← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 137

Sashe 102

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar Daddy ya san meye a ransa hakanan shi da Abhi suka matso kusa da Junior Abhi ya d’an juyo da shi a hankali gaban Daddy yana fad’uwa dan bai san ta ina zai fara had’a jini da Kausar ba..yana murna Yassir ya tsallake rijiya da baya yanzu kuma ace innocent Yashjub d’insa ne a ruwa…tausayinsa ya ke ji matuk’a dan tun d’azu ya lura da halin da ya shiga…
Ahankali ya kalli Junior yace
“Zaka iya aunawa?,kwanakin?”
Dan a yanzu bashi da wani burin da ya wuce ya ji ance cikin nan ya fi sati biyu…

Sai da Junior ya juya ya kalli Yassir wanda ya ke yi masa wani kalar murmushi,Dan tunda ya tura masa last message da video ya lura tarkonsa ya kama kurciya..
Had’e fuska Junior ya yi ransa a b’ace hankalinsa a tashe ya kalli su Daddy yace”Eh amfanin abun nan da na d’aura mata ma a cikin nata kenan,new invention ne….[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 38
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Tana shiga ta tarar da su ita da su Yasira…
Ganin yanayinta ne ya sake d’aga musu hankali dan haka suka rufar mata da tambayar “mai ya faru?”.

Ba ta b’oye musu ba dan zuwa yanzu tana so ta gogawa Daddyn bak’in jini a idanun y’ay’an nasa ta yadda za su tsaya mata su bi bayanta a kan komai.
Komi ta kwashe ta sanar da su tana kuka abun tausayi wanda hakan ya sa Yadira da Yusra fashewa da kuka suma…
Yasmeen kam ta d’an ji babu dad’i tunda uwa uwace sai dai kuma har ga Allah ita ba ta ji haushin Daddy ba,Yasira da Ya’isha ne suka fi kowa fusata Ya’isha har da cewa “ai da ba ta fito ba!”da ya ce ta fito d’in.

Sosai suka rarrashi mahaifiyar ta su wadda hakan da suka yi ya sa ta d’an ji sanyi,daga nan ta kalli Baba larai tace mata “suna sama suna meeting Larai kin san me ya kamata ki yi a halin yanzu ko?”

“Dalla dalla ma kuwa!”
Baba Larai tace,daga haka ta mik’e ta fice Ya’isha da Yasira suka bi ta Yusra da Yadira suka zauna suka ci gaba da rarrashin Mommy yayinda Yasmeen ta fice ta basu guri,dan tunda Mommy ta fara magana da Baba Larai ta fahimci what they are up to…ba ta against wai Kausar ta auri Yash kawai ita Asiri ta tsafin nan na su ne ba ta so sannan makircin su har ga Allah ya yi yawa,gashi ba ta Isa ta ce komai ba.

Mommy tana fita Yassir ya shigo…kwata kwata ya kasa
gane kan dalilin wannan dramar da Kausar ta gabatar,zai je ya sameta su keb’e su yi magana ya tambayeta dalili amma for now tun kafin iyayen sa su yanke wata muguwar shawarar da zata tarwatsa shi gara ya zo ya fito kawai ya gaya musu zai aureta…a yanzu babu lokacin pretending ko actin domin a yadda abubuwa suka gudana da abunda tayi ya san tsaf su Daddy za su ce Yashjub ya d’auki responsibility d’in cikin da ya yi wa Kausar ko dan kar sunan family ya lalace.

Ba su kaiga fara magana ba shima Junior wanda sai yanzu ya dawo daga had’o results ya hawo saman ya shigo cikin parlourn.

Ganin kowa jigum ya sa shima ya nemi waje ya zauna ya yi
shiru….sam ya k’i yarda ya kalli inda Yassir yake ma sakamokon wani haushi da takaicinsa da yake ji.

Numfashi Daddy ya fesar kafin ya kalli Junior yace”ya bayanin
result d’in???”
Mik’ewa Junior ya yi ya kai masa takardun da ya shigo da su na results d’in a envelope tukunna ya koma ya je ya zauna sannan yace” irin na d’azu ne cikin exactly 12 days ne..na yi kwakwaran bincike yadda ya kamata,sai da na je ma na sake d’aukar jinin nata na yi binciken komai kamar yadda ka ce ga kuma scanning d’in shima.”
Dubawa Daddy ya yi ya bawa Abhi shima ya duba.

Shiruuu parlourn ya kasance daga nan kafin Yassir yayi gyaran murya
yace”Daddy idan ba damuwa ni na yarda zan auri Kausar!!!
Akan dai ta fita ta tonawa family d’innan asiri on top
of that ta d’auki d’an d’anuwana ta tafi dashi tayi masa raino da tarbiyyar single parent
Ni Naji na gani zan aureta
tunda dama ina sonta.”

Cikin katseshi Daddy yace
“Yassir I’m sorry kawai ka bar maganar nan,ka san cewa Kausar ba za ta yarda ta aureka ba,tunda har mahaifiyarka ta fad’amawa watak’il ba ka sani ba ne amma ta nuna ta kuma ce ba za ta tab’a aurenka ba don ba ta sonka…k’iri k’iri ta bijirewa auren ku kwanakin baya so inaga yanzu is not the right time ace za ayiwa Kausar dole
she’s stubborn
I think she’s capable of anything za ta iya tafiya d’in kamar yadda ta fad’a kuma na tabbatar sai ta yi using wannan Yaron against Yashjub besides bai kamata mu bari ta tafi da Yaro ya rayu kamar yadda ka fad’a ba.
Also akwai abunda ta shirya tunda har ta fara maganar tafiya dan Kausar d’in da na sani ba za ta yi abunda ta yi yau ba tare da ta tanadi kwakkwaran plan ba….ai ta ga ta samu ciki so tanada weapon dan haka ya zama dole mu yi mata shigar sauri kafin ta yi b’arna.
Sannan Yassir ko an yi aurenka da Kausar ba za ku zauna lafiya ba ta dinga taso da fitintunu dan zatace an yi mata dole ne,again kamar yadda ka
fad’a kana sonta so za ta ke juyaka ne kawai!
In zan baka shawara ka d’auka dan Allah ka hak’ura da Yarinyar nan har abada.

Cikin d’an uwanka ke a jikinta
haba mana kwab’ar kar ta yi yawa.

Sannan ba zan ji dad’i ba
Ni kaina idan aka ce ka d’auki
responsibility d’in abunda ba laifin ka bane ba.”

Da k’arfi gaban Yashjub ya yanke ya fad’i dan a kaff cikin maganganun Daddy tun kafin ya fito ya fad’i abunda yake ransa ainun ya fahimci inda zancen zai dira dan haka ya runtse idaunsa da mugun k’arfi yana sauraron Daddy da ya ci gaba da cewa”some facts cannot be denied!!kasancewar ba na son Kausar ba shi zai sa in rufe ido in k’i gaskiya ba!sannan ko babu komai nima y’ay’a mata ne guda shidda a gabana,idan wani ya yi musu haka ba zan ji dad’i ba!
A al’amarin nan Abu na farko da zan so ka saka a kanka Yashjub shine ba zan bada goyon baya a zubar da ciki ba saboda haramun ne.

Sannan ka yi hak’uri Yashjub kaima na san ba laifin ka bane ba amma itama ba laifinta bane ba saboda kamar yadda ta fad’a da gaske ne maganar da Likita ya yi akan mahaifarta lokacin na ji zancen dan haka ka ga ba za ta so ciki da gangan ba tunda ba zata yarda ta yi abortion ba kuma ba za ta so ta haihu babu ciki ba.Ta yiu tricking d’inka ta yi da gaske amma tabbas na san ba ta yi tunanin za ta samu ciki ba.
Abunda nake so ku fahimta a nan shine k’addara ce ta fad’o mana…. idan muka ce Kausar ta zubar da cikin nan considering health condition d’inta to mun zalunceta kuma ba zan ma bari a zubar da cikin ba,idan kuma aka ce ta haihu babu Miji shima mun zalinceta kuma na san ma ba za ta yarda ta zauna da mu ba….kuma duk daren dad’ewa kowa ya san Yaro na Yashjub ne dan gaskiya ba ta b’uya.”
Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin ya kallesu one by one tukunna yace”which is Y na yanke shawarar abunda ya kamata a yi a rufawa kowa asiri.Yashjub k’addara ta riga fata kuma an zo wajen da dole sai ka yi hak’uri ka danne zuciyarka an rufawa juna asiri..ni Mahifinka ne har abada ba zan yi abunda zai cutar da kai ba sai dai in yi wanda ba zai cutar da kai ba wanda zai rufa maka asiri. Ka dai ji dalilan da na bayar kuma na san ka fahimta…dan haka ka auri Kausar!
A samu ta haihu lafiya daganan duk decision d’in da ka yanke ba zan ce komai ba!
Ko wanne family suna da nasu secret d’in cikin jikinta it’s just two weeks idan aka yi aure za ta haihu ne on time asirin kowa a rufe duniya ba ta sani ba.Yaro kuma kai ka san yadda zaka yi a gaba ka fitar masa da hakkinsa ba tare da an kwaresa ba.
Ka yi hak’uri ka d’auki responsibility d’inka,na san ba laifinka bane ba amma duba da yadda Yaron nan zai zo duniya a ganina idan aka barsa da ga shi sai Kausar a inda ba mu sani ba to gaskiya ba mu yi masa adalciba kuma kai ka san wacece Kausar! ba ta nustu ba ma ballantana ta yiwa wani tarbiyyar da ta kamata.”

Ajiyar zuciya Abhi ya sauk’e kafin yace”Daddy abunda ka fad’a gaskiya ne! sannan its the only easy option we’ve got dan duk wani ba shi ba to
akwai consequences”

Mik’ewa tsaye kawai suka ga Yashjub ya yi….yana jin kanshi yana wani irin juyawa yace”Daddy idan na auri Kausar zan iya mutuwa amma kamar yadda ka fad’a k’addara kowa da kalar tasa…zan je in samu Manubiya in gaya mata komai duk abunda tace a yi shi za a yi
Wannan rayuwar mu ce
Na ci amanar ta
A ganina this should be her decision to make.

Dukda cewa idan na auri Kausar zan iya mutuwa amma idan har ta bi bayan abunda kuka hango kuka fad’a shikenan na yarda zan aureta d’in har zuwa lokacin da za ta haihu!.
Idan kuma ba ta yarda ba i’m sorry to say this amma Kausar is free to do whatever the hell she’s planning on doing,ban damu ba!”
Yana gama fad’in haka
ya juya ya fita ko bi ta kan Daddy da yake cewa “yanzu zama za mu yi mu jiraku kenan kake nufi?”bai yi ba.

Sai a lokacin Yassir ya d’an samu nutsuwa…
Chapter 102 · 0% Book details