← Book details Boyayyar Alaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 82

Sashe 30

Boyayyar Alaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naga tunda kazo office
in nan naga bakayi min magana ba." Shiru kawai Junaid yayi ya zubawa Dr Sharif
in ido wanda amsarsa kawai yake jira, Dr Sharif ya nisa yana fa
Wallahi mahaifiyarta ce take da matsalar kidney kwanansu kusan hu
u anan yanzun maganar da nake yi maka aiki ake so za'ayi mata ku
in aikin kawai 500k a kasa kafin sauran ku
in siyan magani su biyo baya.

Matsalarsu ta kasa fita kaina karfina bai kai ba dana taimaka masu, tunda suka zo asibitin nan nike basu ku
in abinci da kananun abubuwa." Shiru dukansu suka yi kafin Junaid ya kallesa a nutse yace masa
Ka bani details
inka zan saka maka ku
in." Abdul-Hakeem bai wani girgiza ba dan yasan ya saba irin wannan taimakon
Amman da shara
in idan har yarinyar ta amince." Wannan karon da mamaki cikin fuskar Abdul-Hakeem yake kallon Junaid
in, Dr Sharif ya
ara gyara zaman gilashinsa ya maida duka hankalinsa kan Junaid din, wannnan karon yana tunanin abunda xaiyi kamar ba daidai bane dan yasan zata taimaka mashi shima zai taimaka mata, cikin rashin kallansu yake cewa
Idan har zata yadda ta aureni na tsawon watanni shida." Kallonsa kurum Abdul-Hakeem keyi mamakin Junaid
in ya hanasa magana, da mun cika watanni shida zan sallameta xan sakata makaranta zata cigaba da zuwa makaranta tamkar kowane yaro." Murmushi kurum Dr Sharif yayi
Meye a zuciyarka Junaid na auren watanni shida da zaka mayar da yarinyar mutane bazawara?

Ka saba taimakon mutane meyasa wannan karon taimakon naka yazo a wani iri?" Dr Sharif ya fa
a yana kallon Junaid
in, girrgiza kai ya shiga yi yana fa
in "Wannan kuma wani sirrina ne kai dai kayi abunda nace idan ta yadda a shirye nake kowane lokaci ka
kirani." Kallon tuhumar da Abdul-hakeem yake yi masa yasa ya miqe ya nufi
ofa yana yiwa Dr.

Sahrif sallama.

Bayan fitarsa da kusan minti biyu Dr Sharif ya
aga kai yana kallon Abdul-Hakeem
in shima da yaga yayi shiru
Me Junaid keson aikatawa?

Duk da nasan aurenta xai yi amman Jiddah tayi masa kankanta bazata iya
aukar lalurarsa ba a yadda yake
in nan kuma har na tsawon watanni shida yana morewar ganggar jikinta da ya gama kuma shikenan ta koma bazawara?

Shi dai Abdul-hakeem rasa ma abuncewa yayi dan yasan tunda Junaid Dikko ya bullo da wannan maganar babu wanda ya isa ya tsayar dashi koda shine kuwa, Abdul-hakeem ne ya kalli Dr Sahrif yana fa
Ka yiwa yarinyar magana ina hango wani babban al'amari a tsakaninsu karka yi saurin yanke masa hukunci nasan bazai ta
a wulakantata ba." Daga haka sukayi sallama da Dr Sharif a mota ya samu Junaid, shiga motar yayi ya tayar suka bar cikin asibiti, a hanya Abdul-Hakeem ya kallesa yana fa
Kana tunanin su daddy zasu amince da auren watanni shida a tsakaninka da wannan yarinyar?

Ni abunda ma ya
aure min kai naji ka kira sunanta daman kasanta ne?." Junaid yace.

"Kana tunanin zan tsaya jiran su daddy ne?

Kai nifa auren sirri zanyi da wannan yarinyar babu wanda zai sani har muje mu dawo, banada matsalar wanda zasu tsayamin na samu aurenta, wattanni shidda kawai zamuyi a tare." Ya fa
a yana tsuke fuska
menene amfanin wannan auren?

Amfaninsa bazan kula matan waccen
asar ba har na dawo, kaga kenan amfaninsa ina da inda zan sauke duk wata lalurata kuma babu aikata haramun aciki tamkar yadda kake magana a kullum, so zanyi auren watanni shida da wannan yarinyar shine kawai manufar kaji Abdul-Hakeem."
Abdul-hakeem yace"Kai baka ganin yanayinta karamar yarinya ce fa Junaid dan za su zo sa'anni ita da Assha." Junaid ya ta
e baki"Ai dai mace ce a hankali zata saba da ni." Abdul-hakeem yace"Karka fara abunda baxaka iya kai karshensa ba, dan Allah karka fara wannan wasan Junaid!" Abdul-Hakeem ya fa
a yana kallon yanayin Junaid din "Menene bazan iya karasawa ba?

Kaga malam idan baxaka fa
i alkhairi ba kayi shiru dan Allah." Ya fa
a yana wani ha
e rai lokaci
aya.

Shiru Abdul-hakeem
in yayi bai kara kula Junaid
in ba.

Har
ofar gidan Abdul-Hakeem
in ya karasa dashi, daman mafitar da yake ta son samu ne yasa yake ta bibiyar Abdul-Hakeem
in sai gashi ya sameta cikin ruwan sanyi ba tare da yasha wahala ba, har ya bu
e marfin
ofar ya kalli Junaid yana fa
in "Baxaka shiga ku gaisa ba kullum tana yi min complain baka ta
a zuwa ba." Junaid yace"Zanzo wani lokacin." Abdul-Hakeem ya wani cire car key
in yana fa
in "Yau me yasa baxaka shiga ba
an iska duk kabi ka firgita min mata sai tsoronka takeji, ko waya taji muna yi bakaga yadda take nutsuwa ba, ka fito kawai malam." Da wani kallo Junaid yabisa kafin ya fito daga motar yabi bayansa, tuni maigadi ya bu
e musu
aramar
ofa dan Junaid bai shiga da motarsa ciki ba.

Tana bu
ofar parlorn da gudu taje ta shige jikin Abdul-Hakeem da ya riqeta sosai cikin jikinsa dan bata ma lura da Junaid ba dake tsaye yana kallonsu.

"Sannu da zuwa wanka zaka fara ko abinci zaka fara ci?" Abdul-Hakeem yaja dogon hancinta yana fa
in.

"Duk wanda kika za
a min Madam shi zanyi." Zata yi masa rigima tana
ago kanta sukayi ido biyu da Junaid Dikko da ya karasa shigowa cikin parlorn ya samu waje ya zauna.

Ware ido
inta tayi cike da kunya da kuma mamaki.

A hankali ta cire jikinta daga cikin na Abdul-Hakeem cike da kunya take fa
in.

"Sannu da zuwa Yayan mu." Ta fa
a cikin jin kunya sannan ta kar
i briefcase
in Abdul-Hakeem, murya
asa-
asa take fa
in.

"Kace ma Yayan mu ya tsaya muyi lunch tare." Daga haka ta juya ta nufi stairs.

Ha
a ido sukayi da Junaid ganin irin kallon da yake yi masa yasa shi cewa.

"Madam ta nemi alfarmar ka tsaya muyi lunch tare." Daga haka ya nufi stairs yabi bayan Amaah Dikko.

Kusan cin karo suka yi da ita ta fito sanye da dogon hijab har
asa, kallonta yayi ta turo baki tana fa
in.

"You did not tell me tare zakuzo da Yayan mu." Ya Jawota cikin jikinsa yana sha
amshinta yace "Ko yanzun da kika ganshi motata ce ta tsaya na shigo tasa, kin san halinsa bazai yadda ya biyoni ba." Suka sake fitowa tare, Amaah tana gama zuba masu abinci ta juya da nufin tabar wajen, Abdul-Hakeem yayi saurin riqo hannunta yana fa
in "Ki zauna muci tare mana." Da sauri ta girgiza kanta yasan saboda Junaid taki zama tace "Sai zuwa anjima zanci." Da idonta take roqonsa akan yayi hakuri ya barta.

Sakin hannunta yayi ta juya tabar cikin dining area
in, lokacin Junaid har ya fara cin abincinsa tamkar babu shi a wajen suke abubuwansa, bai jima ba yayi musu sallama, har bakin gate suka rakasa ya tafi.

Yanzu damuwarsa
aya ta yadda jiddah zata yadda da wannan auren nasa kawai yake tunani.

Yana riqe da wayarsa yinin ranar dan yana da lambar Dr Sharif
in,
iran nasa kawai yake jira har washegari da ya shirya ya fita aiki amma shiru, samun kansa yayi da yin addu'ar Allah yasa Jiddarh ta amince masa....
*Account Details*
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin wayar MTN ta 07043079282 Shaidar bita ta. 07065283730*
#ASMY B ALIYU
#secret Relationship
#Junaid Dikko
#Jiddah
[10/23, 6:15 PM] Asmy B Aliyu: *BOYAYYAR ALAQA*
( Secret Relationship)
*PAID BOOK #500*
Asmy b Aliyu
*Account Details*
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin wayar MTN ta 07043079282 Shaidar bita ta. 07065283730*
Tunda kawu Audu ya bu
e baki yana mata bayanin yadda auren Jiddah yazo da wani irin hargitsi jin komai Ummah tayi ya tsaya mata na wucin gadi, bayyanannen tashin hankali ne kwance acikin fuskata tamkar bada Hausa Kawu keyi mata bayani ba.

Wata zufa wacce bata da alaqa da zafi taji tana fito mata ta ko'ina, cikin rawar murya da wani irin tsoro Umma ke fa
in.

"Wannan wane irin aure ne kawu? duka-duka Jiddah nawa take da za'a yi mata irin wannan auran?

A ina ma suka ha
u dan ni ban ta
a saninsa ba?

Toh wannan auren bai zauna min a zuciya ta ba bana jin zuciyata ta natsu dashi, bana jin zuciyata ta qarbesa." Ummah ta qarasa maganar da wani irin yanayi a muryarta wanda bazai fassaru ba.

Baki kurum Kawu ya saki yana kallon Ummah da ta rikice masa lokaci
aya.

"Shin wai wannan tashin hankalin na menene? da yaron nan bai biya an yi miki aikin ba kina ma da kwarin gwiwar wannan maganar ne?

Ki natsu Zahara'u ki kar
i kaddarar da tazowa Jiddah da hannu bibbiyu, bafa karuwanci akace miki tayi ba aurenta aka daura." Ta inda kawu ke shiga batanan yake fita ba ita dai Ummah tayi shiru kawai sai binsa take da ido tana ganin an daketa an kuma hanata yin kuka.
arshe kawu da yagama fusata ya miqe tsaye ya kakkabe rigarsa yana fa
in.

"Idan har na isa dake Zahara'u ki bar yarinyar nan tayiwa mijinta biyayya kamar yadda kowace macce keyi a gidan aurenta.

Anjima zaizo ya dubaki bazaki san auren gata ake yiwa Jiddah ba sai nan gaba." Da haka kawu ya fice daga
akin ransa a
ace, daman Jiddah na hangosa ta
oye, yanayin yadda ya fito ya tabbatar mata da komai ya faru ya sanarwa da Ummah maganar aurenta.

Taya zata fahimtar da Ummah bata goyon bayan wannan auren?

Taya zatayiwa Ummah bayanin saboda lafiyarta ta amince da auren Junaid Dikko ba dan zuciya da ruhinta sunyi ammana dashi ba? har kusan magariba tana zaune a wajen tana kaucewa duk wani abu da zai ha
ata da Ummah, sai da aka fara kiran sallah cikin massalacin asibitin sannan ta miqe tsaye ta doshi
akin da Ummah take da wani irin sanyin jiki ta tura
ofar room
in, hango Ummah tayi a zaune akan carpet tana sallah daman kuma har yanzu jikin nata bai gama yin karfi ba, toilet ta shige tayo alwallah itama tazo ta tada sallar.
Chapter 30 · 0% Book details