← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 98

Sashe 82

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Su Goggo dai sai da suka tabbatar an siyo magani sannan suka yi sallama da Naila zasu tafi gida Kuma,Naila ta bawa su Rayya powder da jambaki da sabulai na kwalliya cikin na lefe ta eba,ta bawa su Goggo ma suka ce baza su karba ba suje su kwashe mata kaya dama kawaye ake bawa kawai.
Rakasu tayi har mota suka tafi,daga can Spark yasa cikin cousin dinsa yace ya Maida su gida na Kano su kawayen Umma ne sun waye a sasu a jirgi zuwa Kano,su Kuma na riga sunfi kusa da Jos a sasu a na Jos ya rakasu har kauyensu sannan ya dawo,Yana murna zai samu kudi yayi yanda ake so kuwa.

Naila da kyar ta koma sama tayi wanka ta kalkale ko Ina a jikinta ta fito ta shirya a hankali ta saka atamfa half boubou wacce gaba yafi bayan tsayi da skirt,ba karamin kyau tayi ba,tayi daurin dankwalinta me kyau Wanda shima daurin koyo take faman yi kullum a waya iri iri,tana da basira shi yasa take iya nadawa kanta.
Tana shafa turare ya shugo bedroom din,Nan take ta koma kalar tausayi dan kar ma Spark ya ganta normal,abincin da Mummy ta kawo ya shugo musu da shi yasan fitar ma matsala ce a wajenta.

A baya idan ya Kalli Naila sai yaga tana Jin dadi amma yau sai yaga ta dauke Kai da sauri duk ta diriri ce ta fara soshe soshe kamar me kaikayin jiki,yace wai me nayi ne? Naila tace wa ta nuna kanta tace ni a'a ba abinda kayi,kalle ni to hannayenta ta hade waje daya ba tare da ta kalle shi ba tace to ni da na kalle ka Kuma sau nawa Kuma ko a prison ai na kalleka da yawa tayi dariyar dole Kuma duk Bata kallonsa sai kallan gefe da gefe take,hannayenta ya ruko a hankali,idon Naila ya ciko da kwalla,yace mene ne? Ko Kari kike so ne? Kai yanzu idan nace ka Kara sai ka Kara yi?

Wa yaki dadi da gudu ma zanzo,Naila shuru tayi tare da canja zancen tace ni dama gidanku ka kaini,gidan Mummy? gidanku na asali gidan Mima naga da yara kannen ku da yawa sai ka kaini yau ma na yini mu Saba da su sosai,Spark ya gano wayon Naila, yace ni ba gidanmu bane,ko ance miki ni gidanmu ne ban taba kwana ciki ba,to kira Chikar Gayu tazo ,tace baza ta zo ba sai yamma, Gani na isheki nima ai Chikin gayu ne idan ita Chikar gayu ce to ai nima Chikin gayu ne,zaki sa ma na kulle gidan gaba daya,shuru tayi ya dakko ta ya Maida ta gefen bed din suka zauna ya hada musu tea da kayan soye soyen a Baki yake bata har suka koshi,ya kwashe komai ya Kai kitchen masu aiki sunzo suna ta gyara gidan ko Ina, shine ya gyara bedroom din ya samu har ta fara bacci,tashinta yayi da kiss a baki,ture shi tayi da sauri tana harararsa, yace makwaftanmu sunzo gasu can sun Kai su biyar.

Naila jiki ba kuzari ta mike tace ya zanyi yanzu tafiyar ma da kyar nake yi kana gani ga mutane kowa ya gani sai ya gane sabo da Allah wannan abin kunya Ina zan kaishi,Spark yace ni tafiyar ma birgeni take yi wlh sai naji kamar sake yi nake yi,taso na dauke ki,Zasu ce bamu da kunya,ai gwara suce bamu da kunya akan a Ganki kamar wata Yar kaciya Kuma da gefe daya fa kike tafiya,Spark daukanta yayi cak ya fice da ita Yana mata rada a kunne,tana wutsil wutsil da kafafu,har Palo ya kawota ya ajiyeta a kujera sannan yace bata min lokaci zata yi na dakko muku ita,Yan layin ne dukkansu sun San Spark sabo da shi Spark duk Inda ya shiga ana zama da shi lfy duk Yana zuwa suna gaisawa da makwaftan sa,sabanin wasu suzo unguwa babu Wanda suke kulawa sabo da suna da shi,babu kyakyawar mu'amula da mutane,ba abinda zai faru na jaje mutum yaje ko na farin ciki yaje,ko Kuma Ta'aziyya,wani maigidan ma sai makwafcinsa ya rasu bai sani ba,baya kula kowa ya fita da sassafe ya dawo da dare bai ma San me ake ciki ba a unguwa,wani iyalan sa ma bazai bari suyi harka da kowa ba,wani abin kuma idan ya same ka kafin ma Dan uwanka yazo makwafcinka yayi Maka shi,shi yasa Spark Yana zuwa duk abinda ya faru har gudun muwa yana bayarwa komai kudin mutum.

Yaran layin indai yaga wasu ko bai sansu ba Yana basu kudin school sai yayi ta rabawa yara alawa da kudi,duk sun San Spark matan ma da basu sanshi ba sun San sunansa a baki.

Zama yayi a gefen Naila yace wannan duk makwaftan ki ne,Kinga Hajiya Babba,ga Aunty Maryam,Aunty Maijidda,wannan Ummu Salma,Kinga Aunty Naja'atu,Naila da fara'a ta gaishe su suka amsa tace Sunana Naila,suka ce kamar yanda ya fada miki makwaftanki ne mu da fatan watarana zaki kawo mana ziyara,Spark yace zan kawo ta ai gidan ko wacce,Hajiya Babba tace ai ka kyauta wannan shine zaman tare ai hakkin makwaftaka ne,ace sai dai talakawa suyi mu banda mu ai bai dace ba sabo da Allah ya rufawa kowa asiri,Naila haka duk langonta ta mike tana daidaita tafiyarta ta shiga kitchen.

Ruwa da lemo ta kawo musu sai kayan gara da aka yi mata dublan da Alkaki harda Chin chin ta kawo musu,tace Dan Allah kuci idan ma baku ci ba sai na zuba muku abinku a Leda,kadan suka ci suna hira,Hajiya Babba tace Amma Spark matar nan taka Yar Fulani ce ko? Spark yace sosai ma,tace ai naji maganarta gaba daya gata mashaallah kayi dace,harda cewa na gode cewar Spark.
Sun Dan jima sannan suka tafi,Naila tace gwara na zauna a palon kar wasu suzo,kafin ta rufe baki kuwa sai ga wasu makwaftan suma sun zo,suma Spark ya gabatar dasu basu Dade ba suka tafi,sai Kuma ga Yan uwan Spark Badia da Anam,sai wasu Yan matan su biyu suka zo,sai Arham,da Shahid suka zo gidan.

Badia tunda ta shugo take kallon gidan tana wani tabe baki,Naila tace sannunku da zuwa,iya mazan ne suka amsa da fara'a ba ruwansu amma su Badia ko amsawa basu yi ba,Badia tace Kai ku zauna mu da gidanmu suka zauna,Naila tunda Taga haka sai ta kama kanta suka gaisa da mazan kawai ta share su Badia,au mu baza ki gaishe mu ba? haba yara Kuna kannensa ni zan gaishe ku Yayanku nake aure fa.
Arham yace da gaskiyarki Aunty wlh karki gaishe su.

Spark ne ya sakko daga step ya daure fuska ba wasa ganin su Badia, System dinsa ya dakko ya sa a charge sannan ya dawo ya zauna ya jawo Naila ya dorata Saman cinyar sa,Arham yace Yaya Spark ya kalle shi babban yatsa ya dagawa Spark wai yayi dai dai,dariya Spark yayi yace yaro kayi biyayya ka samu aikin yi,Arham yace ai tun jiya nabi ma,Dan Allah ka bani kudi na siyi wani agogo da wando,Spark yace ai baka da matsala indai kabi Amarya ba wando ba har da rigar ma sai a siya Maka,Shahid yace gaskiya Yaya wlh ka iya zabe,Spark ya mika Masa hannu yace mu gaisa,Naila dariya tayi tayi derere Saman cinya tace Arham Dan shiga kitchen ka debo muku drinks nidai bazan tashi ba,ya shiga kuwa ya debo musu harda kayan gara din ya zubo musu,a hankali Naila ta zame ta koma Saman kujera,Badia taki ci tace sai kace mayya,Spark yace to da mece ke? Ai mayyar ce ke duk gidanmu ai kece kike kama da mayun,ai kece full definition na mayya,Anam tayi dariya,yace Ido kamar na kwado zaki zo ki min iskanci,ko baki San gidan wa kika zo bane.

Naila ce ta katse maganar tace ya ka bar System din a can? so nake tayi charge,tace okay tun safe muke baki ai,ni fa Chika bata zo ba har rana tayi,Spark fuskarsa ya dora a Saman kafadarta yace zata zo ne.
Spark kannensa ya kalla mata Wanda basu da aure yace kai kuyi Maza ku saka kuka kuce Papa ya muku aure akwai baiwa a cikinsa,Arham suna dariya suka ce Lallai Yaya ka fara canjawa baka taba fa shiga harkar mu amma gashi yau sanadin aure muna ta Hira harda dariya,yace ka taba ganin me Iyali shashasha? yanzu ko kanka na shafa sai kayi albarka yaro,har su Badia dariya ya basu,Da kuwa ni kaina bani da albarkar bare na shafawa wani yanzu kuwa yaro kayi kokari na sa ma albarka binka zata yi, sun Dade suna cin dariya Spark yayi aure ba zaman lafiya,suna komawa gida suka hau bawa Mima labari,wlh Yaya bashi da kunya har muka taho tana cinyarsa,Mima tace ku kuka Kai kanku ai ,Kuma ko me tace Mima wlh baya musu Inda kisan rakumi haka take jan sa cewar Badia,tace itama ashe irinsa ce tayi shuru har da gyara zama sai faman rada suke yi,Mima tace wannan anyi tambadaddiyar Amarya,ai zanje ne da kaina.
Chapter 82 · 0% Book details