← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 98

Sashe 28

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya zuba tea din ya Dandana yace not bad amma a dakko Madara a Kara wannan gidan rayuwa cikinsa sai da Madara,Naila ta dakko peak da aka kawo Masa aka rasa da me za a fasa sai wajen me shayi ta koma aka fasa mata ta dawo suka sake tsulawa a shayinsu itama ta zuba Nata,ta dakko bread kamar nata me dadi ta saka kwai a tsakiya tana yaga tana kora ruwan tea,kallonta yayi shima ya fara cin nasa,tace wai mu Maza me yasa muke da Yaudara ne? Spark yace Gender dinmu ce haka,ta cika baki da kwai da bread tace uhmmm? Yace yeah,tace kune dai masu Yaudara, ai da ganinka zaka yi Yaudara ba kadan ba Spark,mata nawa ka cinyewa Bado? dariya yayi ba shiri yace da ace nasan mata ai ta Katanga zan dinga haurawa part din Mata na zama kwarto a gidan Nan,dariya tayi ta sake kurbar tea tace nufinka Kai virgin ne? original ma kuwa,Naila tace kaji tsoron Allah fa,yace da gaske ai ni da ace nasan mace to Beauty zaka bani kawai naje can, yanzu sai ka haura? Ina nan zan sa a kawo min ita ba Wanda ya sani ma.

Naila tace lallai da kuwa kaga namijin kishi,ya Yagi bread and egg Yana cin nasa a wani gayence yace egg din ma ba dadi,tace to kawo ta dauke ledar kwai tare da furta do you think i will beg you to eat? So you can't beg me to eat?ya tambaya, tace yeah,Spark yace ai naga baka da Imani ko kadan ya kwace ledar Kwansa yaci gaba da ci har suka gama ya wanke hannunsa da sabulu tare da kuskure bakinsa,Jamilu ma haka,yace sai me aikin nawa,Jamilu yace gani,yace Start to ya koma kujera ya kwanta Yana kallo Yana danna wayarsa

Naila sai da ta fita ta samo tsintsiya ta siyo harda mopper duk gasu Nan ana siyarwa,ya bata kudi again ta siyo bokiti dasu plate da spoon da duk wasu tarkace na bukata amma sai shegiyar tsada dake a gidan yari ne, tazo ta fara shara Yana binta da kallo komai irin na mace, shi kansa daurewa yake yi gaba daya bai taba ganin namiji haka ba ko mata Maza ne kuwa,Jamilu Yana ta aikinsa sai da ya gyara ko Ina neat har toilet ya wanke Kal Kal,Naila a ranta tace ko a gida bana aiki Ashe dai na iya gashi Ina bautar kato,naki yiwa uwata da ubana nazo Ina yi a banza.

Tana gamawa ta tattaro kayansa kala hudu duk ya cire ta shiga toilet taci ubansu da wanki sabo da tasan tsaftarsa da iyayi amma duk da haka ta fito zata shanya yace kawo na gani,ya duba kayan kafar wando da su aljihu ya kare musu kallo yace basu fita ba a sake,Naila ta gaji Dan ma kana nan kaya ne haka ta koma ta sake wankewa,ta fito yace Jamilu da ka Dan sake wankewa Banga sunyi haske sosai ba,Naila tace ni baiwarka ce wlh bazan sake ba ta fice ta shanya ta leko tace idan kaga dama ka saka idan baka dama ba ka barshi ta juya tayi ficewarta, Spark ya jinjina Kai yace ba komai gidan yari ce ta jawo min shi yasa yake ganin ni sa'ansa ne yaron da baifi na dauke shi ya zama cleaner dina ba,rayuwa kenan, shi Spark a dole anci Masa mutunci,yace kwana nan zan daina dariya ya daina ganin hakorina,ya dinga jinjina maganar yanda Jamilu ya wani zazzaro Masa Ido Yana Masa fitsara,ya nuna kansa yace niii...hmmmm ba komai.

Beauty tun jiya take so taji Muryar Jamilu amma shuru,duk ta damu kanta ga number waya ta bashi yaki kira,Naila kuwa Yar kwakwurar wayarta ta sa ta kira Beauty Wanda ita ta zaci wayar da tasa babanta ya bawa Jamilu ne,bayan sun gaisa tace to ya kaji wayar? Jamilu yace wani dadi idan Ina shafa Saman screen sai naji suwal suwal gaskiya wayar ta hadu na zama babban yaro,kinji yanda nake Jin muryarki kuwa clear wani so smooth,sai naji zuciyata tace aaa...aff idan muryarki ta daki dodon kunnena, Beauty harda dariyar farin ciki tace daga Jin muryarka my love nasan Kaci kaji jiya anzo Maka da kaji ko daga gida? Naila tace harda ragadada, Beauty tace sai watarana zan baka labarina, Tantiriya tace karki damu nima zan Baki nawa, to ya soyayyata? Beauty tace tana kashe Murya da yanga ta furta tana nan mana sai karuwa ma da take kullum, percentage nawa? ta kusa cikewa 100, Tantiriya tace har naji dadi kin san Ina sonki da yawa,Gashi baki taba ganina ba,Beauty tace duk a suffar da na ganka zan iya aurenka ko kuturu ne, Tantiriya tace da yatsuna ma kwantar da hankalinki,in kika ganni zaki ji dadi fa,Beauty tace muyi Whatsapp mana sai naga pics dinka,Naila Ido ta zaro tace yanzu Ina da wani uzuri ki bari zan miki magana,Beauty ta furta angama ogana my man.

Watace tazo wajen Beauty ana kiranta da chikar gayu, yarinya ce matashiya domin su Naila sun girmeta baza ta wuce 18yrs ba, ita ba fara ba Kuma baza ace baka bace amma tana da kyau matukar gaske,dumimi da ita da gudu ta shigo ta daki Beauty a gadon baya ta fice da gudu,Beauty bayan ta kashe wayarta ta mike ta biyo Chikar gayu da gudu,wata dattijuwa ce me kudin gaske wacce ita ba a block din Yan daurin rai da rai take ba,shekaru biyar aka yanke mata saura baifi wata biyu ba wa'adinta ya cika ta bar gidan gaba daya,Itama a VIP take me kudin gaske ce ita Chikar gayu ce Yar aikinta ta zama kamar yarta,Bata Jin magana tsokana ce da ita tun Yan gidan suna dukanta har sun daina ma.
Dattijuwar me suna Hajiya Kaltume itace ta rike Beauty tace dan Allah kyale min yarinya bakya ganin ita yarinya ce kin bata shekaru biyu haba Beauty tamu,Beauty tace wlh Dan Ina ganin girmanki ne Hajiya ba komai na kyaleta,tace na gode Queen of Beauties,Beauty taji dadi tace Allah Hajiya na Kai queen? tace ae mana,Zan iya birge mijina? Hajiya tace sosai ma ai bazai iya Kara miki kishiya ba,tace sunansa Jamilu,Hajiya tace Nice name,Ina sonsa Yana Sona,jiya ma da ban ji muryarsa ba sai da nayi kuka,Hajiya ta zaro ido tace kibi soyayya a hankali Yar Nan,Beauty tace ni wlh bazan bita a hankali ba akan Jamilu sai dai a mutu,Hajiya tayi dariyar manya tace uhm uhm fa Beauty kar muzo muga ana tsinewa Jamilu muga ana rusa kuka,Beauty tayi dariya tace Allah ya tsareni da zagin Jamilu har abada,wallahi da zanga malamai ma sai nasa sun mana addua Allah ya Kara mana dankon soyayya da Jamilu.

Hajiya tace lallai kinyi nisa baki San iskancin soyayya ba idan ta tashi maganinki,Beauty tace ki mana addua kawai Hajiya amma idan Allah yasa muka fita daga gidan yari zamuyi aure Jamilu zaiga soyayya a karuwata zan shiga gidan mijina ba kunya ba komai sai abinda Jamilu ke so,Hajiya tace Allah ya nuna mana tace Ameen,kina Jin labarin nayi aure idan kika ganni Hajiya kawai ki kirani da Karuwa, ai zansa Daddyna ya bibiyar min hakkin Jamilu shima sharri aka Masa, Daddyna me kudi ne Kuma Kinga Yana da kafa gashi Senator ne har sau uku yayi senator yayi minister na tsaro da wasu mukamai duk ya rike,Hajiya tace mashaallah,Beauty tace Babana Yana da Dabban kudi,wani jahilin kudi ne dashi,Hajiya mutuniyar kirki tace mashaallah Allah ya Ida nufi.

Ameen cewar Beauty,Chikar gayu ce tazo ta wuce da littafanta zata je Islamiyya,Beauty tace zan kamaki a school ne yanzu zanzo nima,Chikar gayu tace wooo ta zaro harshe ta Kara gaba,Bangaren mata ma haka yake gasu nan ba kalar da babu manya da yara,ga Yan iska Nan tatattun gaske da Wanda kaddara ta kawo su,iya shege kala kala wani bangaren ma kida suke ji a Bluetooth speaker suna ta faman tikar rawa ta fitsara,duk a nan su Beauty suma suka sake wayewa idonsu ya bude suka zama basu da kunya basa shayin uban kowa.

Makaranta Beauty taje ta samu Yan mata suna girgiza wai ana gasar girgiza Boobs aga wace tafi iyawa sai shewa suke a class,Malama bata shugo ba a Islamiyya suke wannan iskancin,Chikar gayu da nata ko girman kirki babu amma tafi kowa zakewa kamar zata cire Kafadunta, Beauty tana zuwa ta ajiye Jakarta ta shiga ciki tace ga rawar Jamilu,haka zan na masa a Palo idan munyi aure,guda suka saki da shewa ana dariya,Chikar gayu tace saura luwaluwai muga wace gwana anji Beauty ta lashe gasar, Nan ma suka fara har malama tazo suna ta fama sai da ta musu magana sannan suka San tazo ma.

Abban su Mohsin Yana bencinsa a zaune Yana ciniki sai ga wata bazawara ana ce mata Zainab Kai zaka rantse Bata taba aure ba ta dau wankan yan birni tana taku dai dai,tunda ta taho yake kallonta sai kace Dan iska, Zainab tana zuwa yace Zainabu Abu me tagwayen suna Allah ya kawo miji na gari ko da kuwa nine,Zainab tayi dariya dama har gulmarsa suke a layin yanda yake Mayen mata ba uwar da ya iya sai son mata,tace kayan Miya za a bani,Abba Yana washe baki yace kice yau dadi za a ci naga gidanku kunfi dafa shinkafa da wake,Zainab a ranta tace kaji mutum marar mutunci ya fada min magana a wayance,a fili tace ae a zuba min na Dari biyar, ai kuwa ya dinga antaya mata kayan Miya Yana kallonta ba ledar yake kallo bama Zainab din yake kallo Yana ta faman zubawa ya bata yafi na dubu daya,hannunsa sai rawa yake karrrrr karrrr, Zainab ta karbe kayan Miya,yace cucumber fa ga salat ai girkin zaifi dadin ci,tace kudina sun Kare,hannu na rawa yace ai sai a baki ko kyauta ne zo ki karba haba kamarki ai sai da kayan lambu, ya dakko hannu na rawa zai zuba a leda sai ga Umma ashe tana labe tana kallonsa ta cikin gida ta fito fit....
Chapter 28 · 0% Book details