← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 137

Sashe 46

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shiruu duk suka yi kafin chan Mommy tace”Allah ya sa mu dace,sai kuma ta kalli Yassira tace”Yasira,ba na son fad’a tsakanin ki da Yahanasu bana so ki yi mata komai…”
K’ura mata ido Yasira ta yi ba tare da tace komai ba,wanda hakan ya sa Mommy ta matso kusa da ita ta dafa ta tukunna tace”Kamar yadda Baba larai ta fad’a’Ummi!Munirat!Mannubiya!Yahanasu duk kar ki bari hayaniya ta tashin hankali ta shiga tsakanin ki da su wanda har zai janyo idanun
Mahaifinku har ma Yash,ban ce dole sai kin yi zaman lafiya da su ba amman kar ki bari su Daddy su fahimci kuna masu jangolo rigimar,mu yi abunda Baba larai ta ce har zuwa lokacin da Allah zai k’addara rabuwar mu da su a samu su kama gabansu.…sannan yanzu the most important thing shine Daddy!,a yadda ya zuciya d’innan komai ka iya faruwa,dan haka inaso da ni da ku mu yi sauri mu gyara mu dawo da hankalinsa garemu idan ba haka ba akwai babbar matsala dan indai har baya bayanmu to komai ya d’auko hanayar lalacewa kenan.”

Jin jina kai Baba larai ta yi kafin ta ce”Yauwa ko ke fa!hakan ne ya kamata and InshaaAllah nan ba da jimawa ba Daddy zai dawo saiti na san abunda zan yi,amman fa ku ma sai kun taimaka!…”
daga nan ta ci gaba da yi musu lecture….
Shiruu kuwa duk suka yi suna sauraron ta….Yadira ce ta fara lura da yadda Kausar take nan sheme a bakin k’ofa dan haka ta kwala kiran Kausar d’in sai
kuma ta nufi inda take suma duk suka rufar mata…..yau ma sai da Yasmeen ta sha wahala tukunna da ikon Allah aka samu Kausar ta farfad’o.

Babu wanda ba ta bawa tausayi ba dan tana farfad’owa da sunan Yashjub ta fara sai kuma ta fashe da kuka.Dan tun d’azu idan ta rufe idanunta Yash kawai take hangowa tare da Manubiya dan ko ta k’i Allah ta riga ta san by now kam suna manne da juna,wallahi wallahi inda ace za ta iya d’aga k’afafuwanta da sai ta nemi gidan ta je a yau idan ba ta kashe Manubiya ba to ba sunanta Kausar ba.
Baba larai da Yasmeen ne suka d’auketa suka yi sama da ita dan jikinta in banda karkarwa ba abunda yake yi ta ma kasa tsayuwa…Mommy da cewa ta yi a kaita asibiti amman sai Yasmeen tace”ba komai stress ne da tashin hankali idan ta samu rest ta d’an nutsu za ta dawo daidai,ko sun je asibitin ma abunda za’a ce musu kenan.!”
A d’akin Kausar d’in suka ya da zango tukunna Yasmeen ta fita ta je ta had’o allura mai mugun nauyi su Mommy suka danne ta aka yi mata aikuwa ko gama tsiyaya ruwan allurar Yasmeen ba ta yi ba Kausar ta fara lumlumshe ido nan da nan kuwa ta yi bacci.Sai a sannan tukunna suka samu kunnuwansu suka huta dan kuka sosai Kausar d’in take yi tana cewa”ita fa ba zata kwana a cikin gidan nan ba,ba ta da k’arfi a jikinta dan Allah Yassira ta taimaka mata ta fitar da ita daga cikin gidan nan,a nemo mata Manubiya yau sai ta kasheta……”waye waye..harda shirme hakanan ta dinga had’awa tana yi kafin aka samu ruwan allura ya saka ta a silent.
Su Mommy kuwa a tsaye suka kwana dan tashi d’aya bacci ya k’auracewa idanunsu tsabar tashin hankalin da suke a ciki.
Yadira ce kawai ta d’an runtsa
Mommy kuwa ko zama bata iya yi ba dan abu biyu ne suka had’ar mata,na farko ba wai iya Kausar bace take cikin tashin hankali a wannan rana har ita dan wallahi babban
abunda zai k’arasa kasheta bai
wuce ace Manubiya ta samu ciki ba,dukda Baba larai tace mata “ta kwantar da hankalinta za ta kunce mata jini har zuwa lokacin da za su dawo cikin gida kusa da su da zama a san abunyi”amman sam hankalinta ya gagara kwanciya .
Abu na biyu kuma ‘Ummi da Daddy’!dan tun d’azu take safa da marwa a bakin stairs d’in Daddy amma ba ta ga sauk’k’owar Ummi ba.Tana ganin Daddyn ya zo ya wuce lokacin da suka dawo daga asibiti,a tunaninta magana kawai za su yi da Ummin da saukk’o amman har yanzu an fi awa uku da hawan sa babu Ummi babu motsinta.
……
A kwance cikin sofa Daddy ya sami Ummi a cikin d’akin nasa har ta d’an fara bacci saboda sun d’an dad’e a asibiti tukunna suka dawo,a kusa da ita ya nemi waje ya zauna ya d’an ruk’o hannunta ya na kallon saman goshinta inda Yasira ta daketa wajen har ya d’an yi jaa….farkawarta kenan ta ji ya mik’e dan haka ta shiga bud’e idanunta dai dai ta ga ya nufi fridge da towel a hannunsa yana zuwa ya bud’e ya d’auko ice ya saka a cikin towel d’in ya juyo ya nufota,mik’ewa ta yi ta zauna dai dai ya k’araso tace”ya jikin Yaha?”a hankali ya ce”Alhamdulillah,she’s fine tana d’akinta”tukunna cikin kulawa ya zauna kusa da ita sosai ya fara daddana mata k’ank’arar a inda ya yi jaa yana mai jera mata sannu a d’an rikice….Ummi ba ta san lokacin da ta saki wani sassanyan murmushi ba wanda hakan ya sanya ya tsayar da abunda yakeyi ya shiga kallonta,ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya sunkuyar da kansa k’asa yana tunano ire iren abubuwan da aka yi mata a cikin gidan amman ta yi hak’uri ta zauna,bada hak’uri baya daga cikin tsarinsa amman tashi d’aya a yanzu ya yanke shawarar chanja tsari dan tabbas Ummi ta chanchanci ya bata hak’uri ya jinjina mata…a hankali ya d’auke hannunsa daga kan goshinnata ya runtse k’ank’arar dake a cikin towel d’in a hannunsa duk biyu kafin ya kalleta cikin rashin sanin ta Ina ma zai fara yace”am..Ummi,ki yi hak’u!”
Da sauri ta sa hannunta ta toshe masa baki ta shiga girgiza masa kai alamun kar ya bata hak’uri sannan tace”ba komai,ka d’auka a ranka kamar baka tab’a yi min komai ba kamar su Yasira ma ba su tab’a yi min komaiba…”cikin tarar numfashinta yace “taya zan iya?”
Yanzun ma katsesa ta kuma yi tace”dan Allah dan Annabi komai ya wuce,pls ka manta da komai let’s start a fresh.”Ta fad’i hakan tana murmushi sannan ta sake cewa”plssssss”ta had’e hannuwanta waje guda.
Kallonta kawai ya tsaya ya na yi yana mamakin kyakkyawar zuciya irin tata…yana mai jin k’aunarta tana sake shigarsa. A hankali ya ajjiye k’ank’arar a gefe ya sa hannuwansa duk biyu ya rungumota izuwa jikinsa daidai saitin kunnenta yace”thankyou Saddik’a!you are right!let’s just start a fresh ta yadda zan nuna miki da gaske i’m sorryy and I love you so much!”
Murmushi tayi itama tace”i love you”tana mai jin son mijinta yana sake shigarta.
……
Sai da gari ya fara haske tukunna Yashjub ya farka daga wahalallen baccin da ya yi awon gaba da shi sakamokon zazzab’in da ya rufar masa lokaci guda!
Juya wa ya yi ya kalli Manu wadda ke kwance lamoo a gefensa idanunta a lumshe,wani kalar farin ciki da annashuwa ne suka lulub’esa yana kallonta yana jin kamar kamar ya had’iye ta gaba d’aya ya huta watak’il zai samu sauk’in abunda yake ji game da ita.Yadda fuskarta ta kumbura saman idanunta sukayi luhu luhu ne ya sanya ya d’an ji wani iri dan ya san ya yi laifi!sam baya so ya zama silar kukanta amman kuma wani ikon Allah ji yake kamar ya k’ara!wallahi he can’t get enough of her..Manubiya ita ce mace ta farko kuma inshaaAllah ta k’arshe da ya fara sani amman tabbas ya san she’s different ba lalle a kuma samun irinta a cikin mata ba idan kuma an samu to ba su fi 1%out of hundred ba wallahi..shi kad’ai ya san me ya ji. Ahankali ya matsa gareta yana mai jin yadda gaba d’aya gab’ob’in jikinsa sukeyi masa ciwo, sosai ya shige jikinta yana addu’ar Allah ya basa ikon lallashintan da yake da niyyar yi ba tare da ya sake yin wani laifin ba,wani sassanyen murmushi ne ya sub’uce masa wanda har sai da sautin murmushin ya fito fili kafin a hankali ya sa hannu ya yi hugging nata ya lumshe idanunsa yana mai sauk’e wata nutsatsiyar ajiyar zuciya tashi d’aya ya shiga koro kirari ma Ubangiji a cikin zuciyarsa kafin ya d’aura da addua da sanya albarka a Manubiya
matarsa farin cikin sa cikar
burinsa…. bud’e idanunsa yayi ya na mai kallon fuskarta yace”Baby!”a hankali.
Tun d’azu idanunta biyu dan bacci ba nata baneba,sai dai kuma ba ta jin za ta iya bud’e daidai da kwayar idanunta a halin yanzu…Sau uku yana cewa “baby”jin shiru ya sa ya sake zubawa fuskarta idanu sosai k’irjinsa yana dukan uku uku,ganin tana d’an motsi ne yasanya sa fesar da numfashi a hankali yace
“Alhamdulillah”.
Sai kuma ya sake hugging d’inta ya ruk’umk’umeta kamar wanda akace za’a kwace masa ita……da godiya ya fara kafin
ya d’aura da sanya albarka
sai kuma alk’awarurruka iri iri,har da hawaye sai da Yashjub ya yi yana mai yi mata godiya cike da shauk’i da k’auna bayan wanda ya yi jiya.
Chapter 46 · 0% Book details