← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 98

Sashe 61

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ya shirya ya fita Office cikin wani yard me masifar tsada,Kai da ganinsa ba sai an fada Maka ba Tan color,fuskar nan a hade ba fara'a yanda yake asalin Spark kowa ya kulashi sai masifa,Aikin ma ya kasa tsaki ya ja ya shiga Mota zai fita,manager yazo yace sir takardun nan zaka kawo,Spark yace karka dameni da wasu takardu ya ja tsaki ya yace da driver muje, gidan Mummy yaje,ta ganshi ransa a bace yau a spark dinsa yazo,tace kaga karka zo Inda nake bayan rashin mutuncin da kayi mana a gidanka, Spark Ido ya lumshe yace Mummy Ina Kwana? Ban sani ba ta bashi amsa.

Yace sorry Mummy daga nace zan afka miki shike nan sai ki dauki gaba dani ai idan aka tsine min nake nufi,yanzu Spark sai ka iya afka min? Spark yace idan aka tsine min ba mene bazan yi ba ai tsinuwa ce take aiki,yanzu sai ka aikata? Spark yace me zai hana kuwa,Spark ko wani ka ganni dashi Ina harkar banza da shi ai sai kayi min fada,yace Akan me? Kina Jin dadinki zan miki fada,ke da kika Raine ni Kuma kawai sai na miki fada sabo da kina neman Maza ba ruwan Spark kiji dadinki ai ko Mima ce ba abinda zance,iyakaci na dinga yawo da wandon karfe sabo da kar a biyo ta kaina.

Allah ya shiryeka yace Ameen wai Mummy ku mata ya kuke ne? Sai a rasa gane kanku sai kace masu Shan kwaya mata haka suke,Mummy tace an fara fada ne? dama wannan marar kunyar ai tukunna nama sai ka saketa da hannunka,nifa ba laifin data min kawai tambayarki nayi sabo da na San rirrin yanda zan zauna da abata lafiya,Mummy tace lallai baka da kunya,ka gama yi mana rashin mutunci a kanta yanzu kazo wai a fada Maka siririn mata, ta kasheka,share zancen yayi,tace ai baka Jin kunya Kai ka gama zaginmu shine kazo yanzu kana wani tambayata sirrin mata ya muke.

Yau da yamma Mummy ta dauki wanka sosai ta shiga motarta tana Jin kida sosai sai gidan Chikar gayu,tana zuwa ta hango gidan Malam wow tace Kai kai ya zama wajibi na shugo gidan Nan a matsayin mata,Chikar gayu tayiwa waya ta fada mata a bude gate,daya me gadin ne ya bude gate tayi parking sannan ta fito tana baza kamshi, Basiru kuwa ya saka Yar shaddarsa ta sallah Yana zaune a Palo ya hakimce Yana karkada kafa irin me kudin nan,Chika tace kayi fa aiki me kyau,yace za a ga aiki ai ki kwantar da hankalinki,aiki sai ma mun shiga dakin bacci, Mummy ce ta shugo Palo taga yaci kayan alatu sosai shugowa tayi ta zauna tare da furta wow ta zauna,Basiru Yana karkada kafa Yana wata gadara da kyar yake magana,yace barka da zuwa ya Kalli Chika yace my Watermelon Ashe yau bakuwa zakiyi Yana magana Yana kallon Mummy,Mummy ma kallonsa tayi kawai Basiru ya kashe mata Ido daya tare da daga mata gira,Mummy a ranta tace kaiii ya daga min girma murmushi ta saki,ya kwalawa Sheyi kira kamar wajensa bakuwar tazo yace a kawowa babbar bakuwa kayan motsa baki,Mikewa yayi harda zuwa ya rike hannun Chika Yana cewa Watermalone,Chika a sace ta fisge hannunta tare da gasa Masa harara tana ce Masa Banda wannan.

Amma Ina Basiru a ransa yace tab ai wlh ba a isa ba na fito a miji Kuma ace bazan taba komai ba an San hakane akace ayi film,Sama ya haura yace kizo Ina son ganinki harda masifa irin me gidan Nan.

Ba yanda Chika ta iya ta bishi sama tace da Mummy Ina zuwa,suna zuwa Sama a palon sama suka tsaya ya Bata rai yace wuce ciki,in wuce ciki in Maka uban me sadaki ka biya? Film kika ce za ayi ai ana kwanciya a Saman bed,ai Hausa film muke yi ba Nollywood ko American film ba cewar Chika,Basiru yace dama kin San ba Nollywood zamu yi ba kika bata min lokaci to wlh Baki isa ba ni Nollywood film zanyi sabo da haka wuce ciki muje.

Chika tace baka da hankali Basiru Hausa film muke yi na musulmai,Basiru yace ba komai ai Hausa ma suna Waka da rawa a ciki sai munyi rawa da Waka tunda hakane Kuma karki sa Bra kizo muyi girgiza,Chika tace ai ban taba sanin mahaukaci bane Kai sai yau na fika iskanci wlh ta ja tsaki ta juyo wajen Mummy ta barshi tsaye,yace wlh sai nayi Yaudara a film din sai na so kawar taki komai tsufanta.

Mummy ce tace wannan ne dama mijin naki? Chika tace ae,amma duk kudinsa yake saka shadda me araha haka,to ai wasu masu kudi idan kudi yakai kudi ba sa saka kaya masu tsada,Mummy tace wannan ma gara ne wlh karki sake ya dinga raina miki hankali Yana zaginki ki rama ki zagi iyayensa,haka Mummy ta zauna tana faman zuga Chikar gayu akan taci uban mijinta kar ta daga Masa kafa...

Chika harda hawayen karya tana fada mata yanda Basiru yake zaluntarta,Mummy tace shi yasa fa wasu matan suke kashe mazajensu wlh ni bana ganin laifinsu ma,ba ruwanka zaka huta ka shana kayi abinda kake so,Chika zama ta gyara tare da gyara wayarta tace kice yanzu haka ake yi?Sosai ai mata sun daina zama yanzu,Ina ma zan San Inda ake siyar da gubar Nan,Mummy tace zaki samu mana wata kawata tana siyarwa a sirru,Naila tace idan na gaji zan kawo kudina,Mummy tunawa tayi karta jawowa kanta sai tace ke naji yanzu bata siyarwa amma zan tambayar miki ko ta dawo tana siyarwa.

Basiru Yana Jin zata tafi ya fice ya rigata zuwa Jikin motar,Chika Bata hanashi ba,Mummy ya Gani tana Masa murmushi,yace bakuwar Alkhairi zaki tafi? Mummy tana wani fari da Idanuwa tace ae sai na sake dawowa,wani zuwan ni zan kawota da kaina,Mummy tace okay bari kaima na baka number ta ko gaisawa zamu dinga yi watarana,Basiru jiki na rawa ya dakko kwakwurar wayarsa yace Af na manta babbar wayata a bedroom,Kai ai wayarce babba sai ta dinga Maka nauyi a aljihu musamman iphone nauyi ne da su,Mummy tayi murmushi tana karanta Masa number bayan ya shigar tace ko Kai kadai ma zaka iya zuwa gidana ba kowa,yace kasurgumar bazawara ce ne haka? Mummy tace wlh sakin Allah ce ba sakin mutum ba mijina mutuwa yayi kaga kuwa ai sakin Allah ne,Basiru yace sorry sorry harda dafa Kafadar Mummy sorry Yana girgizawa da hannu,Wayancewa tayi tace bari mana Alhaji Basiru kar matarka kanwata ta Gani,yace ke rabu da ita hakuri nake dama da ita ba uwar da take min na soyayya,Mummy ta furta wasu matan sai hakuri wlh basu iya kula da miji ba musamman yaran Nan,Basiru yace habawa bari kedai Hajiya Ina Shan wahala a kasar Nan da kudinka da komai mace ta zame Maka masifa ni sakinta ma zanyi,Mummy tace a'a ka dai Kara hakuri ai gwara kayi mata kishiya tunda gidan kaga part part ne,Kin kawo shawara na gode sai na kawota,Mummy ta shiga mota tana kissima irin kudin da zata samu a hannun Alhaji Basiru.

Basiru ne ya dawo ciki yace Baby,Chika ta hade rai tace the End film ya kare,ko kwanciya bamuyi ba zaki ce ya kare? Chika tace ya kare gashi Nan rubutu akeyi na karshe dalla mallam kama gabanka bana son raini,tsayawa yayi zai sake magana Chika ta jawo takalminta me tsini ba shiri ya fice.
Shirye shirye tayi itama na tafiya Kano,washe gari ta wajen Mummy ta biya ta daki cikinta a haka ta samo address din Misam har Office dinsa tace bari na dawo daga Kano nasan ta Inda zan bullo Masa.

Naila tunda taje Kano ake Bata magungunan gyara da kudinta Kuma tana siyan wasu,Yau zasu je zance wajen budurwar Mohsin,Naila a waya ta kira Spark ya daga Yana fushi sabo da Bata taba kiransa ba idan ya kira ma sai taga dama take dagawa sannan idan ma ta daga baza tayi maganar kirki ba, daga gaisuwa shike nan,abin Yana yiwa Spark ciwo matuka,sai da kiran ya katse sannan ya kirata back ta dauka,tace Ina yini? Lfy Alhmdllh,dama unguwa zanje nace....sai kin dawo kawai ya kashe wayarsa,hankalinta ne ya tashi amma ta danne ta shirya ta zabo atamfa cikin kayan lefenta wata Indigo ta saka riga da skert kamar an aunata,tace wai Lefen Umma har akwati Sha shida aka kawo? Umma tace gashi kin Gani ai sun kashe kudi,tace to ki kwashi wasu mana a bawa su Hidaya da Zarah suma su Dinka,cikin shaddojin Kuma Abba ya dauka,Yaya Mohsin da Aslam,Umma tace wa yace miki haka akeyi? Ai Dan kiyi Masa kwalliya ya zuba miki,to ai dai ana kyauta ki zaba Hidaya da Zarah su zaba a bawa my love Mohsin da Abba ki duba sunyi yawa fa,shike nan zan fada musu an gode.

Mohsin ne yazo yace fito mu tafi mana,Naila ta fito da Jakarta da mayafi duk sababbi,Umma tace ki gyara mayafin Nan sosai bana son wannan iskancin na yaran zamani mace me aure ba a banbanceta da budurwa bai dace ba, wasu mazan suna tare su a hanya idan mace tayi shigar Kamala ba me tareta yace Yana so,amma yanzu mayafin da wasu matan auren ke yafawa ko budurwa sai taji kunyar fita da shi, Naila an zama matan aure cewar Hidaya tana kallonta,tace ai kuwa Hidaya baki ga sai Shining nake ba? Hidaya tace na gani ai,Naila tace to Hallare ce ta jawo shi yasa kika ganni haka,Hidaya kunya taji tace ke Aunty,Naila tace ah to Kuma baza a Fadi gaskiya ba sai a zauna ana boye boye kamar me bin Maza,Mohsin ne yace Dan Allah muje ko kunya bakya ji naga ranar da zaki hankali ki fara kunya Umma fa tana jinki sharewa takeyi,Naila tace to ai ta San harkar itama gashi nan ta siyo min kayan gyara.
Chapter 61 · 0% Book details