← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 98

Sashe 77

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Goggo tace ke dai bari kar Kiga gulmar Hashimu da akeyi ana Masa dariya tun yana yaro yau gashi Allah ya yarda, yaran Hashimu sai arziki suke yi ana ta Masa dariya ana kiransa da Dolo,Tani tace ai yafi Kubra hankali wlh ke ba Kubra ba kadai ba, da yawa yafi mutane ganewa ne ba a yi sabo da yana da shirme watarana amma Hashimu ba dolo Allah ya halitta ba,mutane dai kawai akwai su da son yiwa Allah shishigi a cikin lamarinsa,abin gulma da yi da mutum yanzu bashi da yawa, yanzu Gulma ce ke cinye ayyukan mutane na kwarai,kullum cikin hirar mutane ake,makwafta na gulma a junansu,Yan uwa na gulmar Dan uwa,ko Ina munafunci yayi yawa.

Baka ba mutum ci da Sha ka zauna kana gulmarsa,Kuma idan ance rashin aikin yi ne ai masu aikin ma yi suke,suna wajen sana'a suna gulmar mutane,Hashimu kuwa ba a gulmar wani da shi,ai Hashimu ko shugaban kasa kike zagi bazai goya miki baya ba,idan kika ce Abatcha yayi sata, haka zaki ji yace kin tabbatar? Zaki sheda a gaban Allah,idan kika ce a mulkin buhari anci wuya haka yake cewa ni ban ji ba, lafiya Lau nayi rayuwa ta a shekarar ma nafi samun kudi,idan kika ce Kai Obasanjo ya cuci kasar Nan,yace a'a ai baki fahimce shi bane, shi ya kawo mana wayar Cellular, shine ya wayar da yan Nigeria, shi akan Obasanjo ya waye,gashi ana ta social media kowa ya waye sai tambada iri iri, Goodluck Abba yace mugunta aka hada Masa aka dinga kashe mutane sai da aka sauke shi ta karfi,Allah yasa ma ya musulunta kowa ya huta da gulmar da akewa Goodluck.

Naila dariya tayi tace ai Abba yace shi ba ruwansa Yana Jin dadinsa a kasar nan tunda shi aka yo shi musulmi to ko iya haka ya gode,ba abinda zai dame shi,gashi da yaransa suna Masa komai me zai dame shi Allah sarki Abbanmu.

Goggo kallon gidan suka fita ko Ina lungu da sako suna furta hodi amma anyi asarar dukiya a nan,sai dare kusan 9pm sannan aka tattara su tare da Maida su gidan Mima,ba wulakanci suna Jin tsoron Goggo salin alin aka basu dakunan kwana da abinci,Goggo tace Kai ku kawo min yaji girkin ku salab ba gishiri,Tani tace ba a sa gishiri sai shegen Maggi har tsakar Kai,a bamu yaji mu dangwala da kazar ta fi shiga,haka aka basu yaji,Goggo tace Sanyi nake ji a gidan Nan,tiles zai kashe mu da Sanyi, a kawo shayi ruwan bunu banda Madara,na saba a Makkah kullum sai na Sha,Larabawa sun koya min mummunar al'ada,Me aiki aka sa ta kawo shayi ko wanne dakin suka sha abinsu,Mima tace jaraba sun sauka a gidana Kuma sai addua.
Badia tace ni Goggon Nan anya bata da bindiga a jikinta kuwa, Goggo kwanciya suka yi bayan sunci sun sha suna Hira,Tani tace Naila zata kwashi kashinta a hannu,Ina tausaya mata wlh,Goggo tace ai duk soyayya ta rufe mata Ido ta zaci ba komai,shi yasa ai na zugata nace ba zafi kar ta damu kanta, babu komai dankon kauna yake karawa,Tani tayi dariya tace Yar banza harda cewa to, na tabbata gobe ranga ranga zamu sameta,Allah yasa muje tayi kuka ni Kuma lokacin zan ci Ubanta dai dai gwargwado, ai rashin kunyar data nuna mana sai na wanke ta tasss,Allah ya kaimu gobe.

Naila kuwa su Goggo suna tafiya ta mikawa Chika hannu suka tafa,Chika tace saura ni Daya nima tafiya zanyi,Naila tace ki bari Spark ya shugo sai ki tafi zai sa a kaiki gidanku ke da su Basiru Kusa,Dariya suka yi tace saura bikin Basiru da Uwar raino,Naila tace abu namu,Chika tace naji kamar motar angon ma ta shugo,Naila tace shine gashi nan yana kirana a waya, dama yace Ina ganin kiransa to ya shugo gidan nan, Chika tace to dai karki bada mu,Banda kuka a saki jiki a sha love,Beauty tace ba zafi duk karya ce,Naila tace ai kin san nima a no wan carry last,to haka nake son ji,Naila tace Dan lelena fa Spark ah ai dole ma a ajiye tarihi.
Chika tana zugata tace sai tawan suka tafa tace bari na kira Abba na fada Masa an kaini gidan mijina,dama na fada Masa sanda muka shugo Abuja lafiya nace mun sauka lafiya,Umma wayarta bata shiga,Chika tace kina son Abban Nan naki da yawa,Naila tace ke ai fada ma bata baki ce, rayuwa ai sai da Abba,5 and 6 muke da Abbana,duk shirmenka Abba sai ya dauke shi, Abba baya nasiha a kaina ya fara kinji dai yanda ya dinga fada min gaskiya waye ma yayi min fada irin na Abba ko Umma Albarka wlh,sannan Sanda ta Ina sane da ita a gidan Mummy, Mohsin bai dauki gadonta ba,sai ranar karshe idan asiri ya tonu zan dakko ta,wannan Sandar me nasibi ce ko na mutu a binne ni da abata,Chika tace au Walakiri zaki ragewa hanya da Sanda kenan? Dadin ya dauka ya jibge ki,sai kace ta tsafi Yar iskar Sanda anki mantawa da ita,tace Dan Allah kije gobe ki dakko min abata, Spark bai san sandar nan ba haba ai na ma boye Masa sirrina,Chika tace sandar har wani sirri ne da ita wlh bazan dakko ba.

Abba ta kira a waya,bugu daya ya daga,yace Nailata,na'am Abba,yace to dazu Tani ta fada min komai gidan Ango sun jefar da maganganu ko? Naila tace a'a Abba kawai basu fahimta bane kasan Fulani da zuciya,Abba yace hakane, lafiya Lau aka yi komai a dakin ma fa Mima nayi bacci,kaga da akwai wani Abu ai da bazan hau gadonta ba,Abba yace hakane to koma sunyi ko basu yi ba karki fadawa kowa,ko mijinki karki fada Masa dama dole duk Inda aka Kai mace sai tayi hakuri sabo da zata ga canjin rayuwa ba wacce ta Saba da ita a gidansu ba,zata hadu da masu hali ko tarbiyya ko al'ada wata iri daban wacce bata Saba Gani ba.

Karki zama Hanan kullum Kai Kara,kiyi hakuri kowa hakuri yake da Inda ya tsinci kansa,dole zaki ga dabiun wani gidan da naku ba daya bane,Naila tace to,Yace yawwa yanzu kina Ina? Naila tace gani a kan gado na,to sai da safe, Naila Ummanku tayi bacci gata Nan Ina mata tausa wai ta gaji, Naila tace to bye ta kashe tana dariya tace Abba yanzu fa ya gama nasiha kai Abba nidai kar yaje ya Kuma yiwa Umma ciki wlh,nazo Ina da ciki uwata tana da shi ni wannan abin kunya ni Naila Ina zan Kai shi,daga tausa Kuma ba sai Kwalbewa ba ni dai Abba zai bada ni wlh.

Naila ta Kalli Chika tace kin San tsoro na yanzu shine kar ace maganin nan da kika sakawa Spark ya taba shi,sai yau na tuna wlh Kaka yace idan namiji jarababbe ne baya taba su sosai,idan ya sha zai dinga Jin sha'awarsa normal amma ana yin nisa da deep romance bazai iya komai ba zata kwanta,shine nake ta tunani ko Spark yana daga cikin irinsu,wlh abin ya dameni idonta ya ciko da kwalla tace na cuce shi yanda yake ta zumudi.

Chika tace karki damu ba dai kin taho da maganin matsalar a jakarki ba? Naila tace ae suna Nan,to idan kika ga ya gaza sai ki bashi ya Sha shike nan amma a boye zaki saka Masa ya shanye,Naila tace na yarda da maganin kaka babu karya a cikinsa wlh zai wahala Kiga baiyi tasiri ba,amma ba komai ai akwai maganin matsalar sai dai Yana da karfi kinga ba taba yi nayi ba kar yayi min warka warka na kusa mutuwa,Chika tace koma mene laifinki ne haka zaki karbi Hallare a duk yanda tazo.
Kece ai kika cuceni da kika zuba Masa yaci,ya zanyi ai dadin abin ma ance ba wani zafi,da sauki ko zanji wahala kadan ne.

Spark ne ya shugo ya Sha wanka new Shadda fara ba irin ta dazu ba,sai kamshi yake kawai,Naila ta Kalli Chika data mike tsaye tace ni waye zai kaini gida? Spark yace ga Misam can zai Maida ke ai nasan da zamanki Chikar gayu,sannu kin Sha aiki na miki Alkawari amma bazan fada miki ba sai na cika,amma ki sani za a miki bajinta,Chika tayi dariya tace na gode,Naila tace ni Kuma Amaryar fa? Yace ai ke sai dai ki min bajintar.

Chika tace Amarya sai gobe Kuma zanzo,Naila tace ni me zan baki ne? sai kin nutsu ai zan dawo gobe Chika ta fice da sauri,tana zuwa gaban motar Misam ta shige tace Ina yini,da kyar ya amsa mata tun daga lokacin bata sake Masa magana ba.

Har ya dauki hanya ga wata Babynsa tana jiransa a Hotel sai waya take buga Masa, yace mene number din Room din? Yana ta faman tsinka gudu a titi Yana sauri ya tafi shekewarsa,Chika tana ji yace 44 number din?

Wani kishi ne da taikaci ya lullube Chikar gayu,cikin masifa tace slow down malam,yace Ina ne gidan naku? tace I said ka Sauke ni a nan wlh,Mamaki ya kamashi yanda take bala'i da masifa,ba shiri ya gangare yayi parking ta bude mota tana tsaki tace kwarto,Manemin mata,tirrr da haihuwarka,motar ta balle ta fice ta sake lekowa ta zuro jikinta gaba daya ciki tare da kwada Masa Jakarta a kansa tace Dan Iska kwarto,Kansa ya dafe da Sauri kawai sai ya suma,Chika ta zaci wasa yake,tace Kai tashi dalla kwarto, ta fara jijjiga shi,Taga da gaske ne,ruwa ta dauka na roba a gaban motar ta fara yayyafa Masa tana girgiza shi cike da damuwa tana hawaye tace na shiga uku gidan yari zan koma.

A hankali ya farka kansa ya dafe sosai Yana Masa ciwo, Chika tace wayyo Alhmdllh Dan Allah kayi hakuri,koma sit din chan na kaika Inda zaka je mu rabu lfy,da kyar ya iya komawa Daya bangaren ta tuka motar da kanta,tace wanne hotel? Ya fada mata Yana dafe Kai yace kiyi sauri maganina Yana can,Chika taja a tamanin ba wani kwarewa tayi ba amma giggiwa irin tasu ita da Naila basa tsoro.
Chapter 77 · 0% Book details