← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 137

Sashe 103

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai Daddy ya ji haushi ya fusata…tayaya Yash zai ce sai abunda ta yanke tukunna shi za su yi??a tak’aice dai Yashjub ba shi da choice sai na Manu su kuma suna zaune suna jira har sai ya je ya tambayota ta fad’a tukunna a zo ya gaya musu su yi.!

Ya san dole abun zai tab’ata tunda abune wanda ya shafi Mijinta da wata mace amma power d’in da Yashjub ya bawa Manubiya is too much…this is not the right time da ya kamata ya ji haushin Manubiya a kan wannan maganar dan tunda cikin jikinta ya zube shi tausayinta ma yake ji over amma tashi d’aya a yanzu sai ya ji takaicinta ya rufe sa….ba zai tsaya a mayar masa da d’a boyi boyi ba.
Wato ko abu zai kashe shi kmr yadda ya fad’a in ta na so
zai yi kenan! matar da ya kamata ace she’s even greatful da Yash ya aureta aka kawota cikin family d’in su shine amma ta kafa ta tsare ta ke juya musu d’a suma take so ta juya su.

Lissafin da Daddy yakeyi haka nan shima Abhi yake irinshi
Exactly.
Dama shi Abhi tun farko da su ka je kai kud’i sai da ya saka hakan a ranshi amma daga baya sai ya janye yanzu kuwa power d’in Manu ya yi yawa gaskiya dole a ja mata layi.
Dan wannan Yarinyar idan ba su yi da gaske ba har Hajiya mama sai ta juya.

Numfashi Daddy ya fesar kafin ya kalli Abhi yace”yanzu me ye abunyi?ni dai ba zan jira sai Yarinya ta yanke decision tukunna mu maza za mu yi ba.”

Jinjina kai Abhi ya yi yana d’an lissafi kafin yace”Daddy a yiwa kowa adalci sannan a duba Yaron da bai ma riga ya zo duniya ba…kamar yadda ka fad’a duba da yanayin hanyar da akabi aka sameshi ya kamata ace mun tsaya tsayin
daka mun yi sacrifing komai wajen ganin mun inganta rayuwa da tarbiyyar sa…”

Da sauri Yassir yace”Abhi ni k’anin Yashjub ne inason Kausar me yasa ba za ku aura mini ita ba ni???
Wallahi idan kuka had’a Kausar da Yashjub to
kun had’a fitina ne saboda ba sa so…..”

Cikin fushi Daddy ya katse sa yace”One more word from you Yassir Allah sai ka fita a parlourn nan!!!
Mahaukacin banza kawai mara zuciya…
Anya Yassir ka san ciwon kan ka kuwa??”

“Hmmm”kawai Junior yace

Wanda hakan ya sa duk sai da suka d’an kalleshi.

Atake jikin Yasssir ya d’anyi sanyi dan sai yanzu ya fara tunanin kar fa ya kwafsa..to amma shi yanzu ya zaiyi???….ga duka ga hana kuka!inaa!!!ba zai bari auren nan ya d’auru ba.

Sai da su Abhi suka sake yin d’an k’us k’us d’insu tukunna Daddyn ya d’auki waya ya kira Ummi daganan ya kira manyan drivers d’in gidan da aka dad’e da su yace “su zo!”

…Manubiya abar tausayice duba da zargin zubar matar da ciki da suke yi sannan Yarinyar ba ta matsala ga kuma tarbiyya da hankali above all d’an su yana sonta he’s happy with her!amma kuma Tabbas ya kamata a yi limiting d’inta dan ba zai you su je garin tausayin su kunnawa wani haske su kuma su k’ona kansu ba…soyayyar Yashjub a gareta ta yi yawa ba su damu idan ya so ta da yawa ba kawai su problem d’insu importance da power da ya Bata wadda take k’ok’arin danne su da k’imar su a idanun Yashjub ne matsalarsu sannan ba a yiwa mace haka!idan su ka zuba ido a gaba za su matsala.
Tun da akayi auren yake haka inda gigin amarci ne da tuni ya daina amma abun nasa k’ara gaba yake yi.son da Yashjub ya ke yi mata ya yi yawa…ba sa jin haushinta infact su tausayi ma take basu ammafa fa hakan ba shi zai sanya su zuba ido Yashjub ya zama boyi boyi ba.
Sun san idan ya riga ya auri Kausar ya saba da mata biyu ko ya rabu da ita bayan ta haihu kamar yadda aka shirya ba lalle ya iya zama da mace d’aya ba…Idan aka barwa Manubiya Yash ita kad’ai akwai gagarumar matsala….
Dan haka suka ga dacewar su jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya……

Yana gama waya da su Ummi ya sauk’e ajiyar zuciya ya yi shiruuu yana mai jin kamar ya d’aura Hannu a ka! ya kurma uban ihu…wai yau shine da kansa zai aurawa Kausar Yashjub!
Tabbas shiyasa ba a son mutum ya tsananta tsana!saboda ba ka san inda rana za ta fad’i ba.
….
Sai da aka kusan yin fad’a da Daddy da Ummi da ta ji wai aure za a d’aurawa Kausar da Yashjub…so ta yi ta fita ta kira shi ta sanar da shi amma Daddyn ya ce ta zauna Abhi kuma ya shiga bata Baki,ga drivers d’in gidan a zaune sun yi jigum suma kawunansu a k’asa,shiyasa Abhi ya dage ya lallab’ata ba dan ta so ba ta hak’ura ta zaune ta na mai jin kamar zuciyarta za ta fito babu yadda ta iya haka aka d’aura auren Kausar da Yashjub akan sadaki naira dubu d’ari Abhi ya yiwa Yashjub wakili Daddy kuma ya yiwa Kausar.

Ba abunda ya fi d’aurewa Junior Kai kamar rikicewar da Yassir ya yi,Dan ba da shi ma aka d’aura auren ba korarsa su Abhi suka yi ganin yana shirin yi musu hauka da kyar kuwa ya fita yana huci ya nufi side d’in Kausar amma sama ko k’asa ba ta nan kuma wayoyinta duk gasunan a zube a kan gado.
Ita kuwa Kausar b’uya ta yi a box room d’in saman saboda shi tana kallonshi ya sauk’o a rikice ya nufi side d’in nata sai da ya fito ya sauk’a k’asa tukunna ta fito ta shige dan ba ta shirya fuskantar sa ba Bata gama had’a wayon da za ta yi masa ba wannan karon.
Dukda tana zullumin son jin dalilin yanayin da ta gansa a ciki amma za ta bari ta ji zuwa gobe.

A b’angaren Mommy kuwa ta fito kenan za ta tafi wajen Baba larai ta ji ya ake ciki ta ga Yassir ya sauk’o kamar ma yana kuka shiyasa ta kasa hak’ura ta haye saman ai
kuwa tun kafin ta k’arasa jikin k’ofar sosai ta fahimci d’aurin aurene ake yi….

Hamdala da sujjada ta yi sai da ta ji an ida d’aurin auren tukunna ta juya ta nufi side d’in Kausar har tana tuntub’e.

A b’angaren su Daddy kuwa ba a tab’a d’aurin auren da babu wanda yake farinciki ba sai a yau! Kaff wajen babu wanda yake
farin ciki da d’aurin auren hatta drivers d’in da aka kira su ka yi
shaida ba su yi murna da wannan al’amarin ba dan su kansu sun san Kausar ba ta dace da Yashjub ba gashi bai dad’e da yin aure ba.
Junior ji yake kamar yayi kuka dan takaici saboda gani yakeyi kmr hakan duk laifin sa ne
amman kuma shima bashida yadda zai yi,ba zai je garin taimakon Yashjub ya lalata nashi relationship d’in da bai ma samu ya fara ba along with his image and reputation.
Su Daddy suna gama d’aurawa kuma sai suka fara da na sani..kamar irin ba a cikin haiyyacinsu suka d’aura d’innan ba.
Babu tsoron wadda ya fi rufe su kamar Hajiya mama
dan haka suka d’aura alhakin gaya mata a kan Ummi…a ganinsu tunda tana ji da ita
tabbas za ta san yadda za ta yi mata bayani ta fahimta ta kuma taushe ta ta hak’ura.
Tana gama jin bayanin su tace”to”kawai daga haka ta juya ta fice ranta a mugun b’ace.

A b’angaren Yassir ma zuwa yanzu ya rikice dan yana k’asa drivers d’in suka sauk’o ya tambayesu suka ce “eh an d’aura”
bai ma san next step d’in d’auka ba shiyasa kawai ya zauna yayi shiru dan kwakwalwarshi ta d’auke ta tsaya daga aiki.

Mommy tana shiga d’akin Kausar ta sameta a tsaye dan itama shigowar tata kenan.

Murmushi Mommyn tayi kafin ta k’arasa inda Kausar d’in take ba ta damu ta yadda ta turo Baki ba dan ta san yanzunnan za su shirya…
Cikin tsananin farin ciki tace
“Ki yi mini alk’awari
goron albishir d’innan da zan baki yanzu shine za ki daina fushi da mu!!”

Gaban ta ne ya yanke ya fad’i a ranta ta shiga adduar “Allah ya sa hasashenta dai dai ne Allah ya sa tarkonta ya kama kurciya”
A fili kuma sai ta kalli Mommyn tace”Inajinki”

Cupping fuskarta
Mommy tayi kafin tace
“Ki yi mini alk’awari first!”.

Juya ido Kausar ta yi
kafin tace “okay fine!yawan farin cikina yawan daina fushi da ku”
Dariya Mommy ta yi sannan tace mata”Y’a ta ta girma ta zama matar aure
Matar Yashjub imam kura
yanzunnan Ubangiji ya yi ikonsa.”
Tun Mommy tana murmushi mai had’e da dariya har ta zo ta daina dan Kausar ta k’ame k’am!!!
Ta ma kasa yin ko motsi.

Sai da Mommyn ta d’an jinjigata tukunna hawayen farin ciki suka zubo mata,a hankali ta kama Hannunuwan
Mommy biyu da suke rik’e da kumatunta idanunta na zubar da hawaye tace
“Mommy da gaske kike
Dan Allah ki yi mini wasa da komai banda wannan”.

“Wallahi da gaske nake”
Mommy ta fada mata tana murmushi tana goge mata hawayenta.

Fad’awa tayi jikin Mommy kawai ta fashe da kuka…dai dai nan su Yassira suka shigo ita da su Yusra cikin farin ciki sukace
“Mommy da gaske ne abunda muka ji Ummi tana waya yanzu tana fad’a???”
Jinnjina musu Kai ta yi still tana rik’e da Kausar dan ta k’i ta cika ta har yanzu…
Aikuwa a take gaba d’ayansu suka taho suka had’asu suka rungume…
Farin ciki a ranar dai ba mahaluk’in da ya kai su Mommy.
A ranar Kausar ta nemi yafiyarsu dukkansu na ganin kamr sun daina sonta da ta yi dan yau kam ta tabbatar da suna k’aunarta duba da yadda suke taya ta murna.Kowa in ga kalla baki a washe Yasmeen ce kawai babu a wajen.
A ranar har Baba larai suka yi alk’awarin had’e kansu guri d’aya su taimaki Kausar su tsaya mata ta yak’i Yashjub
su ga bayan Manubiya.
Chapter 103 · 0% Book details