← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 137

Sashe 49

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da Ya Musbah ya bud’ewa Muhsin wanda suke zaune a gaban tare da shi ya fita
tukunna ya juya ya kalli ya Nafi’u ba tare da ya rufo murfin motar ba yace
‘’Jiya ma ka tambayeni kuma amsa d’aya zan baka,’ba abunda yake damuna’saboda dagaske babu abunda yake damuna d’in‘’.

Cikin tarar numfashin sa ya Nafi’u yace
‘’Ko kuma dai ba za ka gaya min ba saboda ka san ba zan tab’a goya maka baya ba ko?,
Haba Musbahu na fa san a kan Baraka ka shiga wannan damuwar.”kafin ya gyara zama ya fuskance sa tukunna ya d’aura da cewa”har wanne dad’i ku ka yi da Baraka da har zai sanya kake missing d’inta har haka?.
Baraka fa Musbahu!”
Ya k’arashe maganar tasa cikin rashin jin dad’i.
Shiruuu Ya Musbah ya yi kafin yace”ba fa a kan Baraka na shiga damuwa ba!shin ba ka ga halin da muka tadda Manubiya sannan muka baro ta a ciki ba ne?”

Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace“Jiya waye ya je wajen Baraka bayan sallar Magrib???”

Da sauri Ya Musbah ya d’ago ya kalle sa sai kuma cikin fushi yace “Bibiyata kake yi?”.

“Babu zancen bibiya a nan!
amsa kawai nakeso ka bani”.

Kamar Ya Musbah ba zai ce komai ba sai kuma ya kallesa yace
‘’Wajen mai sunan baba na je, ko ban Isa na je naga d’ana ba??”

Cikin katsesa sannan cikin tsananin fushi Ya Nafi’u yace
‘’ba za ka tsaya ka gaya min gaskiya ba? Yau nine na zama wanda za ka yiwa wannan k’umbiya k’umbiyar???
Shikenan ka je ka yi ta yi,dama shawara ce zan baka amma tunda na ga bakaso fine!
In dai Baraka ce bismillah,ga ka ga ita amma inaso ka san cewa ba za ta tab’a chanza zani ba.”
Ya fad’i hakan yana mai k’ok’arin zare makullin motar ya fita.
A hankali Ya Musbah ya ce
‘’d’an tsaya Nafi’u.”
Shiruu Ya Naif’un ya yi kamar ba zai kula sa ba sai kuma ya juya yana kallon sa tare da basa dukkan nin attenbtion d’insa.
Ahankali Ya Musbah ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“Ina son ta,har yanzu’’

Wani irin kululun takaicin Baraka da tsantsar tausayin Ya Musbah ne suka lullub’e Ya Nafi’u a lokaci guda.Da kyar ya had’iye abunda ya ji ya tokare masa mak’oshi yana shirin yin magana ya ji Ya Musbah ya ci gaba da cewa
“Har gobe inason Baraka,har abada!.Kai Abokina ne kana fahimta ta akan komai dan Allah ka fahimceni ka bani goyon baya akan wannan ma.
Itama ta shiryu ta ce min za ta gyara halayyarta sannan tana so ta zo ta bawa su Inna hak’uri kuma tace za ta rik’e Muhsin.
Har yanzu ba ta riga ta fita a idda ba shiyasa da ni da ita muke so a had’u a gyara abun nan kafin ta fita idda kaga ba sai an yi sabon d’aurin aure ba.
Wannan shine abunda yaketa damu na, na rasa wa zan gayawa kuma ni a ganina Baraka za ta zauna lafiya da ni da kowa ma tunda yanzu Ina aiki kuma Inada rufin asiri.”

Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace
‘’Musbahu duk matar da ba ta zauna ta ci talaucinka ba to bata yi deserving arzik’inka da kai kanka ba.
Musbahu Baraka bata da kirki ta raina ka ta raina iyayenka…..”
Shiruuu ya Nafi’un ya d’anyi ya tsagaita da magana ya dafe kansa saboda ciwon da ya ji ya fara yi masa a sakamokon b’acin rai da takaicin Ya Musbah da Baraka.
Ya d’an jima bai ce komai ba kafin ya cika kan nasa tukunna ya kalli Ya Musbah ya ci gaba da cewa”shikenan, tunda ka nace…sai ka je ka samu Inna ka ce mata kanaso za ka dawo da Baraka.”

Da d’an zafi Ya Musbah yace
‘’Ya za ka ce in je in samu Innaa?bayan abunda Baraka ta yi mata taya kake expecting in je ince mata zan dawo da ita?ai wannan aikin ka ne
Kai ka san ta inda za ka b’ullowa al’amarin Kai ne za ka taimaka mini shiyasa na ke gaya maka,saboda ka taimakeni‘’

Shiruu kawai Ya Nafi’u ya yi yana nazartar sa…bayaso ya zargi Baraka amma kuma kana ganin Ya Musbah da zantukan sa tashi d’aya zaka fahimci tabbas aikin asiri ne ba haka ta bar sa ba.
Ya taso masa da maganar Inna ne saboda yanaso ya tuno masa da abunda Baraka ta yi wa mahaifiyarsa ya ji zafin abun ya daina tunanin dawo da ita
amman it’s like kamar ma an yi deleting takaicin da wannan ranar ta k’unsa dan kwata kwata bai hango haushi ko takaicin Baraka a idanunsa ba
bayaga zazzafar soyayyarta da tausayinta dayake hangowa a tattare da shi.

“Ba laifinta bane itama,sharrin shaid’an ne amma ta yi mini alk’awarin ba za ta sake ba har hak’uri tace za ta zo ta bayar,ka yarda da ni Nafi’u Baraka ta shiryu tun ba yau ba”
Ya sake jin muryar Ya Musbah.

Kallonsa ya yi da kyau kafin yace”Tun ba yau ba?kenan tun ba yau ba kuke waya kake zuwa???”
Bai basa damar cewa komai ba yace”Am Musbahu…
ba zan baka goyon baya ba sannan ba zan hanaka ba.As far as I can remember na san kanada hankali da sanin abun da ya kamata dan haka ka yi
duk abunda ka ga dama.”
Yana gama fad’in haka ya bud’e k’ofar ya fice ya wuce cikin gida ya bar Ya Musbah a nan zaune shi kad’ai.

Ya jima sosai a cikin motar tukunna ya zare makullin ya rufe motar shima ya nufi cikin gidan.
A zaune ya same shi suna raha wasa da dariya shi da su Inna,
yana shigowa Ya Nafi’u ya mik’e ya yi wa su Inna sallama suka wuce shi da iyalinsa…ko ba a fad’a ba tashi d’aya zaka fahimci Ya Nafi’u haushin Ya Musbah yakeji shiyasa dukkan su suka shiga al’ajabi dan abu ne wanda bai tab’a faruwa ba.
Suna fita Baba ya kalli Ya Musbah yace
“Tashi ka bi sa ku sasanta.”
Zai yi magana yace
“Jeka”
Saboda dama shi tunda aka ce masa suna waje suna magana ya san akwai wani abun,yanzu kuma da ya ga hakan sai ya fahimci tabbas sab’ani suka samu…maybe ma shiyasa kwana biyu yake ta ganin Musbahun a cikin damuwa…

Ba su jima da fita ba Baba ma ya mik’e ya fita bayan an tabbatar masa da cewa su Manubiya suna lafiya,daganan Muhsin yace “bara ya je d’akin su”Jidda kuma ta tafi raka Siyama…
Suna fita Siyama tace “ni kam ina ma ace Ammi za ta
hak’ura wallahi…kinga d’azu fa dakyar ya iya jan motarsa ya shiga gida!,ko ba ki lura da shi a time d’in da muke shirin shigowa gida ba lokacin shima yana k’okarin shiga gida.
Kinga yadda ya rame kuwa a cikin kwana hud’u gask…..”

Kukan da Jidda ta fashe mata da shi ne yasanya Siyaman yin shiru,kafin da sauri tace “Innalillahi yi hak’uri Jidda mai ya yi zafi??”

Cikin kuka tace
‘’Siyama dan Allah ki daina min maganar Al‘Ameen dan Allah!kin san Ammin sa ba za ta tab’a amincewa ba ko ta amince ma su Ya Musbah suma yadda suka zuciya na san ba za su bada goyon baya ba.
Ki daina yi min zancen sa ki taimaka min in samu in fitar da shi a raina dan Allah.”

Shiruu Siyama ta yi tana mai jin tausayinta yana sake rufeta…
rana d’aya tak ta d’an samu moment da Najeeb ta kuma fahimci k’udirin sa a kanta amman ba k’aramin Namijin k’ok’ari take yi wajen dannawa calls d’in sa reject ba.
Shiyasa ta ke ganin k’ok’arin Jidda na hak’ura da Al’ameen bayan shekaru wajen hud’u da suka yi a tare kawai yanzu tashi d’aya an raba su,tabbas abun da ciwo.

Rarrashin ta ta shiga yi tare da bata baki dakyar Jiddan ta d’an dawo dai dai dan a kwana biyun nan ita kad’ai tasan halin da take ciki..kwanakin baya ta ji haushi ta ji takaici amman kuma tun da ta gansa gaba d’aya sai ta ji ta yafe masa.
Kuma tabbas a yadda ta ga ya yi ta san yana da uzuri sannan uzurin na sa mai k’arfi ne…she just wants to hear him out,forgive forget and be with him….
Tana wannan tunanin suka fara takawa towards wajen su Siyama kowa ta yi shiru da abunda yake damunta a haka suka k’arasa Siyama ta zaro makulli daga jakarta ta bud’e
Parlourn dan maman nata
bata nan ta tafi gidan suna.

Suna shiga ko gama zama ba su yi ba
Siyama tace
“Kina ganin mu kira Manu mu yi magana ko mu je gidanta bayan kwana biyu?”

Shiruu Jidda ta yi kafin tace
“Sai dai zuwa anjima mu kirata dan kinsan tafiya za su yi tace jibi ne da asuba.
Amman zakice na gaya miki dangin mijin nan nata ne suka sakata kuka ba ruwan Ya Yash
kinga yadda jikin sa yayi sanyi
ai ba laifin sa bane.”

A hankali Siyama ta nemi guri ta zauna sannan tace
“I hope so dan ba na so su fara samun matsala da shi.Allah dai ya sa ta gaya mana.”

Cike da assurance Jidda tace “za ta fad’a inshaaAllah..idan na bayar da shawara ne sai mu bata idan kuma munga ya fi k’arfin mu sai mu sanar da su Innaa dan ba zai yiu mu zuba ido ba…kwata kwata fa yau ne ta yi 4 days a gidan.

Ahankali Siyama tace
“InshaaAllah ma k’aramin abu ne Allah ya sa ba wani babban issue bane ba.”
Chapter 49 · 0% Book details