← Book details Boyayyar Alaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 82

Sashe 73

Boyayyar Alaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai ko a lokacin ma ni ne na yanke watannin da zamu zauna, dan haka sai ranar da naga dama za'ayi wannan rabuwar ki daina
aga min hankali yanzu, ki daina
ata min rai, kuma ko yanzu hakkina zaki bani an nothing else." Yayi maganar da kwarin gwiwa akan fuskarsa yana kallonta da fusattatun idanunsa.

Karfin halinsa bazai daina bata mamaki ba.

"Okay machine ka mayar dani ko me?" Kansa har juyawa yake saboda yawan maganar da take sakasa bai san yaushe Jiddah ta koyi magana mai tsayi ba har haka ba.

Ji kawai tayi ya sunkuya ya
auketa dukkan ta, zaro ido ta shiga yi gabanta na mugun fa
uwa duk yadda take tunanin Junaid Dikko ya wuce nan.

Bai sauketa a ko'ina ba sai a
akin baccinsa akan gadonsu, ganin yana
arin cire belt
in jikinsa ta sauko daga kan gado.

Yana
arin kamata ta
aga hannu ta ri
o masa wuya ya yi saurin zare mata hannun daga jikin wuyan sa, yana kokarin zuwa gabanta ranta a mugun
ace take fa
in.

"Wallahi karka karaso kusa dani zanyi maka abunda baka ta
a tunani ba na rantse da Allah, Haba! meka
auki kanka ne? kayi yadda kaga dama da jikina ka tsallakeni k
barni shikenan buqatar kanka ta biya?

Toh karka manta har raping dina kayi acikin gidanku, kuma ko kara na kai sai anyi maka hukunci sannan shine sanadiyar kwanciyya ta a asibiti, karka
auka bani da wayau wannan qaron zan baka mugun mamaki duk lokacin da kayi yunkurin kai hannunka jikina zan nuna maka waceceni a lokacin, niba sauran matan daka sani bace a baya wa
anda zaka dauka a titi ka biya su da ku
in da bai fi su sha ruwan pure water dasu ba.

Magana na ta karshe ka sawwake min aurenka saboda lokacin yayi ni bana sonka kuma bazan fara sonka ba." A cikin maganganunta babu wanda yafi kona masa da
ata masa rai irin wai na bata son shi.

Junaid ya wani irin fisgota ya matseta jikin bango ya shake mata wuya, sosai idanun Jiddah suka fito waje ta dinga kallansa cike da tashin hankali.

"Baki san darajar so ba ko? baki san mutuncinsa ba ko ka
an ko?

Toh zan iya jure duk wasu munanan kalaman da zaki fa
a min amma banda abu biyu.

Na farko karki
ara furta bakya sona a gabana dan zaki sha mamaki na, tabbas nasan kina sona ki daina pretending ki daina walahar da zuciyata hakan nan.

Kece macce ta farko dana zauna ina tsarawa kalamai masu wuyar fita daga bakina shine kike
arin shunning
ina.

Na biyu ko zaki mutu bazan sakeki ba wallahi tallahi ki shiryawa zama dani dan auren mu babu saki a cikinsa." Yana ganin yadda hawaye ke ambaliya sosai cikin fuskarta, gabaki
aya tayi laushi ya ri
o ta jikinsa yana rawa, a haukace ya shiga lashe hawayen yana riqe da ita ajikinsa daidai kunnenta cikin rawar murya ya shiga fa
a mata kalaman da ni kaina mai rubuta muku labarin ban san ta yadda zan hadddace su ba har na rubuta muku.

Wannan qaron hawayen Junaid Dikko ke zuba cikin fuskar Jiddah itama da nata hawayen.

Ganin hawaye a idon Junaid ba qaramin karya mata zuciya yayi ba, ya saketa a hankali ya koma kan bed ya zauna yana dafe kansa.

A hankali ta sulale ta zauna akan marbles, ha
e kanta tayi da gwiwa ta cigaba da shesshekar kukanta, tabbas tana son Junaid Dikko har yadda baki bazai iya furtawa ba, idan kuma ta tuna da auren da xaiyi sai taji komai ya fice mata arai saboda tana da kishi wanda batasan kalarsa ba dan mugun haushin Junaid
in takeji sosai.

Miqewa tsaye tayi cike da karfin hali ganin tana
arin ficewa daga room
in da sauri ya karaso ya dakatar da ita.

"Idan kin shirya zama dani a matsayin miji nayi miki alkawarin baki farin ciki har karshen rayuwarki, wallahi a shirye nake da na zama bawanki inhar zaki bani dama na gyara duk wani kuskure na da nayi a baya.

Abu
aya na sani bazan iya rayuwa babu ke ba.

Tunda Allah ya ha
a ni da ke naji babu wata mace da take burgeni ko take bani sha'awa ko nake son komai nata sai ke, please kizo kawai mu kwashe kayanmu mu koma
asar Paris daman acan muka fara rayuwa kizo mu koma mu cigaba da rayuwarmu acan yafi Alkhairi, naga alamar idan kina
asar nan canza miki tunani za'a yi akai na." Ya qarasa zancen yana kallonta.

Ka
a kai ta shigayi tana fa
in.

"Amma meyasa son kanka yayi yawa Doctor? kana cikin laifi kuma kake son aikata wani laifin?

Toh ba dani ba, sai dai idan da Khairiyyah zaku tafi ni babu inda zani." Jin ta ambaci Khairiyyah yasa komai dake cikin kansa ya fita.

Yana ji yana gani ta fice daga cikin gidan, ya rasa inda zai tsoma kansa saboda tarin damuwar da yake ciki.

Sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta samu abun hawa, kai tsaye gidan Ummah ta nufa acan kasan ranta tana jinjina son kai iri
n na Junaid Dikko.

Tun daga lokacin kuma bata
ara ganin Junaid Dikko ba, ko kiran da yake yi mata a waya da sakonnin da yake tura mata duk ya daina har ta dawo kuma tana damuwa da rashin kiran nasa.

Jidda ta zana jarabawar ta ta shiga nursing school cikin nasara kuma ta kawo mark
in da ake bukata.

Satin da za'a daura auren Junaid da Khairiyyah a satin ta fara zuwa school daman Abba ya samo mata driver.

Junaid kuwa ya tattara kowa ya saka musu ido, Khairiyyah kuma tuni ya da
e da blocking duka numbobinta bare ta takura masa.

Ranar jumu'a ana tashi daga massalaci aka
aura auren Junaid da Khairiyyah,
aurin auren da ya halarci manya
an kasuwa da shugabannin gwamnati, daman ana gama shafa Fatiha a motar Abdul-hakeem suka taho baima jira Abdul-hakeem ba ya fisge car key
in Abdul-Hakeem
in yabar masallacin.

Allah kadai yasan abunda yakeji a wannan lokacin ga wani irin zazza
i da sanyi da yaji yana shirin rufesa lokaci
aya.

Wannan karon ko marmarin xuwa gidansu bai yi ba nashi gidan ya nufa da har an jerawa Jiddah kayanta a sama ita kuma Khairiyyah zata zauna a part
in kasa wannan umurnin Abba ne babu maganar raba musu gida.

Dangin Abba dake can Dikko duk sun halarci
aurin auren ana dawowa kuma gidansu Mamma aka wuce aka ha
aramar liyafa, daman kwanakkin biki na matsowa Mamma ta fara gyaran Jiddah ta ciki da waje harda maigyaran jiki ta musamman ta dauko mata.

Itama Ummah a gefenta duk kayan gyaran jikin da zasu ha
a yartata su kwato mata daraja a gidan aurenta ta kawosu.

Xuwa lokacin Ummah tasan Junaid din zai yi aure.

Sai dai Mamma tayiwa Ummah bayanin komai cewa Khairiyyah yaso ya aura tun farko Allah bai yi ba sai ya fara auran Jiddah.

A duk daren Allah Jiddah sai tayi kuka har wani zogi xuciyarta keyi mata idan ta tuna Junaid nada wata matar a gefe sai takanji wani irin kunci ya rufe mata zuciya.

Hankalin Mamma ya tashi da taga damuwa na
arin kwantar da Jiddah ga wata irin rama da ta shiga yi,
Mamma ta ha
a ta da Allah da Annabi akan ta rage wannan damuwar kar ya shafi cikin jikinta, wanda sai a lokacin Jiddah ta san tana dauke da ciki a jikinta.

Jikinta yayi mugun sanyi baya Mamma ta fita ta gama rarrashi ta
ora hannunta akan cikin ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi.

Bata ta
a tunanin zata samu ciki tare da Junaid Dikko ba, hawayen idonta suka kasa tsayawa murmushi ta shiga yi ita
aya tana ta shafa cikin jikinta bata ta
a tsintar kanta cikin farin ciki irin wannan lokacin ba.

Wani irin kaunar abunda ke cikin cikinta yazo ya lullubeta, a ranar kwana tayi tana addu'ar Allah ya raya mata abunda ke acikinta yai mata tsawon rai na kula dashi har karshen numafashinta, ya kuma karesa daga fitinar duniya yasa kar xunubban mahaifinsa ya shafe shi.

Wani irin tsoro takeji tsoron kar wani abu ya samu
an jikinta take, dan haka zatayi addu'a zata cigaba da addu'a komai zai samesu yazo masu da sauqi.
*#KHAIRIYYAH*
Ummi tabi Khairiyyah da kallo da ta fito daga toilet tana bin bango duk tayi wani irin zuru-zuru, ta kara komawa ta kwanta wannan karon harda jan duvert ta rufe duka ilahirin jikinta.

Da mamaki Ummi ke fa
in.

"Kin fasa zuwa wankin kan kenan?" Khairiyya tace.

"Ummi baki san ya nakeji bane, wankin kan nan a hakura zuwa anjima idan naji daidai sai naje." Baki bu
e Ummi ke fa
in.

"Amman kin san babu lokaci Khairiyyah ko kin manta yau ne dinner party
in ku." Khairiyya ta sake cewa.

"Bazaki gane bane Ummi, wallahi ni ka
ai nasan azabar da nake sha." Ummi tace.

"Amman sai da nace mu tafi asibiti kika ce kin sha magani gashi ko Mami kin hana a sanar da tun safe kike amai." Shiru kawai Khairiyyah ta yiwa Ummi bata kara cewa komai ba har kusan minti goma sha biyar ta miqe zaune Ummi dake danna waya tana ganin ta dafe kanta lokaci
aya.

"Ummi ki ha
o min lipton da lemun tsami dan Allah." Shiru Ummi tayi kamar bazatace komai ba sai kuma ta fice daga dakin dan hadowa Khairiyyah ruwan lipton
in da take bukata.....
#ASMY B ALIYU
#BA (secret Relationship
#Junaid
#khairiyya
#jiddah
[10/23, 6:23 PM] Asmy B Aliyu: *BOYAYYAR ALAKA*
(Secret Relationship)
*PAID BOOK#500*
ASMY B ALIYU
ONLINE BUSSINESS IDEAS CLASS
(DABARUN INGANTA KASUWANCI)
TARE DA DEEJARH BERVER.

DATE :- 10 November 2023
VENUE:- TELEGRAM
PRICE :- N4000
- YADDA ZAKI BUNKASA SANA'ARKI
- YADDA AKE ADANA RIBA.
- DABARUN KASUWANCI
-YADDA AKEWA COSTUMERS.
- SIRRU
AN KASUWANCI
- SAMUN MABIYA A KAFAR SADA ZUMUNTA.

YouTube,IG,TIKTOK.

BAYANI DANGANE DA WASU SANA'OIN...
- YADDA ZAKI FARA SANA'AR CAKEPOPS.
- YADDA ZAKI FARA SANA'AR PANCAKE MIX
-PUFF PUFF MIX
-GARIN DANWAKE
-GARIN KUNUN AYA
-TEA SPICES..
- HAIR GROWTH OIL.
Chapter 73 · 0% Book details