← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 98

Sashe 57

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hanan ce ta shugo gidan hankalinta a tashe ko sallama babu tazo ta zauna tace Umma Ina yini,ko amsawa Bata bari anyi ba,tace zuwa nayi naji waye yace bana kula da mijina? ance magana daga Nan gidan ta fito?,Umma tace wato kureni kika zo kiyi kenan to an fada ko kina kula da shi ne,tsakani da Allah ni an sa min Ido an hanani sakewa a gidan mijina idan Banda mugayen mafarki ba abinda nake yi idan wani Abu ake min a gaskiya a daina domin idan aka cutar Dani baza mu yarda ba domin nima yace a wajen iyayena,Umma tace keee....Kutmar ...burar....Umma ta dinga zurawa Hanan ashar sannan tace bafa tsoronki akeyi ba,abinda yasa kika ga bansa ya sakeki ba Gani nayi ya macece ke kamar yanda nake mace,sannan baza ka raba yarinya da gidan Ubanta ba kazo ka saketa ba, baka yiwa iyayenta adalci ba tunda sun sauka sun baka yarsu,wannan dalilin yasa ban sa Mohsin ya sakeki ba,ke wlh a yau idan naga dama sai ya miki saki uku gwara ki rufawa kanki asiri,Abba yace aure ma zai Kara kowa ya huta,Kururuwa Hanan ta saki tace ai ke ba haka mijinki yake miki ba, ta juya ta bar gidan tana kuka tana tozartasu a layin ita uwar miji ta hanata sukuni da asiri.

Chikar gayu farko shiri tayi abinta ta sa kaya na mutunci masu kyau ta yafa mayafi a kanta irin Yar matashiyar matar aure mayafin kato,gidan Mummy taje tayi sallama a nutse,Mummy tana Palo ita Kadai tana kallo tana ci n popcorn,tunda Chikar gayu ta shiga Mummy take kallon karfarta da suturar Dake Jikin Chikar gayu, tana Gani a ranta tace ba laifi da Yar tsadarsu,tace shugo mana zauna,Chikar gayu ta zauna tare da Furta Aunty Ina yini,Mummy ta amsa da fara'a tace dama makwafciya ce ni Amarya ban Dade da zuwa layin ba nace bari na shugo mu dinga zumunci,Umma tasan layinsu gidajen masu kudine tace wow ai kuwa kin kyauta na gode,ta sa me aiki ta kawowa Chikar gayu kayan motsa baki Sannan tace wai Yan mata yanzu Ashe kin shugo cikin shahada kema,Chikar gayu tace me fa? Aure mana ai aure babu dadi a cikinsa mazan Nan basu da mutunci,Chikar gayu tace wlh Aunty kamar kin shiga raina ta matso hawayen karya tace tun Ina Amarya kwata kwata watana biyar da aure amma wai akan naki samun ciki shike Nan wai har zaiyi min kishiya,Mummy tace Laaaaaaaa ke tun da wuri gaskiya Baki karki ba ni Ina ganin sai da na kwashe Shekara talatin da aure mijina sannan yace zai min kishiya ai kuwa wlh nace ban yarda ba,ke yanzu mata kwayar yancin su suke,Chikar gayu tace ai kuwa nima nace wlh bazan yarda ba ko ni ko shi,daga aure akan kawai ban samu ciki ba,Mummy tace Dan banza watakil ma mataccen Sperm ne dashi yake tiltila miki a jiki,karki sake zai shafa miki ciwon mara,mata sun waye yanzu,kina ji ya matsa miki wlh kiba shege wuta ki bar Masa gida,Chikar gayu tace idan na tafi Ina zanje? ko Nan gidan kizo ai ni Ina so inga mace tana gasawa Maza Aya a hannu,Chikar gayu tace ai kuwa zai ga yanda ake tsiya.

Naila baccin karya tayi har yazo ya kwanta yace in zaki tashi ki tashi ni motsi kika yi nasan me yake nufi,Naila tayi mukus yace wa yace kisa riga tunda kika ji na dawo ai sai ki cire ko madam,wai dama Kai haka kake? Baza ki San haka nake ba sai munje wajen Umma da Yaya Mohsin wlh,nifa gaba daya haushinki nake ji,ni zaki canjawa kamanni,Kinsa zuciyata radadi,kin fito gidan yari amma ko ki nemeni sai ma harkarki da kika shiga,kin san halin Dana shiga? to yanzu ai ka samu Wahida ba shike nan ba,Kwafa yaja yace nine ma bani da zuciya Dana ke kulaki,to ya zaka yi Dani tunda kana kwadayina,ni kaga naje wajen hallarenka ko na taba ta,dariya Spark yayi yace wai Hallare.
9pm zamu tafi Kano a can zamu yini a can zan barki sai Nan da 2weeks za a dawo min Dake inji Umma,Yana magana Yana shafa albarkatun kirjinta,Naila ko magana daga an taba ta shike nan ta daina magana Kuma ta Lula wata duniyar.

A dinga sharhi aga posting

Masu Sharhi na gode

AsmaBaffa
[12/17/2023, 8:11 PM] AsmaBaffa: https://wa.link/49vn47

PAID GROUP ONLY

Accnt no
0175487861

Katin MTN
08061929616

Yan Niger
+22790795939

🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI

BOOK 1

61-65

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

Page naku ne

Meta force Business
Amina Maman Ibrahim
Shehuhassana
Hajjora Investment
Hajjafatty
Hasiya Muhammad

Hey lovelies

Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?

Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?

Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?

Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?

Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din

https://wa.link/49vn47

Bacci su Naila suka koma,lokacin Chikar gayu taje da safe ta shugo palon Mummy tace Aunty yau baza ki fita bane? Mummy Dake kitchen ta fito tace gaskiya ba Inda zanje,Chikar gayu tace key din gidana zan Baki ajiya zan fita wurin aiki idan na dawo na biyo na karba ta mikawa Mummy key ta Sha Abaya ta zuba kyau,Mummy ta karba tana tambayarta ya tsohon guntun mijin naki? Chikar gayu tace wannan ai in kina mutumin banza jarabar duniya to shi ai Alhaji Basiru mugun Dan duniya ne,Mummy tace au me kudi ne? Chikar gayu tace jahilin me kudi ne Yana da mata amma ita a kasar waje take rayuwa uwar gidansa, nice nake zaune a Nan Abuja,Mummy a ranta tace anya bazan aure mijin yarinyar nan ba kuwa,gashi tace matarsa har a kasar waje take rayuwa Kai bari na kokarta na raba yarinyar nan da gidan mijinta na huta ni na shige ciki,na gaji namiji nake bukata,Mummy tace yaushe zanzo gidan naki Ina so na kawo miki ziyara,Chikar gayu tace gobe ma Ina Nan kizo inshaallah tayiwa Mummy kwatancen gidan Daddy din Beauty Inda take zaune,Mummy tace ai muna da Nisa ma ke ai layinmu daban? Chikar gayu tace abinka da bakuwa ai na zaci duka street Daya ne,Mummy tace a'a ba daya bane Dan kawai ke bakuwa ce a Abuja,na gode da kika wayar min da Kai sai dai kinzo Allah ne ya hadamu shi yasa nazo Nan Ashe da rabon zaki bani kyawawan shawara,Idan kina tare Dani bake ba takaicin da namiji,Chikar gayu tace naga alama tana dariya ta mikawa Mummy hannu tace halina Dake kin San kan tsiya suka tafa kamar sa'arta,sai bayan sun tafa Mummy tace kaga yarinya kamar sa'ata.

Chika tace Ashe kuma sai naji danki yayi aure,Kun Sha biki Kuma lokacin bamu hadu ba wlh ban sani ba sai jiya naji ana cewa angon ma Ashe wacce ya aura daban naji ana ta labarin a gidan suna,Mummy tace Kai mutane da gulma suke yanzu wannan labarin har gidan Naming ceremony? Chika tace sosai ai kunyi fice a duniya sabo da Kuna da arziki,Mummy tace wlh fa ai arziki yayi,Chika ta sake cewa angon aka ce baya ma gari ya koma kasar waje,Mummy kiri kiri taki yarda ayi gulmar Danta Spark sabo da tana sonsa ita barta dai suyi shi da ita da Yan uwa amma bare bazai taba Jin kansu ba iya nacinsa,Chikar gayu ta dinga soko zancen Spark Mummy taki yarda ayi zancen sai ta waske,Sai da Chika tace naji ma ance Ashe ku ya rufe sabo da karku dame shi Yana gidansa shi da matarsa yau naji a wajen kawar matar tace ai sunje yayi fata fata da amarya sai da aka mata dinki sunje dubiya, Mummy tace to Ina ruwansu mene na zuwa dubiyar in banda sa Ido shi yasa kawaye suke da matsala Spark yaushe zai iya wani fatattaka mace mutumin da Bai taba yi ba yaushe ma yasan mace,da ace kaninsa kika ce Misam wlh zan yarda domin shine me neman mata,
Chikar gayu kamar an watsa mata ruwan zafi haka taji tace a ranta dama Dan iska ne kenan,tace ah nima ai ba wata ta gari bace sabo da haka Ina son kayana haka ni zan saita Masa Hallarensa wato checking balance tunda Bata da saiti kowa ma bi yake chab,Kasa hakura tayi tace na tafi Aunty ta fice..

Tana komawa gida Daya daga cikin me gadi Ana ce Masa Basiru Yana da kiba gashi Dan babba haka suna shiri da Chikar gayu sabo da Tantiri ne shima akwai iya shege,samunsa tayi tace zanyi bakuwa gobe kayi shiga me kyau a matsayin mijina Kaine me gidan Nan,Basiru yace wato dai film zamuyi motocin nan duk nawa ne da gidan? Chikar gayu tace ashe ka gane ta karanta Masa duk abinda zaiyi,Basiru yace gaskiya ke me kaunata ce, ya sake cewa na gode ai ko da wasa aka ce kayi acting a matsayin me gidan Nan to Wanda ya saka aikin Yana cikin me kaunarka,ace wannan motoci da gidan Nan duk nawane a Kuma wasan kwaikwayo ai na gode Kuma na fito a mijinki Haba Chika dadin ya min yawa tsakanina Dake sai addua,da ace cewa kika yi na fito a talaka to wlh da bani ba ke nasan bakya kaunata ko da wasa akace ka fito a talaka ai an cuceka,Chika tace Kai kuwa Basiru kamar an baka gidan kyauta irin wannan murna wasan kwaikwayo fa zamuyi Kuma biyanka zanyi,da sauri yace bama sai kin biya ba ni hakan ma na gode ai arziki ne ace ka fito a me kudi.
Chapter 57 · 0% Book details