← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 137

Sashe 27

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su Siyama suna gamawa,suka yi sauri suka shiga wanka dan Aisha su take jira suje su kwashi kaya su kai gidan amrya,suna fitowa suka shiga shiri da hanzari…ba komai a fuskokinsu sai Vaseline ankon
su da suka yi na atamfa shi
suka saka dan har Aisha
Itama shi ta saka da mama,
A shape aka yi wa Siyama Jidda kuma riga da skirt
Atamfar kalar light blue ne da white shiyasa ta karb’i jikinsu ta sake fito da ainihin kyawun hasken fatar su…Tsayin su kusan d’aya ne sai dai Jidda ta d’an fi Siyama jiki kad’an.
White vail Siyama ta rufa ta yi d’aurin ta mai kyau,Yayinda Jidda ta rufa blue vail itanma sosai d’aurin ta ya yi kyau.
Suna fitowa daga side d’in su Siyama suka had’u da ya Musbah…sak’on Yashjub ya gaya musu saboda d’akin su innar ya cika taff shiyasa bai samu ya iya shiga ba,yana gama gaya musu sak’on ya juya ya koma d’akin shi ko waje wajen Nafi’un ma bai koma ba dan kansa wani kalar azababban ciwo yake masa..ba daban bai yarda da tsubb’ace taubb’ace ba to da babu abunda zai sa ya k’i yarda da cewa ‘Baraka tsafi ta yi masa!’idan fa ya rufe ido har ganinta yakeyi sannan ji yake kamar ya je ya d’auko ta kawai ya dawo da ita,bai tab’a missing mutum kamar yadda yake missing Baraka ba
sannan a iyaka kwana biyu kawai ya ji soyayyarta da k’aunarta sun dawo mishi sun zauna daram sun mamaye koina sab’anin kwanankin baya da ya tsani ya ji ko da sunanta ne. Dama tun sati biyu bayan da ya sake ta ya fara jin hakan amman abun bai yi worst kamar yanzu ba.
A shagub’e ya d’an gwada tuntub’ar Nafi’u ba wai direct ba,amsar da Nafi’un ya basa yasanya ya fahimci tabbas indai har ya dawo da Baraka to Abotarsu za ta iya tarwatsewa,shi kuwa a yadda yake jin Nafi’u yanzu ya ma fi k’arfin Aboki a wajen sa sai dai d’an uwa shiyasa sam ba ya son abunda zai shiga tsakanin su…..to Nafi’u ma ya nuna baya so ballantana kuma inna
wadda akayiwa abun!
Shiyasa gaba d’aya yake a burkice bai ma san ta ina zai fara kallon family d’inshi yace musu ‘zai dawo da Baraka’ba
shi kuma tabbas a yanda yake jin Baraka a halin yanzu in dai har bai dawo da ita ba tou akwai matsala…….

Jidda ce ta wuce d’akin dan sanar da su inna yayin da Siyama ta nufi parlournsu ta shiga tattarewa bayan ta cewa bak’in ciki “dan Allah angwaye za su shigo”,sun fita
Tana cikin tattarewa Jidda ta kirata tace “su inna da anty umma sunce a bari su Yashjub d’in su gaida su a d’akin kawai saboda akwai matar mai unguwa kuma gurguwa ce so idan akace sai ta sake jan kujerarta zuwa parlourn su Siyaman wani sabon aiki ne,”
“But gata nan zuwa ita da Manu su inna sunce ta je parlourn su zauna su yi hotunan a ciki”

Mata wajen biyar ne a d’akin ga kuma matan uncle da su anty umma suka cewa su Jidda su je su kira shiyasa anty umma da mama suka nemi waje a bayan gidan suka zauna dama abunda maman take so kenan shiyasa ta San yadda ta yi ta ja anty umma dan har ga Allah bata so ta had’u da angon dan bata san wanne hali za ta shiga ba idan zarginta ya tabbata ko kuma akasin hakan tsabar yadda ta rud’e ita ba ma ta san me zata ce tana so ba a halin yanzu…ya tabbata ko kuma kar ya tabbata.

Sai da aka d’an tartare d’akin aka saka turaren wuta tukunna
akacewa su Jidda suje su shigo dasu,matan su baba habu kuwa ko da aka gaya musu ma basu tashi zuwan ba dan yaddda suke ganin ran mazajen nasu a mugun b’ace kuma sun san akan auren ne aka b’ata musu rai yasanya bama su gwada tambayr su zuwa su gaisa da angwayen ba gudun b’acin rai……

Yashjub yana tsaye suna waya da Yassira ya hango Yassir yana sallama da Abokansa,suna wucewa ya ga shima ya bud’e mota yana shirin shiga ya wuce dan haka ya yi saurin cewa Yasira”ina zuwa” daga haka ya kashe wayar ya d’an d’aga murya ya kira sunan Yassir.

Sai da yayi tsaki tukunna ya rufe motar ya juya ya na kallonshi,yaffito sa Yashjub d’in ya yi da hannu daga haka ya d’auke kai ya ci gaba da magana da Najeeb.

Kamar zai kama da wuta!haka
Yassir yakeji tsabar takaici..sai da ya taushi zuciyarsa da kyar tukunna ya fara k’ok’arin zuwa inda Yashjub d’in yake dan sai da suka yi shi da Daddy da Abhi suma kafin su wuce akan yadda yake ta faman ciccin magani yake kuma k’in
shiga ayi abu dashi sune har da zaginshi Abhi yana ce mishi mai bak’in hali tukunna suka wuce,shiyasa tun d’azun yake a wuya yanzu kuma ga Yash shima yana shirin k’arasa kaishi bango…sam sun kasa la’akari da yadda ya danne kanshi ya shigo cikin wannan mugun layin dukdan saboda su amma still babu godiya babu jinjinawa kalli abubuwan da akeyi masa…..da kyar ya dan danne kansa dan wani mugun takaici yake ji tukunna cikin takunshi fuskar nan tamau ya fara takawa izuwa inda suke a ranshi yana aiyyana”tabbas ya san sai ya sha maganin allergy dan he’s allergic to warin kwata kuma kwatocin layin kusan duk a bud’e suke,gaba d’aya koina wari yake yi…he definitely has to see a doctor”
Yana cikin tunanin asibitin da ya kamata yaje ya k’arasa inda suke tsaye ya tsaya kawai ba tare da yace komai ba.

Kallonsa Yashjub d’in yayi
kafin da mamaki yace “ya na ga kana shirin tafiya?ba za ka
shigo mu gaishe da su ba?.
Ka tsaya idan muka gaida su muma duk wucewa za mu yi,sai mu tafi tare.”

Yassir ji yayi kamar ya d’aura hannu aka ya kurma uban ihu tsabar takaici….yanzu dan rainin hankali wannan mugun gidan yake so ya shigar da shi tsabar son wulakanci,iyaka layin da ya shigo da su bai ishe sa ba sai ya danna sa a cikin gidan kenan!a ranshi yace”Tabbas na ga alama sai na yiwa mutumin nan da gaske tukunna zai d’aga min k’afa”
A fili kuma cikin tsananin tsageranci da wulak’anci ya kalli idon Yash d’in tukunna yace”ka san dai Allah d’aya ne ko!to wallahi idan na shiga gidan nan sai anyi deworming d’ina!yanzu haka I’ve fallen sick,na san ka san Ina reacting
to dirt and disgusting items amma sai k’ok’arin forcing d’ina kake yi,haba mana!…”

Sakar baki kawai sir Najeeb yayi yana kallonshi shi
Yashjub kuwa ya zo iya wuya jira kawai yake ya kai aya ya fara cin ubanshi tunda ya lura
bashida hankali
Manubiya da family d’in nata ne disgusting items ko
me?tabbas yau kam Yassir ya kuma kaishi bango zai kuma sha mamaki…..

Yassir ya lura da yadda Yashjub yake kallonsa amma sam bai damu ba”besides gwara ma ya kaishi
bango ya k’ular da shi ta yadda zai yi misbehaving a k’ofar gidan surukan sa!
Oho!shikam dad’i ma zai ji”
Ya aiyyana hakan a ransa,sai kuma cikin son sake fusata shi a fili Yassir d’in ya ci gaba da cewa
“Har ga Allah ka fara kaini bango kark……”

Maganar tasa ce ta mak’ale sakamokon hango Siyama da ya yi tsaye a bakin k’auren gidan tana magana da alamar akwai wani a ciki da take magana da,
‘Anya ba gamo na yi ba kuwa?’
Ya yiwa kansa tambayar a cikin ransa yana mai jin wani sanyi yana ratsashi,bai gama
dawowa daidai ba
Jidda ta fito tana hararar Siyama wadda ta tare hanya ta hanata fitowa har sai da ta sauk’e mayafinta daga kai tukunna ta bata hanya ta fito daga gidan,ahankali Yassir ya motsa bakinshi yace “woow”
ba tare da sautin woow d’in ya fito ba.
Girgiza kai sir Najeeb ya yi kawai ya juya dan ya san tabbas maata Yassir ya gani….

Wani tashin hankalin takaici ne ya lullube sir Najeeb sakamokon had’a ido da sukayi da Siyama dan yana juyowa kamar ance ta d’ago suka had’a ido,wato ita Yassir yake k’arewa kallo shine ya k’ame haka….
Dakyar ita kanta ta sunkuyar da kanta k’asa ta ci gaba da takawa inda suke tana jin yadda k’irjin ta yake bugawa
ahankali ahankali…..
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 18
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Manubiya tana chan d’akin su Siyama dan inna kara ta yi ta ce a tafi da ita chan idan an zo d’aukarta a d’auke ta a chan.Haka nan aka wuce da ita d’akin Anty umma bayan inna Baba ya Nafi’u da ya Musbah sun gama yi mata fad’a sun yi mata sallama had’e da saka albarka..da kyar aka b’anb’are Manubiya daga jikin su Baba tana wani Irin kuka kamar za ta shid’e!

Ba k’aramin mamaki Inna ta ji ba da taga maman Abbakar
da maman Baraka sun zo mata,dan ana fita da Manubiya sai ga su sunzo suna ta washe baki kamar ba su ba,sai da suka zauna a d’akin suka shiga yi mata Allah ya sanya alkhairi tukunna ta tabbatar da gaske wajen ta suka zo dan sam ita bata yi expecting ko iskar su ba…kasancewarta mace mai kawaici yasa kawai ta karb’esu ba yabo ba fallasa,daga haka ta gaya musu inda amaryar take.

Kan Manubiya har ya fara juyawa tsabar turaren wuta,a
neighbors d’insu dama akwai wata mai siyar da kayayyakin gyara,haka aka had’a da wanda Inna ta basu kafin su fito da na matar da na wajen su mama ake ta banka mata,dan dama ita inna kunyar fulani ba lalle ta barta ta cewa Manubiyan tayi ba.
Haka suka d’aura ta akan kujerar tsugunno itakam kanta in banda ciwo ba abunda yake yi mata.
Har zuwa wannan lokacin ba matar Baba Habu ba matan Uncle babu y’ay’ansu kamar
ba biki akeyi ba.
Chapter 27 · 0% Book details