAMDULILLAH!!!!!.’

Alhamdulillah!Alhamdulillah!!
Na godewa Allah da ya bani ikon kammala littafina mai taken suna’MANNUBIYA’.
Kuskuren da na yi a ciki Allah Ubangiji ka yafe mini,darussan da suke a ciki Ubangiji ka sa mu amfana.

GODIYA TA MUSAMMAN GA
Nazeefa Sabo Nashe.
Da
Maryam Bulama.
Ba zan tab’a mantawa da ku ba,alkhairin Ubangiji ya isar muku a duk inda kuke.

JINJINA da GODIYA mai tarin yawa ga mutanena
Oum Zahra
Maman Aliyu
Fauziyya Gwandu
Hannah OC
Binta Muhammad
Yumin Aliyu
Shamsiyya wada
Ummi Muhammad
Indo Aysha
Fati Abbas
Kudra
Maman Hafeez
Zahra Auwal
Iymert
Habiba Idris
Salmerh
Maryam Mustapha
Hannah collection
Mrs MB
Sadiya
Oumhanan
Da duk wani member na group d’in MANNUBIYA group one and two..ba zan tab’a mantawa da ku ba,ba ni da bakin gode muku sai addu’a wallahi!na gode na gode sosai Allah ya bar zumunci ya kuma kare mini ku kullum da ko da yaushe!na gode kwarai!!
Ina muku fatan alkhairi.

FATAN ALKHAIRI ga
duk wani member dake Mikiya Writers Association,Rabbi ya dafa mana ya sake had’a kawunanmu.

Taku har kullum
Humayrah Bulama.
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 43
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Ya Musbah yana tafiya su Inna ma suka fara k’ok’arin shiga domin suma su samu su kwanta barci, dan Baba shi kam ya jima da wucewa d’akinsa tun lokacin da suka gama yiwa Yash da Daddy gaisuwa,ya wuce abunsa…

Hijab d’inta ta cire ta linke ta ajjiye a kan dardumar tukunna ta d’auka ta had’a ta yi folding d’insu tare ta tsaya tana kallon Hannun kujerar inda ta ajjiye hularta tun d’azu da Magrib da zata yi sallah amma da ikon Allah har yanzu ba ta ganta ba.
Manubiya ta kalla ta kalli hular kanta wadda gwaggwo Suwaiba ta basu tsarabarta su biyu iri d’aya tace”Manu hular ki ce a kanki ko?
Ni Ina tawa??”
Murmushi Manubiya ta yi tace”
Dama na sani!”sai kuma ta d’aura da cewa”ai dama kinsan Siyama tace itama kalar take so..ba ta son kalar tata ita da Jidda!
bani da tantama itace ta d’auke takin a tunaninta tawa ce na ajjiye shine ta d’auke ta tafi da ita!”.

Shiru Inna ta yi kafin tace”Anya kuwa?
Kuma inda ace ita ta d’auka ai da na san za ta ajjiye tatan..
kuma ai kafin Magrib Siyama ta tafi,ni kuma sai da na zo yin sallar Magrib d’infa tukunna na cire!.”

Cikin tarar numfashinta gwaggo Suwaiba tace”To,watak’ilan mai sunan Baba ne ya d’auka ya saka a wani wajen
,yanzu mu je mu yi barci idan Allah ya kaimu gobe da safe sai a duba!
Idan ma ba a samu ba sai in je kasuwa in siyo yadi kalarsa ai ba za a rasa ba duk ku hud’un sai in had’a Hadiza ta kai tela ya d’inke a yi muku iri d’aya,kinga an huta ai ko?”

Dariya Manubiya ta yi kafin tace”Allah ni fa Ina tunanin Siyama ce ta d’auke! ta yi tunanin tawa ce saboda fa tun da ta ga tamu(ni da Inna) tace ita za ta yi anko da Inna kuma kalar ta fi so shine favorite colour d’inta shiyasa ni kuma tun d’azun har yanzu da ta tafi ma ban yarda na cire ba!”tana dariya ta ci gaba da cewa”wuyan Hijab d’ina ma ya yi mini kad’an fa amma haka nake d’aurawa a kan hular ina yin sallah tun d’azu”.
Ta fad’i hakan tana dariya…..daga haka suka nufi d’aki gaba d’ayansu…ita dai Inna abun ya d’aure mata kai saboda har bayan tafiyar Siyama fa hularta tana kanta…amma kawai sai ta tsaya akan watak’il mai sunan Baban ne ya d’auka ya jefa a wani wajen dan haka ta bari akan gobe da safe idan Allah ya tashemu lafiya sai ta duba!!!!.

Manubiya da gwaggo Suwaiba ne kawai suka shiga suka kama ruwa suka yi alwallah dan ita Inna da alwalarta,dardumarta da Hijab d’in kawai ta ajjiye ta kwanta saboda haka kurum ta ji ta wani iri ga kasala!!!
da mugun kyar ma ta iya kaiwa kan gadon,tana kwanciya kuwa wani wahalallen barci marar dad’i ga takura ya yi awon gaba da ita.
Su kansu su Manu sun yi
mamakin baccin da Inna ta yi nan da nan gashi a karkace ma ta kwanta amma sai sukayi tunanin maybe ko gajiya ce,Manu ce ta d’aura mata Kai a kan pillow tana mamakin yadda take fitar da numfashi da kyar daga haka ta rufa mata abun rufa ta d’an rage k’arfin ac dan a tunanin ta sanyin ne ba ta so…daga nan suka d’an tab’a hira ita da gwaggo Suwaiba suka yi addu’o’i suka bi gado suma.

Da asuba!!…kiran sallar farko ne ya farkar da Manubiya da Gwaggo Suwaiba.
Band’aki gwaggwo Suwaiba ta wuce yayinda Manubiya ta d’an zauna a kan gadon ta yi shiruu sai da ta wartsake sosai tukunna ta juya cike da mamakin Inna ta shiga tashinta dan kullum idan suka farka a zaune a kan darduma suke tadda ita.
Sau uku ta kira sunanta tana mai d’an tab’a mata Hannu amma shiruu…cikin tashin hankali ta mik’e ta k’arasa ta kunna wutar d’akin ta koma gareta da sauri ta shiga k’are mata kallo tana kiran sunanta kafin ta zauna a daidai kanta a firgice ta d’an shafa fuskarta ta ajjiye Hannunta daidai saitin hancinta.

A firgice cikin tsananin masifaffen tashin hankali firgice da tsoro ta tashi da ga kusa da ita da mugun sauri ta ta d’an ja baya ta tsaya a kanta tana ci gaba da kallonta jikinta yana wani irin karkarwa!
Daidai nan gwaggwo Suwaiba ta fito daga band’akin…yanayin Manubiyan ne ya sanya ta yi saurin k’arasawa inda take ta ruk’o hannunta itama idanunta suna a kan Inna tace”me ya faru?”
Ta yi mata tambayar jikinta itanma yana karkarwa dan yanyin yadda Innar take a yashe da kuma yanayin Manubiya sun mugun firgigita.

Juyowa Manubiya ta yi ta kalleta dai dai nan hawaye suka samu damar b’alle mata cikin tashin hankali tana magana da kyar tace”ba ta numfashi kuma jikinta ya yi sanyi”
Ta yi mata maganar tana mai nuna mata Innar da yatsa…

Da kyar Gwaggo Suwaiba ta samu ta yi namijin k’ok’ari wajen k’arasawa inda Innar take ta zaune a gefenta ta shiga dubata…..tashi d’aya ta fashe da wani irin rikitaccen kuka ta shiga ambaton “innalillahi wa inna ilaihirrajiun!
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!!”.

Luuu!!! haka Manubiya ta tafi ta zube a wajen sumammiya…….

Sama sama take jin muryar ya Musbah shima yana kuka yana
yayyafa mata ruwa yana kiran sunanta!
A hankali ta shiga k’ok’arin bud’e idanunta kanta yana wani mahaukacin sarawa…dishi dishi ta fara gani kafin ta samu idanunta suka ware tarr take kallon fuskar ya Musbah shab’e shab’e da hawaye wanda hakan ya sake tabbatar mata tabbas Inna ta rasu!!!
Chapter 130 · 0% Book details