← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 98

Sashe 9

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Naila radio ta kunna lokacin ana shiri da fulatanci dake ita tafi Jin ma fulatanci akan Hausa,tana ji suna hira da Abbansu,Umma kuwa takaicin Naila ya kamata da take zuga Abbansu akan Yana da kyau mata suna kallonsa zata jawo ya mata kishiya gajiya tayi da jinsu ta fito a fusace tace wallahi idan Baki daina zancen mata na kallonsa ba sai na tsine miki Yar banza marar tarbiyya banza Yar kauye,Naila tana bakin cikin da Yan uwa da iyaye suke kiranta da Yar kauye bayan su suka kaita kauyen riko aka bawa kakanta ita sannan tana ganin tafi kowa wayewa da iya wanka amma ana ce mata Yar kauye Jahila bayan ta fisu ilimin addini,idan turanci ne tana jinsa kamar ruwa sabo da tana da brain,tunda suke ce mata Yar kauye take ta kokarin gyarawa lallai sai ta zama Yar birni,Naila tace yaushe ne ake cika a zama cikakken Dan birni? Umma da sauri tace Shekara arba'in,Baki Naila ta bude tace lokacin na tsufa, birni bazan zama Yarka ba, sai nayi shekaru arba'in zan koma Yar birni to na fasa,tsaki Umma ta ja tace da Abba tashi Kai Kuma muje ka zauna kana zance da wata shashasha muje ka yanka min kubewar Miya ,sum sum ya Mike ya bita ciki Yana cewa akwai feraye kabewa ne a fere miki ko miyar kubewar dai zaki yi? Da gadara tace ae,yace to ki kawo sai a yanka miki,Umma wani tsaki ta ja tace sai anjima.

Su Hidaya ne suka dawo daga school Naila ta kalle su tace Yan makarantar bokoko,Hidaya tace Aunty Sannu,Naila tace karki sake kirana da wata Aunty munafuka so kike na tsufa da wuri,Umma ce ta sake fitowa tace ki kyale mun yayana kar ki takura min yara ai ya kamata ke cikin samarinki ma ki fitar a aurar dake,Naila tace wai Khalil Dan Yana zuwa wajena? Umma ai Baki ne wuluk wallahi ya bari sai na samu kudi na siya Masa man bleaching ya koma fari,Ina son fararen Maza sabo da haka dole ya koma fari in Yana so na idan business Dina ya kankama zan dinga siya Masa man bleaching Ina maintaining color dinsa na yarda,tsaki Umma tayi ta koma ciki tace girkin uban waye zai miki?Naila tace kin san wlh ni ban ma taba shiga kitchen ba Allah na tuba to Ina dakko kwano amma ban da shi ko ruwan zafi ban taba dafawa ba kawai abinda na sani shine a bani na ci, yaran naki su dafa miki tunda ni bakya sani a yaranki ta mike ta ficewarta.

Tana fita suka hadu da saurayinta Khaleel Baki ne wuluk amma Yana da kyau, Magana ya mata Naila,tsayawa tayi ba tare data juyo ba tace nace kaje ka koma fari,ga man bleaching Nan ka samu ka dinga shafawa,ni namiji farinsa ko na Mai ne Ina sonsa,Khalil yace Allah ya tsareni sai kace mace ko wani Dandaudu,Naila tace to karka sake kulani matukar baka fara bleaching ba, tayi tafiyarta gidan Hanan ta nufa wato gidan yayansu Mohsin, gidan da nisa tsakaninsu amma haka ta taka a kafa har gidan, kowa ya ganta a mutanen Kano ya zaci ba musulma bace irin aranan Fulani ne,shi yasa sai dai a kalleta ace gaskiya arniyar nan ta hadu Inama musulma ce,tunda taji haka suke fada,duk Inda ta wuce sai tace salamu Alaykum,wasu suce irin Yan Fulanin Daji ne da basa sallah, ga shegiyar Sanda ta kiwon shanu kullum a sakale a kafada har wani Mai ake shafawa sandar tana kyalli.

Da sandarta a wuya tayi sallama ta shiga gidan Mohsin suna zaune da matarsa Hanan a kujera doguwar suna kallo a plasma tv,Yar su Amal tana daki a kwance tana bacci,Naila tana shugowa ta tsaya a kofar palon tayi gyaran Murya Ehem Ehem na shugo?

Mohsin yace yanzu sai da kika zo dan masifa,Naila ta shiga a hankali,yace ki fitar min Yar iskar sandar nan taki sai kace namiji

Naila ta jingine sandar a kofar dakin daga ciki sannan taje ta zauna tace Mohsin ta Sha Mai idan na barta a waje kura zata yi akan kura ta shafi sandar can gwara ni kura ta haye jikina.

Hanan matar Mohsin ta Kalli Naila kawai ta wani watsar ita a rayuwa bata son dangin miji, tafi so daga ita sai mijinta Kuma tana bakin ciki Taga mijinta yayiwa danginsa alheri ko iyayensa bata kauna tafi so kawai daga ita sai danginta,Naila ko ta Hanan bata yi ba,Mohsin ya kalleta yace baki gaishe da Hanan ba

Naila da maganarta ta yan fulani tace ni Shanda na zo ta min ko shannu da zuwa ne? Ni ban taba zuwa gidanka ta min kallon Rahma ba Kuma ai kana gani, duk iskancin da mace kewa dangin miji to wlh mijin ke bada kofa,da ya jajirce akan Yan uwansa ba wata kafura data isa ta wani wulakanta Masa Yan uwa,amma ita su Umma ma bata kauna taga ka taimake su ko sun zo Nan,wlh duk Wanda baiga darajar iyayena ba nima bazan ga darajar sa da iyayensa ba,aikin banza aikin wofi mata an taimaka an auro ki,ki Kalli yayana kyakyawa kamar Dan India ke kuwa kamar Yar yare hanci kamar hannun kuturu ,Allah ne ya miki halittarki amma iskancinki yasa aka fada miki ki sani baki da kyau ehe maleji muke yi dake..

Aradu duk da a Daji na girma na fiki iya soyayya ni tunda naga Yaya Mohsin kafin yayi aure yafi kiba nasan baya Jin dadin auratayya,wlh sai mun miki kishiya ta kwace shi,kullum Yaya cikin gayu da kamshi ke kuwa wankan ma Baki iya ba Yar shagwabar ma da ake yiwa miji Yaya sai dai ya gani a gidan abokansa,wlh kika sawa yayan cuta Hallare dinsa ya daina motsi sai na kaiki Kara, Mohsin bai Jin fulfulden da Naila ke ji bai San mene Hallere ba fulatancinta da babanci Dana wasu yankin hasali ma su basu San komai da fulatancin ba ko wanne iri.

Mohsin yace Zanci ubanki mene Hallere? Naila ta cuno baki tace pole dinka I mean,your Jumbo,ai Mohsin ya Mike a fusace Naila ma ta mike ta fada bedroom ta sa key,yace zaki fito ne wlh yau sai na miki dukan tsiya a gidan nan sa'anki ne ni.

Hanan tace Abban Amal kana gani ta shigar min bedroom ai bai dace ba,Mohsin itama ya zuba mata harara yace ke danginki uban waye baya shiga dakinmu har kawaye kaisu kike idan zakuyi gulma,rannan kaninki Khalifa namiji katon gardi ya isa aure na ganshi a ciki Kuna Hira,ni da gida na sannan Dan kanwata ta shiga shine zaki ce ta shigar miki bedroom sannu me daki, duk abinda kike yiwa Yan uwana Ina kallonki kyaleki nake yi,me yasa kuke haka a rayuwa miji baya wulakanta muku dangi da iyaye amma ku burunku wasunku da yawa ku wulakanta nasa haka ake rayuwa wannan ai jahilci ne da kauyenci,yarinya ta shugo sai da na fara kallon fuskarki kina wani yi mata kallon banza kina harararta taya zata gaishe ki tunda kin zubar da girmanki,babu kawo mata ko ruwa, su shiga kitchen kice zasu lalata miki kaya,Hidaya ba bautar da bata miki ba sanda kina laulayi da kika haihu haka ta dawo gidan nan komai itace take miki amma karshe yanzu in tazo kallon arziki baki mata sabo da ke baki san arziki ba,shame on you.

Hanan kuka ta fashe da shi da karfi Wanda sai da ta tashi Amal daga bacci tace makira annamimiya tazo gidan Nan ta hadani fada da mijina shegiyar Yar kauye,Yar daji munafuka gantalalliya, look karki sake kiran kanwata da gantalalliya shegiya cewar Mohsin,
Na zage ta shegiya gantalalliya Yar kauye munafuk....kafin ta rufe baki taji Mari ta ko Ina,sautin kukanta Hanan ta Kara da ihu.

Naila dake daki tana ji dariya take tana tsalle akan gadon Mohsin tace nice wakiliyarka shedan basai kazo ba jeka abinka je kayi soyayya da matarka Iblis na karbi aikin a hannuna,ka bar min wuka da nama,auren Nan zan raba shi karka damu shedan, kasan ni ba irinku bace iska kullum bazai yuwu Ina nan ba wannan nacin naku bazan iya ba Iblis Allah ya sake la'antarka amma daga yau na kulla zuwa gidan nan ko yaushe Ina tayaka aiki karka damu,kana ganin nazo kawai kayi tafiyarka wani uzurin.

Sai da ta gama surutunta ta dawo bakin kofa tace gidan Yayanmu ne gidanmu ne ehe ba a isa a hanamu shakatawa ba Yar gidan Sule dan koli, Mohsin yace ke nake jira kema ki fito wlh tun kafin na balle kofar nan, Naila tace yo ni nace babanta ya dinga siyar da kayan koli, anan zan kwana yau sai dai ku koma dakin baki gashi Yar katifa ce a dakin Yar gidan Sule dan koli ba a mata kayan arziki ba,shegen gadon da suka kawo na zamanin baya na karfe me spring sai kace gadon gwauraye.

Mohsin yaja kwafa Naila taki bude kofa,Hanan ta gama kukanta har tayi shuru Dan kanta ta zauna sunci gaba da kallonsu ba Wanda ke kula wani,har magriba tayi Mohsin yaje masallaci ya dawo Naila bata bude kofar ba,bayan yayi Sallar Isha ya dawo,Hanan taki yin girki shi Kuma baya cin tazarce,yasan dama indai suka yi fada to gaba zata fara sai ta kwashe wata biyu tana gaba da shi, shi yasa da ya tashi dawowa ya taho da take away dinsa Kuma iya nasa shi kadai harda ruwan roba da lemo.
Chapter 9 · 0% Book details