← Book details Boyayyar Alaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 82

Sashe 32

Boyayyar Alaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sharif akanta tayi saurin juyowa suka ha
a ido, murmushi yayi mata yana fa
in.

"Baki shiga ba ne? ki shiga ciki mana."
aga kai tayi cikin wani irin sanyin jiki ta kama handle
ofar tana tura
ofar tare da bugun xuciyarta.
ago kansa yayi yana xaune cikin doguwar soofa dake girke a office
in da waya a hannunsa, jin karar bu
ofar ya
ago kansa sukayi ido biyu da Jiddah da tsoro ya bayyane da mamaki shimfide acikin fuskarta, daskarewa tayi a wajen ita bata shigo ba ita bata koma ba.

Hawayen da take taso karsu zubo sune suka yi nasarar saukowa kan fuskarta, hannu tasa tana goge hawayen, shiru yayi yana kallonta juyawa tayi tana kallonsa shima kallonta yake.

"Kace min bakai bane, please kace min wanine daban." Kalamanta yaji suna yi masa tsaye acikin zuciyarsa.

"Ni ne meya faru?" Ya fa
a cike da kwarin gwiwa yana kafeta da idanunsa, bata iya jure kallon cikin kwayar idanunsa wani irin kwarjini ne acikinsu kuma acikinsu ka
ai take ganin kwarjinin, tasha ha
a ido da Mu'azzam bata jin wannan kwarjinin kamar yadda na Junaid Dikko keyi mata.

Muryarta ya tsinkaya tana fa
in.

"Meyesa sai ni? meyasa bazaka iya taimkona ba sai ta wannan hanyar? kaima jikina kakeso, da gaske jikina kake so ba soyayyar gaskiya bace ba.

Idan ba haka ba meya amfanin auren watanni shidda? ka fa
a min ma'anarsa.?" Yana mamakin yadda kalamanta ke
assara sa suna ta
a wurare da dama acikin zuciyarsa.

Yayi niyar ya fa
a mata ma'annar auren a wajensa da kuma muhimmancinsa, sai yaji harshensa yayi masa wani irin nauyi na ban mamaki.

Tsintar kansa yayi da fa
in.

"Wannan sirri na ne bai kamata kiji ba, kawai dai abun da na sani shine bazan ta
a cutar dake ba, ni ba mugu bane, nayi alkawarin bazan cutar dake ba Jiddah.!" Girgiza kai jiddah tayi still hawaye na forming cikin fuskarta da wani irin rauni a muryarta take fa
in.

"Meyesa kakeso ka auren?

Kawai dalili nakeso nasani saboda kafi karfina ta kowane fanni tun ranar da na
ora idona akanka." Wani murmushi ne ya subuce mata wanda baida alaqa da farin ciki take fa
in.

"Da gaske jikina kake so ko? shi ka siya da kudinka ba?

Nagode Nagode da dukkan karamcinka, ban san kalar godiya da zanyi maka ba ma." Juyawa tayi tana jin kuka yaci karfinta ta fice daga office
in duka.

Da ido ya bita yana jin maganganunta na ta
a masa xuciya.

Shigowar Dr Sharif cikin office
in yasa ya miqe yana tsokanarsa da ango.

Murmushi yayi wanda ya tsaya iya fatar bakinsa,
aramar waya ya miqawa Dr Sharif, Kallonsa Dr.

Sharif yake yana jiran karin bayani.

"Ka bata kace zamuyi waya xuwa gobe, sannan zan dawo naga jikin Ummah."
aga masa kai Dr Sharif yayi yana hanya ya kira Abdul-hakeem yana hanya yake fa
a masa sunyi magana da kawu shi zai zama wakilin jiddah.

Abdul-hakeem yace Allah ya kai mu.

Bai ta
a ganin dare mai tsayi da ya hanasa bacci irin wannan daren ba, duk inda ya juya kwanciyarsa maganganun Jiddah ne ke juya masa cikin kansa, idan ya rufe idonsa fuskar jiddah ke gilma masa.

Washe gari da ya shigo suka gaisa da Mamma suna karin kumallo Mamma ta lura da yanayinsa sai dai batace komai ba daman tun maganar auren Khairiyyah ta
auke masa wuta har yayi shirin fita office ta masa fatan sauka lafiya.

Suna xaune a office
in Junaid
in Abdul-hakeem ya
aga ido yana kallon Junaid kafin yace.

"Kai suwa zasu zama wakilanka?" "Malam Halilu shi zanje na yiwa magana." "Ya zakayi da daddy?." "Xuwa anjima zamuje wajensa na daukesa sai muje mu samu kawu Audu." Ya karasa maganar yana kaucewa wacce Hakeem
in yayi masa.

Kamar yadda yace bayan sallar la'asar suka samu kawu Audu da wani abokinsa haka suka tarbesu cikin mutunci, daman Junaid
in ya baiwa malam Halilu ku
in sadaki Naira dubu
ari biyu cikin farar envelop, da hannu biyu kawu ya kar
i ku
in malam Halilu ya roqi alfarmar a bar daurin auren ranar Litinin saboda tafiyar da Junaid
in zasuyi sai sun tsaya Kano ya nemar mata tata visar tunda bata da takaddun shaidar barin
asar.

A bayan booth
in motar aka shiga fiddo da kwalayen sweet da biscuits masu tsadar gaske, dasu goro wanda xa'a raba ranar
aurin aure, sai kuma drinks.

Tunda suka dawo xaman shiru suka xauna a motar, Hakeem
in yana hangowa Junaid girman kuskuren da zai aikata aure ba abun wasa bane yasan Junaid
in yayi nisa duk yadda zai fahimtar dashi baxai sauraresa ba, yasan Junaid Dikko tamkar yunwar cikin sa, idan zaiyi abu da gaske xaiyisa amman karshen auren yake hango masa da rikicin dake cikin sa.

Shima a
angaren Junaid Dikko haka yake
aukar wai shine xaiyi aure ba tare da sanin Mammansa ba, komai jinsa yake yana masa sauri tunda maganar auren nan ta shigo, baiyi natsuwar da yake tunanin zai samu ba.

Kullum Khairiyyah cikin yi masa qorafi take, shi dai jinta kawai yake yi.

Ranar Litinin misalin qarfe goma na safe aka daura auren Junaid Dikko da Jiddah lokacin Ummah ta farfa
o kuma har lokacin kawu Audu baiyi mata zancen ba.

Wayar da Dr.

Sharif ya baiwa Jiddah wacce Junaid ya bata har mantawa take da ita sai taji qararta ta karde wuri take sanin zaman da wayar a tare da ita har kuma xuwa lokacin bata wani sake da Junaid ba.

Tun lokacin da Dr.

Sharif yayi mata maganar tayi
ari ta cika alkawarin da ta
auka tunda ga Junaid
in dai ya sauke nasa take
an daukar wayar Junaid yana tamabayarta ya jikin Ummah take basa amsa da ta samu sauqi, shikenan babu kalmar dake qara shiga tsakaninta dashi duk kuwa ta yadda yake
arin sakewa da ita.

Shi kansa mamakin kansa yake akan jiddah, idan mata yake so akwai wanda suka fita komai na rayuwa da jin da
i amma ya rasa meyasa ya aureta, kullum amsar yake nema cikin kansa ya rasa.

Sai da yau Jiddah tana
an baiwa Ummah ruwan tea da yagama yin sanyi kawu na xaune akan kujerar da aka tana da saboda masu jinya, kawu yayi karfin halin cewa Ummah ta nutsu yana son xasuyi magana mai muhimmanci.

Jin haka jiddah ta miqawa Ummah ragowar tea
in da take bata tamkar wacce aka tsikara ta miqe tsaye ta nufi kofa ko ka
an bata son taga reaction
in da Ummah zata nuna akanta.

Da ido Ummah ta bita tunda ta farfa
o take bin Jiddan da kallo jikinta yayi wani irin sanyi ba irin sanyin da take idan tana rashin lafiya bane, wannan karon akwai damuwa akan fuskarta sosai kuma Ummah daman ya kamata ta tambaya waye ya biya mata ku
in da aka yi mata dashen koda duk da xaiyi wuya ace wani ne ya biya mata, so take ko ina ne aka ci bashi ya kamata ta sani ganin daga Jiddan har kawu babu wanda ya ta
a bu
e baki yayi mata bayani sai hidimarsu suke a tsakaninsu tamkar babu abunda ke damunsu musamman Jiddah da taga damuwa kwance akan fuskarta tasan akwai abunda ke damunta.

Gyaran muryar da kawu yayi yasa Ummah ta mayar da hankalinta kansa ta bashi dukkan natsuwarta ga wani irin faduwar gaba da ta tsinci kanta dashi tun kafin tasan me zai fito a bakin kawun....
#ASMY B ALIYU
#BA(secret Relationship)
#TEAM J SQUARE
[10/23, 6:15 PM] Asmy B Aliyu: *BOYAYYAR ALAQA*
( Secret Relationship)
*PAID BOOK #500*
Asmy b Aliyu
*Account Details*
0004157137
Jaiz Bank
Asma'u Buhari Aliyu
Shaidar biya ta
08086207764
*Katin wayar MTN ta 07043079282 Shaidar bita ta. 07065283730*
Kusan awa
aya yayi akan Meenah kafin ya koma gefe ya dafe kansa,
an moment
in da yayi tare da Jiddah yaji yana sake dawo masa sabo fil acikin zuciyarsa, haka hoton abun ya kasa gogewa daga cikin ransa, haka yaja kafafunsa ya nufi toilet yayi refreshing
in kansa.

Cikin kankanin lokaci ya mayar da kayansa daman ba gidansa ya sauka ba ganin nisan gidansa da inda yake yasa ya kama musu hotel, ganin kamar idon Meenah a lumshe yasa shi bubbuga gefen pillown da ta
ora kanta, bu
e idonta tayi a hankali cikin fuskar da take nuna ta gaji take kallonsa.

"Ki tashi na maidake school." Wannan karon ware idonta tayi akansa kafin tace.

"Na zata sai gobe naga ku
in kwana ka biya." Yace.

"Ba nan zan kwana ba, amma idan kina da ra'ayin kwana anan sai nayi tafiya ta."
age masa kafa
a tayi tana fa
in.

"Shikenan sai da safe a sauka lafiya ni kam tunda ka biya ku
in kwana toh kwana zanyi anan ko ba komai zan sha Ac. ba kamar a makaranta ba da basa yawan bada wutan lantarki ga kuma sauron masifa." Tun kafin ya isa gun da yayi parking motarsa ya turawa Meenah alert na ku
i daman yana da details
inta, kai tsaye gidan mahaifinsa ya nufa kusan goma da rabi na dare, Mamma na tsaye acikin
akin Abba bakin window ta harde hannayenta akan kirjinta tana kallon hancin motar Junaid
in ta sauqe wata irin ajiyar zuciya.

Tafi awa tana kai da kawo a wajen tun Abba na ce mata Junaid ba yaro bane yasan me yakeyi meyasa ta kasa kar
ar kaddararsa da hannun biyu?

Ya ce mata inaji ajikina akwai lokacin da zai canja sai dai lokacin ne bai yi ba yana da tsayi kafin ya canja.

Amma duk yadda Mamma taso ta fahimtar da Abba akan lamarin Junaid ba fahimtarta yake ba.

Har maganar tayi masa na ko a daura aure ya tafi da matarsa kasar Paris
Idan suka dawo sai ayi bikin yace mata.

"Karki zama mai son kanki da yawa doctor kin manta yarinyar karatu take za'a katse mata karatunta za'a shiga hakkinta final year take fa bakya ganin akwai takura aciki." Mamma tace, "Nasan da wannan amma idan ta samu lokaci zata riqa zuwa tana dubasa koda na kwana biyu ne, ni na fison naga Junaid da aure akansa.!" Abba yace.
Chapter 32 · 0% Book details