← Book details Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 137

Sashe 37

Munnubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki Siyama take kallonta kafin ta kalli inda ta ga ta tsurawa ido tukunna tace”Jidda!ki shafawa kanki lafiya ki rufawa kanki asiri…”

Kasa cewa komai Jidda ta yi tana mai jin yadda kwallah take k’ok’arin zubo mata dan haka tayi sauri tace”ki zo mu je kawai,Aisha in ta fito sa tafi ta wanchan”
Tayi maganar tana mai yi gaba abunta….Tabbas ta san ko da ace tanason ta b’oye sannan ta share al’amarin to ba lalle ta iya ba!dan ba kad’an ba ta ji tsananin ciwon abunda Al’ameen yayi mata,har fa aiki yayarta ta yi a gidansu duk ata sanadiyyarsu amman shine ko sak’on ‘hi’ bata samu daga garesa ba bayan ya dawo kuma ta san ya ji komai.
Tana k’arasawa ta bud’e gaban motar ta shiga ta zauna ta runtse idanunta…k’ok’ari
kawai takeyi ta ga ta hana kanta kuka.

Tun d’azu ta lura da yanayinshi da yadda yaketa faman shishige mata,shiyasa
yanzun ma tak’i yarda ta tsaya opposite d’inshi ko kuma kusa da shi,ba ta son shiga motar Yassir har ga Allah d’ayar motar kuma ta sir Najeeb d’in ce shiyasa ta tsaya tana wasuwasi akan ta bi bayan Jidda ne ko kuma
ta tsaya Aisha ta zo su wuce tare a motar Najeeb d’in…..ba ta gama tunani ba ta ga ya tunkaro ta. Tashi d’aya ta diririce ta kuma fara data sanin k’in bin Jidda da tayi….har ga Allah nervous take zama idan ya matso kusan ta.
Yana k’arasowa daidai Aisha tana fitowa rik’e da robar capulas wadda ke d’auke da turaren wuta har da kasko da ashanarta.

A hankali Siyama ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya
wadda har sai da duk su biyun sukaji,dariya ya d’an yi kafin ya ce da Aishar”kin barmu a rana”
Kallonshi kawai Aisha ta yi a ranta tace “ikon Allah”ita yake yiwa magana amman idanunshi na akan Siyama,shiyasa kawai sai ta yi murmushi tukunna tace”ku yi hak’uri”.
Siyama ce tace mata”ga Jidda chan,bari in je mu tafi tare,ke
kwa taho”.
Dasauri Aisha tace”a’a bari ni in je mu tafi tare da su,ku kwa taho ku biyu.”
Tana gama fad’in haka ta yi gaba,dan ita harga Allah had’in nasu ya burgeta gashi Najeeb d’in nutsattse dashi daga gani…..ko bai fad’a ba ta san yana ciki ne da Siyama shiyasa ta basu space ta barsu su biyu ita kuma ta nufi motar da akace mata Jidda tana ciki mai uban tint
Ita kanta Jiddan sai da ta shiga ma tukunna ta lura da tint d’in tsabar b’acin ran datake a ciki.
Ko minti biyu batayi da zama ba Aisha ta bud’e gidan baya ta shiga dan haka Yassir ya kunna motar bayan sun gaya mishi inda za su je su kwashi kayan daganan su wuce gidan amaryar,sam Yassir bai so
Aisha ta shigo ba so yayi a bashi chance da guda d’aya kawai especially ma Jiddan
dan shi a rayuwarsa yana
matuk’ar son mace fara fat!ga ta wannan ga shape ga kyau ga ta she’s young,
Kuma zuwa yanzu ya lura she’s very calm and innocent dan ba ya jin tayi magana sau uku tun
daga farkon ganinta da yayi har izuwa yanzu..
Ba dan yaso ba ya kunna
Motar yayi gaba yana tuk’in yana satar kallon Jidda yana mamakin abun da yake shirin sakata kuka.

Aisha tana wucewa
Najeeb ya lura da yanayin Siyama…dariya yayi ganin yadda ta yi da fuska kafin yace
“Savior d’in taki ta tafi ko?”
Shiruu ta d’an yi kafin ta d’an girgiza kai kawai.
Murmushi yayi yace “ki fad’i abunda ke ranki fa”.
Shirun da ta yi ne yasa ya sake cewa “to tunda ba za ki fad’a ba bari ni in bada hak’uri dan
ni kaina na san na takuraki,sorry i can’t help it ne shiyasa ayi min afuwa…um..?”
Ya fad’i hakan yana had’e hannuwanshi alamun rok’o.
Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace”ba komai fa”.
“Really?to ya naga sai faman had’e rai kike yi,especially ma a wajen hoto.
Ya fad’i hakan cikin tarar numfashin ta.
Kamar za ta ce masa
Yassir ne bataso sai kuma tayi shiru dan sun fahimci Yassir k’anin Yashjub ne,kar ta je ko shima sunada dangantaka da Najeeb d’in sosai apart from
Abota ta je ta kwafsa..
Wucewar motar su Yassir ne yasa shi cewa”mu bi bayansu
kar mu b’ata,kin d’auke
hankalina
Like seriously banma san lokacin da ya kunna motar ba.”
Ya fad’i hakan yana kallonta
sannan ya d’an matsa ya nuna mata hanya da hannunshi.
Wucewa ta yi shi kuma ya bi ta a baya yana mai jin wani shauk’i da annashuwa suna ratsashi….tun a asibiti ya kamu yau kam ya sake kamuwa katamau ya fad’a tsundum!Adduar shi d’aya Allah ya sa babu wani sannan Allah ya sa ta amince da shi,dan shi kam ya ga mata kuma inshaaAllah sai ya samu da izinin Allah.

Ba kad’an ba ta ji kunya da nauyinsa da ya bud’e mata marfin motar,dan ta san wannan ya fi sa’an su ya Yusuf ma a shekara sosai…..
Sai da yace “bismillah”tukunna ta d’an d’aga kafarta dakyar ta haye motar dan irin kirar jeep d’innan ce mai
tudu da fad’i sosai amma ba ta cika tsayi ba.
Sai da ya rufe mata murfin motar tukunna ya juya ya koma side d’inshi ya bud’e ya shiga ya kunna da sauri dasauri dan ya daina hango Yassir,kuma ya san ba gidan amarya a ka nufa direct ba.
Da kyar kuwa ya hango sa bayan sun fita titin dan haka ya shiga binsa har ya samu
ya tadda shi suka jeru…

Sai da ya jeru da Yassir d’in tukunna ya d’an kalli Siyama wadda take ta ke faman danna wayarta yace “ku dai Mata bakwa gajiya da chatting!”.
Kashewa ta yi ta d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin tace”ba chatting nake ba,pictures d’in d’azu da na yi da wayar nake
dubawa”.
Kallon hawaii d’in tata yayi kafin yace”ai mai hotunan zai turomin clear ones…”ganin ya
samu opportunity yasa ya yi sauri ya mik’a mata wayarshi tukunna ya d’aura da cewa”ki saka min numberki sai in yi miki sendin ta watsapp idan ya turo”.
Kamar ba zata karb’a ba sai
kuma ta karb’a ta rik’e wayar ahannunta ta shiga jujjuyawa…..da kyar ta gano inane gaba sakamokon hasken da ta yi sai kuma ta rasa ta yadda za ta yi sliding dan babu alamun touch ko hanyr dake nuna mata ta inda zatayi sliding keyboard d’in ya fito,kuma ita harga Allah bata shirya basa number ta ba!bata dad’e da fita daga bak’in cikin ex boyfriend d’inta ba wanda
har ya gama cin amarcinshi ya dawo sai faman naci yake yi mata tsabar ya raina mata wayo ko me yake nufi da ita oho. Bata shirya samun 2heart break ba..had’in su Manubiya is from heaven
Allah ne yayi had’insa, ita kuwa ba za ta d’aukowa kanta dala babu gammo ba…..
Shirun da yaga tayi ne ya sanya ya d’an sosa k’eyara
kafin yace”okay fine!can i have your number,actually i need it..ba wai saboda sending pictures ba”
Ya fad’i hakan yana mai yin kalar tausayi da fuskarshi.

Murmushi kawai ta d’an yi..ba tare da ta san ya za ta yi ba ta d’an shafa kan wayar, da
ikon Allah kuwa sai taga ta bud’u,tashi d’aya ta hango
Phone dan haka ta shiga ta juye masa digits d’in nata daga haka ta mik’a masa wayar tana da ta sanin bashi.

“Tnx”yace
Sai da ya kira ya ji ya shiga wayarta tukunna yayi saving ya ajjiye wayar yaci gaba da janta da hira. Sama sama ta ke d’an biye shi..ya lura Siyama irin y’an matan nan ne masu jan aji shiyasa tashi d’aya ya fahimci zai sha wahala..sam bai damu ba dan shi indai za ta kulasa to ba ruwansa..tabbas ya san sai yanzu zai fara soyayya!a lokacin da Ya’isha take ja mishi rai k’ulewa yakeyi ya ji haushi amma da ikon Allah ko fushi ya kasa yi anan,duk kalar basarwa da cin maganin da Siyama take ta yi sam ya kasa yin ko da fushi sau d’aya d’an kad’an ne.

A b’angaren Siyama kuwa ba wai jan aji bane kawai ita bata so ta zak’e da shi dayawa ne
har ga Allah ba ta so ta saki jiki dashi gudun kar ta je ta fara sonshi
A samu matsala.

Suna tafe kuwa Ya’isha ta kira shi,sarai ta lura da yadda ya yi da farko kamar irin baya so ya amsa a gabanta d’in nan.

Sai da Ya’ishan ta sake kira tukunna ya d’auka ko tsayawa jin me zata ce bai yi ba yace”ina driving zan kiraki”

Ba ta ji me akace daga d’ayan b’angaren ba sai ji ta yi shi yace”Nndc quarters!da sunan layi da number gida…..”
Yana gama fad’in haka yayi sauri ya kashe.

Ba ta san wacece ta kirasa ba amman tabbas ta sake yin dana sanin basa numberta da ta. Ba ta yi mamakin yadda ya ci gaba da flirting yana mata hira ba dan ta riga ta san halin maza,shiyasa kawai ta bisa da “um,um um…”
A haka suka tsaya suka d’auki
gado da ragowar kayan kitchen aka had’a su da manyan motocin d’aukar kaya da masu kafi
suka wuce.

Sun d’anyi tafiya mai nisa kafin suka k’arasa gidan Yashjub
dake a unguwar sharad’a nndc quarters..dank’areren gida mai hawa uku!
Tun daga waje suka fara kallon aljannar duniya,tun kafin a shiga ciki kuwa suke fara ganin ikon Allah dan gate d’in gidan ma……
[17/09, 8:03 p.m.] Hauwajidda: MANNUBIYA
(Book 2)
Page 19
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

K’ok’arin juyawa itama Manubiyan ta fara yi…a hankali cikin tsananin mutuwar jiki Inna ta mik’e ta k’arasa inda take dai dai ta gama juyawa,sai da ta juyar da ita tukunna ahankai murya cike da rauni tace”durk’usa!”

Shiruu Manubiya ta yi ta k’i motsi sai da Innaa ta sake cewa”durk’usa!”
Tukunna a hankali ta durk’usa a gaban Ya’isha tana wani irin kuka.

Jin jina kai Inna ta yi kafin tace
“Allah ya yi miki albarka”
Gaba d’aya parlourn a tare aka amsa da “Ameen”har su Yahanasu.
A hankali Innaa ta cika ta
ta kalli Iya ramma tace”ki kaita ta gaida ragowar.”
Chapter 37 · 0% Book details