Sashe 24
Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hirarsu suka ci gaba da yi Naila tace Abba ya kasuwa ashe an koma kasuwa,yace kasuwa Alhmdllh Ina can Ina ta yin araha,ai kowa araha nake Masa, Naila dariya ta kamata wai Yana can Yana ta Araha,Naila tace Abba kace duk masu abincin siyarwan nan na layin...kafin ta karasa yace duk a wajena suke siyen kayan Miya,zawarawa da matan aure harda Yan mata layi suke min ni kuwa inyi ta musu araha,Umma ta kalle shi tare da galla Masa harara,tace kamar Wanda yayi abin arziki bayan duk dakko kayan Miya sai an cika Masa kudin jarin ya karye,Naila tayi dariya tace Abba Debora me yin Sakwara itama nan take zuwa? Yace ae rannan ma kyauta na bata,Harira kuwa me shinkafa da Miya jiya tace min tunda ta fara siyan kayan miya wajena miyarta yawanta ya karu, tace riba take ci sosai shi yasa kullum a wajena take siya,Mohsin yayi dariya a boye Dan kuwa Su Harira sune suke cutar Abbansu Yana basu da yawa watarana ma shi yasa idan Yana free sai yaje ya zauna a wajen sannan ake cin Riba ko a tura Hidaya ta zauna ta siyar shi Kuma ya koma gida ya kwanta abinsa ko ya taya Umma girki.
Naila tace Inama Ina Nan Abba yanda kake son hutun Nan na karba na dinga siyar Maka kaje ka kwanta ka huta kawai tunda burinka kenan,Abba yace da kuwa na zama Dan Madara,Umma tayi dariya tace a ranta yazo dai ya dameni ba uwar da ya iya sai jaraba shi dai yaji dadi a rayuwarsa.
Suna surutunsu Naila tace ma'aikata ga nama Bismillah Kunga month yayi nisa ba albashi bare a ci a gida,yanzu da za aje shaguna duk list din Yan bashi idan aka dakko ma'aikatan gomnati ne a ciki,dariya suke yi kawai, sabo da suma ma'aikatan wasu duk lallaba Yan gidan yarin suke suna wasa da wasu,Wanda yayi rashin mutunci idan ya sake mutum Yana gidan yari zai bada umarni a bishi har gida a kashe shi,shi yasa sai da taka tsantsan, dariya suke yi indai Jamilu yazo waje sun ga ta kansu da bakaken magana.
Spark ya gama da su Kamal zasu tafi yace Mummy yaushe zata zo? Wai sai ta gama takaba tukun, yace Alright my regard to her ace na gode,suka tafi shi Kuma ya taho zai wuce ciki Naila ta riko rigarsa ya tsaya tare da Juyowa tace abokina ga iyayena da yayana My love,duk wulakancinsa sai tayi mamaki ganin ya rusuna ya gaida da Umma sosai,Ya gaida Abba da mutuntuwa sosai harda kakalo murmushi,Sannan ya mikawa Mohsin hannu yace sannu da zuwa Yaya,Mohsin zasu yi sa'anni da Spark suka gaisa,yace kaima kaddara ta fada Maka to Allah ya kubutar da ku,yace Ameen da ledar take away a hannunsa,muma lokaci yayi tafiya zamuyi an fara Maida mutane ciki,Spark yace yeah ai matan ciki za a fito dasu suma,Naila tace ai naso ganin Beauty amma ba dama, Spark ya faki Ido ya gallawa Jamilu harara.
Mohsin yace to Jamilu ku shiga ciki zamu wuce,Naila ta mike tare da daukan ledojinta, tace a gaida su Aslam da Hidaya,tayiwa Mohsin rada ka tabbatar yau baka bawa Yar iskar matakar ka ba Hallare,Kaine baka da garanti a rayuwa ayi mutum ba hakuri,wlh idan na fito sai na kashe Hallare ta daina komai kowa ya huta,dariya yayi yace munje wajen Kaka Affa,mun fada Masa halin da kike ciki Yana ta kuka wlh,Har maganin gargajiya ya bani shi yasa yanzu Hanan bata so nace ta tafi gidansu,Baki Naila ta rufe da hannu tana dariya tace Yaya kaima ka zama Tantiri,Umma tace Dan Allah Kai muje sai za a tafi zaku fara kus kus, Naila tace Umma ya bin kangon wajen masu gini? Umma tace na daina yanzu bana so na koma neman warin taba sigari,Abba yace Dan Allah muje sun fa daga mana kafa Kalli yanda ake Maida wasu ciki.
Sallama suka yi Naila ta tafi ciki tuni Spark yayi nisa har jiri yake yi na yunwa gashi daga nesa su Kamal suke basu taho Masa da abinci me nauyi ba,Yana komawa ciki ya tsaya Yana jiran Jamilu,Naila ta shugo da kayanta Niki Niki,wai wayo zai mata yace Jamilu zo muje part Dina muyi ciyayye kasan akwai Lada cin abinci da Yan uwa,ana so ko makwafta da abokai ka dinga fitowa da abinci kuna ci tare.
Naila tace Allah sarki ai shi yasa mutanen da suka fimu zumunci da kaunar juna to za a hadu a ci abinci tare muje,yayi mata wayo dake macece.
Spark yace a ransa Kai Jamilu ba wayo, suka shiga bangarensa sai da izininsa aka barta ta shiga ciki, palonsa suka zauna ta bude ledarta ta duba har kayan Maza an kawo mata harda pad a ciki a boye an sassaka a ljihun kayan pieces yanda baza a gani ba,tace ai sai Yaya Mohsin, harda hular Sanyi da hula p-cap yanda zata dinga rufe gashinta, da wani mayafin kamar na Maza tasan na sallah ne, ta samu kayan sawa har kala biyu ga vest ta mata me kalar ta Maza,haka boxers da panties dinta duk a boye Wanda mace na iya sawa haka namiji na iya sawa tasan aikin Mohsin ne.
Shi kuwa Spark Yana Ganinta ko ta kan kayan Bai bi ba kawai abincin yake so a bude yaci me gishiri da Maggi, Naila Jamilu ta bude abincinta na farko farfesun Naman rago Yana kamshi,Ga wata fried rice taji hadi,harda hadin salat daban da soyayyar kaza,gefe ga tuwon shinkafa miyar egusi, harda dambun nama da yawa daban,sai chinchin da meat pie, ga hadadden zobo Umma tayi da sanyinsa,Jamilu yace Kai gidan yari yayi ta wani bangaren,da a gidane yaushe za a kawo min wannan, da spoon na roba guda uku an zubo mata.
Spark sai kace abincinsa ya dauki Spoon yayi Bismillah ya ja kwanon Fried rice ya fara ci,yaji dadi yace mamanku Jamilu ta iya girki,Jamilu ma yasa spoon yace kaifa mamanku? yace tab Yan aiki suke girki ta manta yanda akeyi ba dadi nata, dariya ta kama Naila ta dinga kyalkyala dariya, Spark ya kalleta yaci gaba da cin abincinsa ba tare da ya kalleta ba yace Jamilu kasan kana kama da mace kuwa? Naila tace haka ake cewa ya na iya da halittar Allah,tunda nazo gidan Nan nake kallon kirjinka ko zanga Nono amma babu,Jamilu yace wato Ido kake sa min, fuska ya hade yayi shuru Yana cin abincinsa sai da ya cika cikinsa dam,tunda yazo gidan yarin sai yau ya koshi yaji dadin jikinsa, duk ya cinye shinkafar Naila kadan taci ya cinye mata,tuwon ta jawo zata ci ya kwace yace sai dare za a ci wannan, Jamilu ya tsaya Yana kallon ikon Allah yace ni da abincina zan fasa ciyayyen wlh kaji mutum,Yace baka isa ba sai mun dinga ciyayya daga yau Kaci abincina naci naka ya tura mata ledarsa yace gashi Nan cinye wannan ai dama ba aci nawa ba.
Naila ta bude ledarsa Taga tarin snacks da su yogurt,fresh milk da tarkace daban daban, ta zabi cake kato da yogurt taci ta koshi sannan tace kawo abincin na tafi da shi akwai Yan dakin mu,yace baza a basu ba kawai sai su cinye mana suma ai anzo musu Kai Jamilu bana son wannan Imanin naka,idan mutum ya fiye Imani baya iya taimakon wasu,Naila dariya ta kamata tace to kawo Naman a basu,yace ka basu farfesun mana mu sai mu ajiye soyayyen ko ya kace,Naila tace to Hakan yayi ta dauki farfesun da wasu cakes din da su lemuka Wanda aka kawowa Spark ta tafi da su dakinsu tana cewa sai dare zanzo muci tuwon yace to sai kazo,ka samo min Dan aiki a part dinku zai na min wanki da guga da shara zan dinga biyansa.
Naila tace gani aikin me nake ni indai zaka biyani zanyi,a ransa yaji Tausayin Jamilu Ashe shine Mummy dinsa ta yima sharri,amma bazan nuna nasan shi bane,wannan dalilin ne ma yasa har ya gaida iyayen Jamilu,baida burin yasa Jamilu aiki ya dinga wanke Masa kaya da shara a fili yace muguntar tayi yawa gashi ya yarda naci abincinsa wannan Jamilun akwai kirki,wai har Yan dakinsu zai bawa namansa, kwanciya yayi a Saman bed dinsa Yana ta sake saken rayuwarsa.
Naila kuwa tana zuwa dakinsu ta iske malaman sun hadu suna ta cin abincin da aka kawo musu duk cikinsu babu me binci da nama,daga shinkafa dafaduka sai shinkafa da wake,sai shinkafa da Miya da kifi sai Dan lemon su fanta,Jamilu Yana shiga suka ce Bismillah Malam Jamilu,Naila tace a'a kune malamai Kun taba ji nayi wa'azi a gidan Nan? Ba karantarwa ce ta kawoni ba kaddara ce wlh ba Wanda zan koyawa karatu ko na iya,Malam Sharu yace a daina biyewa rudun duniya Jamilu ka shigo makarantar mu, Naila tayi dariya sosai tace zan shugo,Naman ta ajiye musu tace gashi ta zube musu snacks da lemuka tace ga naku,suka yi ta mamaki Dan a jarabar Jamilu basuyi zaton zai kyauta ba,suka dauki yanka daya daya,Jamilu yace naku ne fa ku cinye wlh du ana tare taya zan cinye abu ni kadai,Malam sai murna da godiya yace Allahu Akbar.