Sashe 16
Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gashi Umma ta Hana kowa zuwa kotu har sai da Alkali ya bukaci ganin iyayen Naila sannan ala dole yau za ayi zama na biyu a kotu shine Umma,Abba da Mohsin suka halarci kotu,ana jiransu ana cewa zasu shugo aka yi yuuuu dangin Mummy da na mamaci mijin Mummy suka zuba musu Ido,ga sojoji a kotu da kaki duk a layin Mummy suke tun a Nan Mohsin a ransa yace Nailansa baza ta kubuta ba dole tayi prison,sai dai ko nan gaba Allah yayi ikonsa.
Naila tana tsaye a cikin Inda Wanda ake tambaya ke tsaiwa ta Kalli Umma suka hada Ido,Umma kuka ya taho mata tayi sauri ta dauke kanta sabo da uwa ai dole uwa ce,Abba kuwa tuni Yana ta sharbar kukansa dama kadan yake jira,Mohsin ne ya Kalli Naila tana Nan da riga da wandonta na Maza,suka ga ta koma namiji ko hular babu a kanta an cire a Inda take tsare, dama Tagwadas ta fada musu komai tace su rufa mata asiri kar kotu ta sake ganowa macece tayi shigar Maza Naila baza ta tsira ba za ace lallai tayi kisan me yasa tayi shigar Maza.
Naila Mohsin ta kalla idonta ya ciko da kwalla ta shanye kukanta sai hannu ta dagawa Mohsin tana murmushin karfin hali, an hana magana ba dalili amma sai ji aka yi tace Yaya Sandata itace gadonka tana gidan munafukar nan wacce ta min sharri,magana alkali yayi ko kulashi bata yi ba tace Yaya ka tabbatar ka dakko sandar nan tana dakin da aka bani ka rike ka dinga tunawa dani kafin na dawo,Abba ka daina kuka zan dawo fa Inshaallah verysoon ana yanke daurin rai da rai Banda ni ban aikata ba Allah zai fitar dani ko Bada sanadin kowa ba,ka rubuta ka ajiye kamar na fito,ku daina wani damuwa ni jajirtaccen namiji ne, zuciyata da karfinta zan iya da gidan yari ko sojoji ne a ciki fitowa zanyi bare wasu gandrobobi,Ni Jamilu na fada muku ko ta Yaya sai na fito Dan bakin ciki sai dai ya mutu ta Kalli alkali ta karasa da gwalo tana Masa gwalo .
Naila tana ta masifa a kotu ko alkali shuru yayi Yana kallo wani abin ma dariya Jamilu yake bashi sai ya ganshi kamar mace in yana wani abin,ta Kalli su Misam da sauran matasan kyawawa kamar su suka yi kansu ga kudi,tace kartan banza kartan wofi kunyi kunyi kyawun banza banza,sojanku bai da amfani tunda baku da CCTV, baku iya kama me laifi a family dinku kunyi asara,Kuma wallahi idan na fito a kanku zan dira duk sai na fanshe wahalata ta gidan yari,haka kawai ko uwata bana yiwa aiki zaku sani bautar iska a gidan yari,ta Nuna Mummy tace kanki kika cuta,naji ana ta zancen wani Dan iskan danki a nan wai Ashraf ku fada Masa sakona kafin na fito ya saurari zuwana gare shi har ta kansa zan bi,gwara da naji kinfi sonsa zaku ga tsiya,Naila bata San Spark ake cewa Ashraf ba,bata ji sunce Spark ba gashi baya kasar ma amma ta dauki Karan tsana ta dora Masa tace a kansa zata huce.
Mutane suna ta kunshe dariyarsu,Alkali kuwa sai da ya Dara a wajen,Sabo da ba wata hujja Naila bata da hujja yaso ya kubutar da Jamilu amma rashin hujja shine sannan yaji kudi ta wajen Mummy ta antaya Masa kudade, Kuma ba kotu ce ta musulunci ba bare yace suyi rantsuwa.
Lauyan Mummy daga ya tambayi Naila Abu sai tace ae hakane nayi, in ta gaji da tambayoyi tace na gaji ni ku yanke min hukunci na tafi na huta anbi an isheni, Duk da haka ba a yanke hukunci ba sai da Alkali ya dake sharia yace sai an sai an sake zurfafa bincike,Nan ma Mummy ta saki kudi ta karkashin kasa.
A zama na uku binciken gawar tun kafin a binne
Gawar da aka auna an tabbatar guba Alhaji yaci ya mutu,sannan an dakko jakar Naila an kawo kotu an tattara maganin gargajiyarta an Kai an auna suma suna dauke da sinadarin guba Kuma irin wacce Alhaji yaci ya mutu,Mummy sai murna take tasan kulla kullar da tayi,babu yanda za ayi da Naila dole hukunci ya hau kanta,ita ta matsu ma a yanke mata hukunci ta huta da tsareta da akeyi cikin Wanda ake zargi sannan tsoro take ji kar a gano ita din macece, dole Alkali ya yanke mata daurinta na rai da rai a gidan yari yace kamar yanda ka furta in kana da gaskiya Allah zai fitar Da kai kayi lafazi me kyau kana da tauhidi Jamilu.
Naila tace oho Kuma dai nidai bazan ga mutuncinka ba tunda ka kare sharia da wuri ba wani bincike,a wannan na karshen Mohsin ne yazo kotu kawai shi kadai,baiyi kuka ba,Naila ta kalle shi tace karka yi min Kuka ni ai zaka dinga zuwa ziyara, ni Namiji ne me dauriya, Ma'aikatan ne suka tasa keyar Naila wato Jamilu gaba,Zasu wuce ta gefen Mohsin ta dafa shi tace sai kazo ziyara ranar akwai shoki wlh, Yaya ba komai karka damu....karka damu Yaya.....zan rike kaina, a haka aka wuce da ita Jikin kowa a sanyaye,babu Wanda baiji Tausayin Jamilu ba,Shariar Sam da ganin yanda aka yita kasan alkalai da lauyoyi sun Sha kudi,kowa Yana da kokonton ba Jamilu ne ya aikata ba da alamar tambaya kawai babu mafita ne,ga Mummy ta iya kulla kullar tsiya.
Mohsin ya fito zai hau lifan dinsa Yana goge kwallarsa da handkerchief Misam ya dafa shi ya tsaya,hannu ya mika Masa suka gaisa,yace karku damu ku bari danta ya dawo ya iya kwatowa mutane hakkinsu Yana da tausayi na tabbatar da Yana kasar wannan abin bazai faru ba baza a kulle Jamilu ba, Mohsin yace kaddara ce ba damuwa,bani number Dinka sabo da duk halin da ake ciki gaba zaka ji,Mohsin ya bashi number suka yi Exchange sannan kowa ya tafi,su suka bi jirgi suka koma Abuja,Mohsin yayi gida.
Yana shiga gida ya iske Umma tana ta kuka a Palo tana cewa duk rashin Jin Naila ne ya jawo gashi Nan nasan ma an yanke mata hukunci,Mohsin yace ai kuwa sai dai ayi mata addua,wlh ba Wanda zaije mata ziyara da wuri tunda taurin Kaine da ita taurin kanta ya ja mata,Abba Yana zaune ya zuba tagumi Yan gida sunyi jugum jugum ana ta zuwa musu jaje,Matar Mohsin tana zaune a gidan da yarta ko a jikinta ita a ranta ma Allah ya Kara takeyi ta tsani Naila,Hajiya Tagwadas itama tana gidan wajen Umma harda zazzabi tace jarabar kwadayi na ne ya kaini, gashi ta hannuna abin ya biyo wayyo ni Tagwadas Ina zan sa kaina,Mohsin ficewa yayi kawai ya tafi gida.
Spark bai San komai ba sai da yau Allah yasa ya kira Kamal,Kamal ya haushi da bala'i yace wallahi abinda kake yi ba tsari bai dace ba,sai ka bar me kake yi ka dawo Nigeria Mijin Mummy Dinka ya rasu,kamar saukar tsawa haka Spark yaji maganar, yace me ya same shi? sai da cuta ake mutuwa magana baza ta yuwu a waya ba malam kawai ka dawo kasar sai kaji komai.
Spark kashe wayarsa yayi ya kira Mummy tana kallo taki dagawa tayi fushi da shi,kiran duniya taki dagawa,Mima ya kira duk suka ki dagawa,kowa ya kira a family bazai daga ba,sabo da ya batawa mutane rai,a ranar da yamma ya tattara ya sauka a Nigeria, Kamal yaje ya dakko shi a Airport suna tafiya Yana bashi labarin komai tiryan tiryan har ya gama Jin komai da ya faru,yace wannan yaron karya mummy ta masa,ai shi yasa aka so kana gari time din cewar Kamal.
Spark ya furta yanzu Yaron life in prison? Wlh baka ganshi ba son kowa kin Wanda ya rasa kyau dai a wajensa har da na siyarwa wlh kamar mace mace,tsaki Spark yaja yace ana zancen hankali sai ka kawo shirme, bari zanbi a hankali Inshaallah wannan yaron bazai yi life in prison ba,idan Mummy ce ta aikata gwara ita tayi zaman gidan yarin.
Naji mutuwar nan sabo da mijin Mummy shi yace na daina Masa magana,na biye Masa sai watarana kawai nake Masa sannu amma baya amsa min ban so Hakan ba bro gashi ya wuce,ban kyauta ba,Kamal yace shi yasa aka ce a dinga hakuri da rayuwar duniya yanzu gashi nan ai ya mutu,idan ance ka canja hali Kai a'a.
Ya isheka Kamal a cikin zafin mutuwa nake karka dameni cewar Spark,mutumin nan sai na bi Masa hakkinsa,Allah sarki rayuwa,Kamal yace watarana mutuwar kanmu zata zo,a fusace Spark yace kanka dai Banda ni,yaushe nazo duniyar ni yaro Dani,Kamal ya dinga dariya yace ake dauke jariri ma karewar rashin dadewa a duniya,Ashraf yace to na ebo shekaru da yawa inshaallah
A haka suka karasa gidan Mummy.
Labarin abinda ya faru kenan Naila ta tsinci kanta a gidan Yari bangaren Maza.
Ci gaban labari.
Free page
Masu bukatar siya 300
0175487861
Asmau Garba Muhammad Gtbank
Katin MTN
08061929616
Yan Niger ga number ku nemi wannan
+227 90 79 59 39
Sharhi please
AsmaBaffa
[12/5/2023, 2:05 PM] AsmaBaffa: 🏫 TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI
16-20
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA
GARE KI❤️
AIDA MAMAN TASNIM
Page naku ne
Najida Aliyu Bicca
Mhiz Awwal