← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 137

Sashe 112

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

D’an k’ura mata ido Yahanasu ta yi kafin tace”as I suspected..ba ki san na sani ba ko?to kuwa wannan karon Baba larai ta munafurce ki.”
Hawayen da suka zubo mata ne suka sanya ta yin shiru itama Mommyn hawaye ta ke yi sosai zuwa yanzu.
Da kyar Yahanasu ta tsayar da hawayenta ta goge fuskarta ta ce”A ranar da kuka dawo daga makarantar mu!a ranar da kuka je kuka had’a guiwa da principal d’inmu kuka saka ta shirgawa Mama k’arya kuka ce Daddy ne ya fad’a!to a ranar ne na ji komai.
….” Tun lokacin da Mama ta fara zuwa wajena a makaranta na so in fad’a muku ke da Daddy amma sai ta ce mini ba ta so ku sani wanda a da laifinta na gani da ta nemi in b’oye muku amma da na ji abunda kuka yi kuka saka aka ce mata Daddyn yace! ne ya sanya na fahimci dalilinta na cewa in b’oye muku.
Tana zuwa wajena a kai a kai har ta fara yi mini maganar tana so za ta d’auke ni in zauna a wajenta zan bita?!’ni kuma na ce mata ‘eh’. A wannan lokacin shekaruna ba su haura takwas a duniya ba amma sai na yi lissafin cewa idan na b’oye muku wannan al’amari to
kamar na munafurceku ne,dan haka na yanke shawarar gaya muku ke da Daddy saboda daga ke har shi kuna nuna min tsananin soyayya shiysa na ga rashin dacewar b’oye muku zancen.
Ina zuwa dai dai k’ofar d’akin ki na ji muyarki cikin fushi kina cewa”Larai!!wannan yana d’aya daga cikin dalilan da suka sanya na ce miki kar mu fitar da Khadijah har ma da mallan lawal d’in amma kika k’i yarda kika ce ba za ki iya bari su mutu ba!
Yanzu ai ga irinta nan inda ace Daddy ne ya fara jin labarin zuwan da Khadija take yi wajen Yahanasu ya san cewa ta na raye har yanzu ai da mun shiga uku!!!kuma dan mun ce wa principal ta ce mata ga abunda Daddyn yace ke kina tunanin za ta hak’ura ta daina bibiyar y’arta ne?dan kawai ance za a tona mata asiri?ina ce farrak’u kika ce kin yi mata da duk ahalin gidan nan sannan kin kafeta a duk inda take?to ya akayi ta fito?”

Kai na ne ya d’aure dan ban gama fahimtar me kike nufi ba sai da na ji batun Baba larai tukunna na fahimta,ta inda take cewa”Kar ki damu akasi aka samu amma zan gyara sannan saboda Allah Mommu yanzu ace duk Irin taimakon da lawal ya yi mana sai mu barshi ya mutu??ba dan shi ba ai da tuni Khadija har yanzu tana tare da Imam…”

A lokacin I was 8 amma tashi d’aya na fahimci abunda kuka yi na fahimci komai saboda a ko da yaushe cewa ake yi gobara ne ya kashe mahaifiyata kuma na tuna yadda ko shekara ba a yi ba Daddy yace mana kar wanda ya sake kiran ko da sunanta kuma akwai ranar da na ji yana kuka yana cewa Hajiya mama da ya sani ya tsananta bincike da ya sani bai kunna musu wuta ba.
Shiyasa na fahimci komai na fahimci tabbas duk shirin ku ne ke da Baba larai.
So na yi in tuna muku asiri amma sai na ji kina cewa”shikenan na yarda da ke amma gaskiya ya kamata ki yi Abu mai k’arfi wannan karon a kansu ki sake kafe ta a duk inda take inda Hali ko makwabta kar ta samu jin dad’in shiga saboda wallahi na tsorata matuk’a sannan inaga larai gara kawai in fito in gayawa Yahanasu gaskiya ta san cewa ni ce na haifeta na san za ta fahimceni!kalli fa yadda Khadija take zuwa wajenta a b’oye a matsayin Mahaifiyarta itama kuma ta b’oye mana!
A gaskiya abun ya fara damuna kuma Ina tsoron kar ta girma abun nan da na yi kuma na yi shiru ya yi affecting relationship d’ina da ita”

Ban yarda da abunda kunnuwana suka jiye mini ba sai da na ji Baba larai ta katse ki itama tana cewa”Khadija ki rufa mana asiri kar ki ja mana,kar ki je garin soyayya da k’ulaficin y’ar ki ki je ki tarwatsamu!!Wallahi ko da wasa idan aka san Yahanasu ce y’arki ba Yashjub ba to komai ya lalace mana kenan..kar ki yi tunanin idan kika gaya mata maganar za ta b’uya ni na san dole za ta fito dan haka ki ja bakinki ki yi shiru mu samu mu cimma burinmu tukunna sai mu san abunyi!as far as I know Yahanasu tana gabanki za ki kula da abarki sannan babu wanda zai cutar miki da ita dan haka idan har zan baki shawara ki d’auka to ki ja bakinki ki yi shiru.
And again!yadda kike yi a gaban Daddy ki d’an rage har ma su Yasirar suma ki rage..jiya bakiga shock da mamakin da Daddy ya shiga ba da akace masa kin daki Yasira saboda Yahanasu kuma itama Yasira suna cin abinci ina jinta tana cewa Mommy ta fi son Yaha a kansu!!dan haka ki ja bakinki ki
Iya takunki tun kafin ki tonawa kanki asiri.”
…….

Hawayen da suke zubo mata sharkaff ta sa hannu ta goge kafin ta ci gaba da cewa”Ina jinta tana ce miki kar ki damu ko nan da shekara nawa ne indai kika gaya mini ke ce mahaifiyata ta asali ba zan guje ki ba kuma ba zan ji haushin ki ba,za ta yi mini katanga da mutane saboda gudun kar in yi k’awaye a gaba in fahimci duniya su zuga ni idanuna su waye in fahimci kin zalinci ni.
Sannan za ta rufe mini Baki saboda kar in gaya wa kowa na ga Mama sannan za ta rabani da Mama ba zan nemeta ba ta inda za ta yi mini abunda ba iyaka maman kad’ai ba ban Isa in sake shiga jikin wani har mu yi sirri da su in kasa fad’a miki ba,nan k’arshen kuma tace”za ta yi abunda ke kad’ai za ta bari a jikina bayan ke babu wanda ya Isa ya shiga jikina ya san cikina komai kawai kika ce zan bi ki in karb’a hannu bibbiyu ba zan yi jayayya ba.!
Saboda har abada ba za ki gaya wa Daddy gaskiyar tsakanina da ke ba gudun matsala,so idan kika yi mini haka za ki gaya min ke mahaifiyata ce zan amince in karb’eki
Hannu biyu kuma ba zan gaya wa kowa ba ba zan kuma ji haushi ba!.

Da farko ce mata kika yi a’a amma da ta ci gaba da tsara ki Mommy saboda tsabar son kai da son zuciya tashi d’aya kika amince a yi mini duk wa’ennan abubuwan duk dan kar in tona miki asiri kuma kar in k’i amincewa da ke as mahaifiyata a lokacin da kika gama tsara plan d’inki kika shirya karb’ata kika shirya gaya mini ni y’arki ce.”
Cikin kukan Yahansu ta ci gaba da cewa”sam ba ki yi tunanin hakan da kika yi mini zai iya shiga tsakani na da aure ba!.”ta k’arashe maganar tata cikin tsananin fashewa da kuka kafin ta ci gaba da cewa
“Ina tsaye a wajen Ina kuka har Baba larai ta fito daga d’akin naki ta ganni, na san ta san idan kika ganni a haka kika fahimci na ji komai to za ki karaya ne kuma ta san akwai matsala,shiyasa a wannan lokacin ta toshe mini Baki ta ja ni d’akin ta ta zaunar da ni.
Ita kanta na san a wannan lokacin ta sha mamaki na dan bata yi tunanin na yi wayo har haka ba saboda duk yadda ta so yi mini wayo ni kuma na k’i Bata k’ofa kuma ta fahimci na san komai na kuma gane komai inaga shiyasa ta je ta yi tsafe tsafenta ba tare da ta sanar da ke cewa na ji komai ba.
Na san da ke da ita duk kun d’auka asirinku ne ya yi tasiri a kaina na daina shiga jama’a kamar yadda kuka tsara amma asalin gaskiya Mommy tsanar ki bak’in cikinki da haushinki ne suka maidani na zama abunda na zama har kawo yanzu.
Chapter 112 · 0% Book details