← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 137

Sashe 31

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da Yassira ta ce mata “keee!”da d’an k’arfi,tukunna Ya’isha ta samu ta d’auke dubanta daga kan su sir Najeeb idanunta suna masu
ciccikowa da hawaye.
A hankali Yasmeen ta matso ta tsaya a gabanta ta d’an kareta daga Najeeb d’in tukunna tace”ba ce miki mukayi karma ki kallesu ba?amma kalli yadda kike..….
Shiruu Yasmeen d’in ta yi sakamokon hawayen da ta gani taff a idanun Ya’ishan suna shirin zubawa…ta san in har tace wani abun ko kuma tace za ta lallasheta to fa hawayen nan da suka cika suka yi mak’il sai sun fito duba da yadda idanunta suka cika taff sannan sukayi jaaa!hatta farar fuskarta ta yi jaa.

Hakan ya sa Yasmeen d’in kawai sai ta jaa hannunta da sauri suka nufi k’ofar parlourn.
Suna zuwa suka tura k’ofar
Allah ya so su akwai masu goge goge a ciki so k’ofar already a bud’e take, ba ta
tsaya da ita a parlourn ko sama ba dan hanyar saman akwai masu guga har biyu haka ma cikin parlourn,kuma ta san kafin su Isa kukan zai iya kufcewa Ya’isha shiyasa ta nufi d’akin da ta gani anan k’asan da ita.
Suna shiga suka rufo k’ofar tukunna Yasmeen ta cika mata hannu….ko magana Yasmeen ba ta yi ba Ya’isha ta fashe da kuka,da sauri Yasmeen ta toshe mata baki tana yi tana
dan kallon k’ofa cikin yin k’asa da murya tace”so kike a jiyo ki?
wanne Irin rashin lissafi ne wannan?
ce miki akayi wani abun ne a tsakanin su?ki tsaya ki tabbatr mana!.”

Ingije hannun Yasmeen Ya’isha ta yi kafin tace”Haba Yasmeen!yanzu ke ba ki fahimci komai ba?ba ki ga yadda yake murmushi yana kallon ta ba?,da kansa fa ya bud’e mata mota ta fito kuma ya mayar ya rufe abunda bai tab’a gigin yi min ba kenan.
Ki duba ki ga ya ganni fa mun had’a ido da shi amman bai zo inda nake ba ko sake kallon inda nake ma fa bai yi ba…..”
Kukan da ya taho mata ne ya sa ta kasa ci gaba da magana dan haka ta yi shiru da magaar ta ci gaba da kukanta.

Cikin d’an fad’a fad’a
Yasmeen tace “Yanzu kuka za ki tsaya kinayi ko tunani mai kyau??kalle ki yadda kika koma a cikin y’an sakannni
saboda shi wanda hakan yana nuni ne da tsananin son da kike yi masa,dan haka sai ki tashi ki nemi mafita tun kafin dare yai miki ba wai ki tsaya kina kuka ba.
Sannan kar ki bari su ga kukan ki ballantana su rainaki.
Tun farko kuma ai ke kika yi wasa da damarki,abunda naketa gayawa Yadira akan Junior kenan amman sam ta k’i fahimtata..haka kuke sai kun shure abu da k’afa kuma sai ku dawo kuna rarumowa da hannu.!
Kuma Ya’isha har yanzu fa ba kya lallab’a Najeeb ba kya yi masa yadda ya kamata…a yanzu duba da yadda Najeeb ya yi kud’i haka sosai dole fa sai da tarairaiya kwantar da kai lallami da lallashi dole sai kin bi ta koina kin mamaye kin rik’esa da kyau kin ajjiye kishi da girmankai a gefe dan wallahi one mistake idan kikayi tashi d’aya zai cika wandon sa da iska sai dai labarin wani ba shi ba. A da ma ya aka k’are y’an mata sun yi masa chaa ballantana yanzu.”

Cikin kuka kamar za ta shid’e Ya’ishan tace”Yasmeen shekaran jiya fa da kuka ce idan ya zo in je in basa hak’uri wallahi da na je har k’asa na durk’usa na basa hak’uri!
How much more good can I be ???”
Ya’isha ta yi mata tambayar tana kuka sosai.”

Tausayinta ne ya rufe Yasmeen
shiyasa ta ma kasa ci gaba da magana,ahankali ta sa hannu ta rungomota…ita kanta ta jijjiga da lamarin, babu abunda ya fi d’aga mata hankali kamar yarinyar.
Itama Ya’ishan haka dan dukda ta san tana da kyau amman fa ta san ba ta Isa ta tsaya tace za ta kara da Yarinyar da ta gani yanzu a fannin kyau ba.
Ba za ka kira Siyama doguwa chan ba sannan ba gajeriya ba ce,tanada haske sosai itama
sai dai yanayin hasken ta ba kalar na Jidda bane dan ita ba fara bace fat!ta fi kama da kalar half caste din da sukai had’i da turawa.
Kamar yadda fuskarta take round haka idanuwanta suke suma ba manya chan bane ba kuma ba k’anana ba y’an madaidaita sannan farare k’al waenda sukayi daidai da yanayin tsarin fuskarta,tana da cikar gashin gira kuma kwance suke.
Pointed nose gareta,sai bakin ta d’an k’arami lips d’in masu d’an tudu wanda hakan ya taimaka wajen k’arawa bakin nata asalin kyau. Bata da jiki sosai amman kamar su Jidda itama tanada structure mai kyau tubarkallah………

Su Ya’isha suna wucewa
Jidda ta fito daga motar Yassir ranta a b’ace.
Inda Aisha take ta k’arasa ta tsaya bayan ta karb’i d’ayan flask d’in da aka mik’o mata daga motar kayan,dama flask biyu ne kawai a cikin kayan sai
robar turare.
Dan haka Aisha ta d’au k’aramin flask da robar ita kuma Jidda ta d’auki babban mai d’an girma.

Ganin su Yassira ma duk sun fito ne yasa Aisha tace”inaga dangin angon ne dan ga wata mai kama da Yashjub d’in sosai,ku taho mu je a gaisa sai mu wuce ciki gaba d’aya a tare.
Dai dai nan Siyama wadda ta samu ta zille wa sir Najeeb da kyar ta k’araso wajen.
Tana shirin yin magana ta ji shi a bayanta ashe tare suke tafe ita bama ta sani sani ba,cikin nutsuwa ta ji yana cewa Aisha “ga sisters d’in Yash da aunty d’insu mu je ku gaisa dasu”
“Ok”Aisha tace daga haka ya wuce gaba suka bi sa a baya.
Kamar Siyama za ta tambayi Jidda mai ya b’ata mata rai har haka sai kuma kawai ta kyaleta tana mamakin abunda ya sake fusatata daga shigowarsu cikin gidan.

Yassira Baba larai sai Yadira da Yusra ne suka tsaya a bakin motar,suna jiran fitowar Yahanasu dan wallahi yau ba za su raga mata ba,rainin wayon nata ya yi yawa! matar da ta ce musu ba ta san kwatancen gidan ba shine suna zuwa suka tarar da ita a bakin gate tana jira a bud’e mata….

Yahanasu kuwa ba k’aramin dad’i ta ji ba da taga su Aisha,dama tunda su Yasira suka je suka tambayeta ta san su da naci shiyasa hankalin ta bai kwanta ba tace bari dai ta zo ta tabbatar da ba su zo d’in ba…..da farko da ta ga motocin su Yasirar a bayanta hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba ta shiga lissafin yadda za ta yi ta taka musu burki amman da suka shigo ta ga su Aisha sai ta ji wata nutsuwa da kwanciyar hankali sun rufar mata ga shi har da sir Najeeb! ta san duk bala’in su ko ma menene suka zo yi ba su isa su yi a gaban sir Najeeb ba,ga kuma Ummi a hanya itama wadda ta tsaya yin waya da ita ne ma shiyasa ba ta fito ba har yanzu…d’azu da Ummin taga sun fito ne ta fahimci gidan za su je shiyasa ta ce su jira ta ta d’auko mayafi itama tana so ta zo gidan amman tana fitowa sai wayam ta gani sun ta fi sun barta,shine a take ta kira Yahanasu ta yi mata kwatance,yanzu kam da suka yi wayar ma tana bayan layi….

Su Baba larai suna tsaye suna jiran fitowar Yahanasu suka ga su Aisha sun tunkarasu.
Baba larai ji ta yi kamar ta koma cikin motar dan ta tsani
yaran dama tun kafin ta gansu,sam ba ta k’aunar Manubiya da duk wani ahalinta….
Ba yadda ta iya haka ta tsaya dan ga Najeeb ya tunkarosu ta san shima gaida ita zai yi if not wallahi da tuni ta koma cikin motar.

Aisha ce ta fara gaida Baba Larai kafin su Siyama.
“Alhamdulillah”kawai tace daga haka ta d’auke kai Yasira kuma ta yi sauri ta kara waya a kunneta ta matsa gefe gudun kar ma su yi gigin kulata.
Still Aisha ce ta ce wa su Yadira “sannunku”
Kamar ba su ji ta ba haka suka yi mata.
Still Aishan ce ta kuma cewa Baba larai”ya taro?Allah ya sanya alkhairi”
Sai da ta juyo ta kalleta kafin tace“Ameen”daga haka ta zubawa Jidda da Siyama jajayen idanuwanta.
Ita Jidda har ga Allah tsoro matar ta bata,ga kuma Al’ameen da shege Yassir da suka kunno ta,ga shi taga ana amsa musu dakyar su Yusra kam ko kallo ma ba su ishesu ba.Shiyasa kawai sai ta juya ta ce “Siyama,ku taho mu wuce ciki”
Kamar dama jira Yusra take,sai cewa tayi”Atleast ai kya tsaya ki yi kyakkyawar gaisuwa da y’an uwan wanda kike k’ok’arin shigewa cikin gidan nasa”
Ta fad’i hakan tana murmushin
da mutum zai kasa gane rashn iya magana ne koko dai rainin hankali ne.
Cike da mamaki Najeeb yace “Yusra!Languagee!”
Ya d’an ja k’arshen yana mai d’age gira sannan yad’an motse baki.
Juya ido kawai ta yi ta kalli sama dan haushinsa dama gaba d’ayansu suke ji.
Ganin abunda ta yi ne yasa kawai ya d’auke kansa ya kalli Baba larai yace”Ina wuni
Baba ya hidima?
Murmushin yak’e ta yi
kafin tace”Alhamdulillah
Ya gajiyarku?”
“Mun gode Allah”yace
kafin ya juya ya kalli Yassira wadda ta gama wayar k’aryar ta zo tana gaida shi,da kulawa ya amsa mata daga haka ya juya ya nufi cikin gidan yana mamakin yadda Yadira da Yusra suka yi masa..wato ko kallo ma bai ishe su ba!tabbas
Yara sun girma kam….

Sir Najeeb yana shiga motar Ummi ta k’araso.
Already su Siyama ko gama gaisawa basu bari sir Najeeb ya yi da su Yassira ba suka matsa da niyyar shiga ciki….Yahanasu ta fito da fara a ta tarbe su kamar za ta goyasu,wanda hakan ba k’aramin sake tunzura su Baba larai ya yi ba…ita Baba larai
Babban tashin hankalinta ma shine
ta yaya za ta aiwatar da mission d’inta
da waennan jama’un a cikin gidan?..
Lissafin da takeyi kenan suka ga gate ya zuge motar Ummi ta danno kai.

Cikin b’acin rai Yassira tace
“Innalillahi!
Tabbas matar nan ta ci a bata sarauniyar y’an naci,
Mace ace ba zuciya kwata kwata,a taho a barki amman sai da kika zo?ko wa ma ya yi mata kwatance oho?!”
Chapter 31 · 0% Book details