← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 98

Sashe 98

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Annoor yana zaune a Office dinsa yana shegiyar yangarsa da ya Saba yaga Yan sanda sun cika Masa Office,ko dagowa ya kalle su baiyi ba,Dan sanda suna cewa You are under arrest amma ko kulasu baiyi ba,wani a ciki yace Malam da Kai ake magana Wayarsa yaci gaba da latsawa,tsawa suka Masa ko gezau,wani a ciki ya daga hannu da niyyar marinas Annoor ya rike hannun ya kwashe dan sandan da Marika har biyu,yace ni zaku rainawa hankali kuje zanzo,waya suka yi aka kawo musu motoci da Yan sanda,mutane suka cika makil a Private hospital din nasa,yaki yarda a kamashi,mutane aka taru ana bashi baki akan yaje kawai kar su tozarta shi,yace shi ya Isa yace wai zai min aski Ina askin banza doka ta Bada dama ayiwa wani aski haka kawai,Tara suma da kitso haramun ne? In nayi laifi ka kamani amma wai batun kace min sai mun Maka aski bai taso ba,ko uban waye bai Isa ya min aski ba,yanzu duk akan aski kake wannan masifar cewar Dpo yace ae ai rainin hankali ne,idan laifi nayi quietly a kamani amma zaizo yace zai min aski ubansa ne ya fito min da gashin,Yasan irin kudin da nake kashe Masa,kasan man nawa nake shafawa? Inama ya taba min gashi ya gani,kamani a kamani na yarda idan laifi nayi amma na mene zasu shugo suce za a min aski burar.....Shaver....shaver taci kut....hour suka kwashe Annoor Yana bala'i akan sumarsa,sai da mutane suka dinga Bada Baki sannan ya hakura yabi Yan sanda Station dan shi bai San me yayi ba kawai dai ya gansu a Office dinsa.

KARSHEN BOOK 1
MU HADU A
BOOK 2

MASU SHARHI INA MATUKAR GODIYA

ZAMU HUTA NA KWANA UKU KO BIYAR ZAN DAWO MU DORA DAGA INDA MUKA TSAYA

Book 2
TANTIRIYA A GIDAN YARI
YARAN JAURO

Bangaren su Misam duka za aci gaba.

AsmaBaffa
Chapter 98 · 0% Book details