← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 137

Sashe 45

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi d’aya idanuwansa suka yi jajir ya juya ga Yassira
tana shirin yin magana ya rufeta da duka,hatta Yasmeen da Yusra saida suka karb’i
rabon su amman sun samu sun zille dan Yassira ya rik’e,ita ta fi
fusatashi.dan dama Ummi ba ta dad’e da gama faiyyace masa abunda suka aikata a gidan Yash da gidansu Manubiya ba…tashi d’aya daga jin zancenta ya fahimci ashe k’arya suka shirga masa d’azun da suka dawo,dama yana jin haushin su akan hakan yanzu kuma ya ga wannan shirme da aika aikar da suka yi shiyasa ya fusata ba kad’an ba.”[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 21
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Abunda bai tab’a yi ba kenan’dukan y’ayansa’.Shi da kansa yana jin zafin dukan nasu da yake yi a halin yanzu amman kuma ya zama dole a taka musu burki dan tabbas abun na su ya zarce misali.

Waya Mommy ta karb’a a hannun Yadira wadda ta b’uya a bayanta,tashi d’aya Mommy ta danna kiran Yassir,dan sun gagara kwatar Yassira a hannun Daddy.Yana d’auka tace”dan Allah Yassir ka yi maza ka zo yanzunna.”

Sai da kyar tukunna daidai
Yassir d’in yana shigowa cikin parlourn
Ummi ta samu ta janye Daddy
yana huci….babu abunda ya fi d’aga masa hankali kamar Yahanasu da ya gani a kwance dan ko numfashi ma yaga kamar ba ta yi…idan sun daki Munirat saboda Allah
Yahanasu da Ummi ai ba sa’anninsu baneba.!

Cikin kuka Mommy ta matso tace”a kanta ka dakar min y’ay’ana mata ba maza ba??
yanzu kai a ganinka ya dace ace ka yi musu wannan dukan??dan ni a ganina ko
Yadira ta wuce duka ballantana Yassira!Yassira fa
ka daka!ka bud’e idanunka da kyau ka gani”

Cikin rashin jin dad’i
Ummi tace “Tabbas Mommy kin tabbata wadda ba ta san abunda ya kamata ba,dan an
daki Yassira?kalli Yahanasu fa ko motsi ba ta yi,kalli goshin Munirat duk jini,sannan ni kaina Yaran nan ba su kyaleni ba amman shine……”
Cikin tsananin b’acin rai
Mommy ta yi kan Ummi kamar za ta daketa ne tace”Saddik’a!
zan miki first and last warning!daga yau duk wani abunda ya shafe ni!ni ko y’ay’ana karki sake shiga!babu ruwanki da mu ba ruwanki da rayuwar mu ba ruwanki da damuwar mu!,ban san wanne Irin naci maita jaraba da shishshigi Allah ya yi miki ba…duk inda ake case d’in da bai shafeki ba a cikin gidan nan to sai an ganki a wajen.
Har ga Allah kin takurani ko tari ki ka jiyo na yi sai kin zo wanne irin jaraba ne wannan??”

Sakar baki kawai Ummi ta yi tana kallon ta…Baba larai kuwa ji ta yi kamar ta rufe Mommy da duka,dan yanzu kam ta san Mommyn ta riga ta gama nunawa Ummi wacece ita tsirararta.

Ummi tana shirin yin magana Daddy yace mata”wuce ki tafi
sama ki jirani a d’akina”
Har za ta yi musu sai kuma kawai ta juya ta wuce saman zuciyarta fall cike da mamakin Mommy,tashi d’aya itama Munirat ta mik’e ta nufi saman tana mamakin yadda ko kallon inda take Yassir bai yi ba amman ya nufi Kausar ya je ya durk’usa a inda take yana ta faman lallashinta kmr shima zai fashe da kuka.Sai da Ummi ta biya da Munirat d’akinta ta bata paracetamol ta goge mata ciwon da ta ji da spirit ta saka mata plasta tukunna ta nufi chan sama ta shige bedroom d’in Daddy ta zauna zaman jiransa kamar yadda ya ce.

Suna wucewa Daddy ya dakawa Yassir tsawa”Tashi a wajen ka kyaleta!bansan mai ya faru ba amman na san itace ummulabaisin abun nan da ya faru!
Cikin rashin jin dad’i
Yassir ya mik’e yace”Haba Daddy…”
Wata uwar tsawa Daddy ya kuma daka masa tare da cewa
“na ce ka kyaleta!ka zo ka tayani kai Yarinyar nan asibiti ko?”
Kamar Yassir zai fashe dan takaici,haka nan ya na ji yana gani ya baro Kausar ya zo ya durk’usa ya kinkimi
Yahanasu suka fice tare da Daddy ko kallon Yassira wadda take durk’ushe a wajen Daddy bai kuma yi ba….
Ita ta ma rasa ta yi kuka ne ko ta yi ihu!ba ma ta san ta Ina za ta fara ba,yau ita ce Daddy ya daka haka anya ba mafarki takeyi ba kuwa?me ya faru?me ya shiga jikin Daddyn nasu tashi d’aya yau haka……
Su Yassir suna fita
Baba larai ta matsa inda take
ta mik’ar da ita ta zaunar da ita ta shiga lallashinta,sai a lokacin ne ta samu ta fashe da wani irin kuka kamar za ta mutu tace”Nima fa na ji ciwo
kalli goshina!sannan cheeks d’ina gaba d’aya ciwo suke yi min amman ki duba ki ga yadda aka tafi kai Yahanasu asibiti ni aka barni anan.”
Gaba d’ayansu kanta suka nufa banda Kausar wadda ta yi suman wucin gadi.
A hankali Mommy ma ta k’arasa wajen Yassirar zuciyarta tana wani irin tafarfasa..ta san ta tsani Ummi tsana ba ta wasa ba ta tsani the sight of her ko labarinta bata son ji amman bata tab’a jin tsanarta
ta masifa kamar ta yau ba!..a kanta aka dakar mata y’ay’a!
Inaa ba zai yiu ba da sake..a tunaninta Ummi k’aramin alhaki ce ashe abun ba haka yake ba dan gashi da idanunta ta gani kuma ta fahimci abunda ta yi ta ke kuma kan yi akanta sam ba ya aiki!..babu abunda ya fi bata takaici irin yadda Daddy yace “ta je ta jirasa a d’akinsa”
Ita kuma ta yi masa biyayya ta wuce d’ingui d’ingui ta tafi.

A b’angaren Yassira kuwa ta riga ta gama kai wa wuya!Wallahi Daddy ya kunna wuta a cikin gidansa da hannunsa,dan wallahi sai dai in ya koreta a gidan amman da Manubiya da Munirat da Yahanasu da Ummi sun shiga uku a hannunta…ita kanta tanajin tsoron abubuwan da zuciyarta take aiyyana mata ta aikata wa su Ummin!wallahi duk sai sun ci ubansu…..
Babu yadda Baba Larai bata so ta fahimtar mata da amfanin kissa da siyasa ba amman tashi d’aya tace”wallahi ita ta gama kissa da siyasa dan bata ga anfani da ribar yin hakan ba!saita nunawa ummi da Munirat nan fa gidan ubanta ne wallahi hatta Yahanasu sai ta gane kuranta,sai ta sake fahimtar cewa’ba ta fa da uwa!ba ta da gata!sun fi ta power a cikin gidan’.”
Cikin takaici Baba larai tace”Yasira wai ya Ina baki kina k’in karb’a ne?duk fa inda mata suke mata ne kuma dole kowacce da tata kalar power ku daina ganinsu kamar k’ananan alhaki za su baku mamaki!yanzu kalli abunda aka aikata muku duk a ta dalilinsu,kuma ina mai tabbar muku muddin kuka ci gaba da wannan shirmen wallahi wallahi this is just the begining….dan haka daga yau tunda har ga abunda ya fara faruwa to indai zan baku shawar ku d’auka hatta Manubiya dan Allah inaso daga yau ku nemi zaman lafiya da ita a gaban idanun su Daddy daganan sai mu san abunyi ta kark’ashin k’asa…”
Cikin katseta Ya’isha tace”Baba larai munfa gama siyasa,mu da gidan uban mu!?amman ki ce sai mun yi musu siyasa?sun shigo sun mak’ale ta k’arfi da yaji and still ace ba mu isa mu fad’a a yi ba kenan?so kike a taka mu a maida mu gefe kenan?ko ya kike nufi?”
Cikin fushi Baba larai tace”wai ta ya zan yi muku bayani ne ku fahimceni?…ai ba su Ummi na ce ku yiwa siyasa ba!Daddy ne ba na so ya lura ko su fahimci kune masu takalo fad’a sannan suma kuma su Ummin ba wai b’aro b’aro za ku yi musu ba dole a sakaya wani abun idan ba hakan aka yi ba wallahi ina mai tabbatar muku shi Daddyn naku sai ya maidaku gefe su Ummin kuma su taka ku,idan bai zab’a muku mazaje ko kuna so ko bakwa so ya yi muku aure kun bar masa gida ba kenan!,kuna abu kamar wasu marasa lissafi!ki duba fa ki ga yadda muka gaya masa abunda ya faru a gidan su Manubiya d’azu da muka dawo amman ya ajjiye namu ya d’auki na Ummi saboda ita ta fi ki iya kissa!,dan ba ni da tantama itace ta zuga sa saboda tunda ta dawo ta haye b’angarensa ban sake ganinta ba sai yanzu da ta ji hayaniya tukunna ta sauk’k’o.”
Cikin tarar numfashinta Yadira tace”tun da suka dawo take samanshi.”Da sauri Baba larai tace”kin ji ko?ai na sani dama tunda na ji yana dukanki yana cewa”kina Babba amma ke ce mai janyo magana,ba za ki b’ata masa sunan family ba”na san cewa Ummi ta fad’a masa wani abun.
Dan Allah ku tsaya ku nutsu mu taru mu rufawa juna asiri,ina danne ku kuna biyewa dokin zuciya wallahi za ku kwashi kashinku a hannayen ku fa!kuma idan har hakan ta faru kar wadda ta kalle ni dan babu abunda zan iya yi infact yanzu ba kamar da baceba saboda a da da mutane masu sauk’in sha’ani muke dealing da sab’anin yanzu!ki duba fa ki ga Manubiya a yadda ta shigo cikin gidannnan ta k’arfi da yaji,sannan ita kanta Ummin yanayin aurenta da Daddyn naku komai a lullub’e yake,dan haka ya zama dole ku yi accepting fact ku daina ganinsu as k’anananun alhaki mu had’a k’arfi da k’arfi da wayo da komai tukunna shine za mu ci riba.Ya kamata ace mun dad’e da wuce wajen nan wallahi ku kuke dawo da mu baya,last time duk kun sauk’k’o kun yi yadda ya kamata ammman yanzu kun sake burkicewa dan Allah ku gyara.”
Chapter 45 · 0% Book details