← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 98

Sashe 15

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mummy sama ta haura abinta Naila ta baje a kujera kamar gidan ubanta harda kiran Yan aiki,wata tazo a ciki tace zubo min abinci ki hado da hantar kifi, Yar aiki tace babu hantar kifi,tace to hantar kaza fa? Babu itama,zabo? Babu hantar zabo?,Naila tace shima comon zabon abin banza? tace ae,tace to ta Dan maraki? Akace babu,tace ta rago fa? Yar aiki tace sai ta Sa gaskiya,Naila tace uhm uhm bana cin Naman Sa sabo da ai cin Amana nayi shanu dabbobinmu kawai sabo da cin Amana naci namansu Bada ni ba,Yar aiki tace sai kace me bautar saniya, a'a daga India nake Naila ta furta da Muryar maza,Uhmm me zan kawo yanzu? Nasan ma babu Koko kawo min abinda kuka dafa banda shayi.

Naila dai tana gida har kwana uku suna shiri da Mummy sabo da maganin da Naila ta bata,Kuma mijinta ya fara sakkowa sun ma kusa shiryawa gaba daya shi yasa yau Mummy zata Masa girki da magani,taci gyaran jiki sosai za a angwance,yau wankan data dauka ma na musamman ne, Naila tana kallonta sai shanawa take a gidan masu hanu da shuni har yanzu Kuma bata ga wani namiji yazo gidan ba basu je gidan sojojin ba,ta dai kira Mohsin ta fada Masa komai normal.

Mummy Dan faten wake da doya tayima Alhajinta yaji kifi,Yana son kifi iya cikinsa yanda Naila tace haka tayi,part dinsa ta nufa ta Kai Masa yace zo Halima,ta koma zata zauna ya jawota jikinsa yace Hali dubu tawa ko kefa ai gwara da kika hakura nayi auren mene aciki kece fa ta gaban goshi,wallahi ba wacce zan so sama da ke a duniya,Mummy tace uhm ta kakalo murmushin dole tayi dai tace ci abincinka ko na baka a baki,yace da zan fi son Hakan,ta dauki spoon ta fara bashi a hankali Yana ci,har ya kusa cinyewa bai sani ba sabo da dadi sai da ya cinye tas sannan ya Sha ruwa sosai,har zai kwanta yace naji na gaji ne sai ya dauki carbinsa Yana tasbihi ya kwanta a Saman bed dinsa,Mummy ta kwashe kwanikanta tas ta fice ta wanke Kal ta Adana sannan ta koma wajen me gidanta,carbin ta samu ya jefosa kasa tana zuwa ta daga hannunsa taji ya saki alamar ya mutu rai yayi halinsa, murmushi ta saki tace akan kamin kishiya wallahi gwara ka sheka can Kai ka isa mutumin banza butulu,Kuma dole group na company naku su ajiye million goma in Sha bushasha ta,Hannu ta Dora a Kai da kururuwa ta fito tana ihu tana bako ya kashe min miji,Magani ya bani na karfin Maza ashe guba ya bani Mummy ta zunduma waje ta tara mutane ta kirawo makwafta,ta hau kiraye kiraye na Yan uwa da abokan arziki sannan ta kira police suka dungumo gidan, gida ya cika makil,Har Hajiya Tagwadas ta kira a waya ta taho hankali tashe domin ita har ga Allah burinta ta samu shiga a cikin masu kudin danginsu ta dinga samun kudade shi yasa ta kawo Naila ko zata Saba da su ta samu saurayi a cikin Yan gidan tunda suna yawan zuwa gidan sannan tasan watarana Mummy zata iya tafiya da ita cikin dangi kuma sai suka canja su gwada maganin ko Mummy zata dace mijinta ya warke ta haihu.

Naila bata gane batu ba,sai da Mummy ta shaketa tare da kifa mata Mari tana jijjigata tana cewa matsiyaci ashe maganin kisa ka bani ka kashe min mijina ta dinga zabgawa Naila Mari, Naila zuciya ta ciyota ta dauki sandarta ta bugawa Mummy iya karfinta a kanta Nan ma Mummy da sharri ta sulale ta fara suman karya farrrr farrr, Naila ta jefar da sandar ta haye ruwan cikin Mummy ta dinga rama marinta mummy duk ta shanye Marin nan wai bata sani ba suma take, Naila ta daga hannaye sama tace a tafi dani da hujja Allah shine shaidata,wacce Bata San alkhairi ba butulu.

Da ace baki saka Masa guba ba maganin Dana baki kika saka Masa wallahi da aurenki ya daidaita maybe ma ke da kishiya shike nan watakil ma ki haihu kinwa kanki, ta ciro takalminta ta bugawa Mummy a Baki baki ya fashe amma duk Mummy wai suma take bata sani ba bayan tana Jin komai.

Mutane kafin kace me gida ya cika dam ko Ina manya Maza da mata,ga dangi ta ko Ina suna ta parking motoci ta bangaren mata da Maza,da kyar aka banbare Naila daga kan Mummy, kuka ta saki taje ta shaki Hajiya Tagwadas tace Allah ya isa d...da ...da .kika...kawo ni Nan...duk kafin kace me sojoji ta ko Ina a gidan matasan samari hadaddu suna ta dira dangi, a tsakiya aka saka Naila duk an zagayeta ana kallonta mutane har sun firfito da waya,ba Wanda ya gane macece,Misam ne ya Dana bindiga yace wallahi duk Wanda ya daukar mana hoto sai na harbe shi,ai kowa a tsorace yayi kasa da waya wasu ma jiki na rawa suka kashe wayar,Mummy dai tana can mata suna ta yayyafa mata ruwa da ta farfado tace wayyo mijina sai tayi farrrrr luuuuu da Ido sai suman karya, suna ta fama sai da kyar ganin za a gane ta sannan ta farfado gaba daya ta kurma uban ihu ta fado cikin mutane da gudu ta isa Inda Naila take ta Kai hanu zata shaki Naila,lokacin Naila zuciya taci karfinta hannunta ta rike gam iya karfinta ta lankwasawa Mummy yatsu,Kara da Ihu Mummy ta tsala tace a dake ka a hanaka kuka ga Mari ga tsinka jaka, ta sake Kai daya hannun Naila kamar Dan biri tayi tsale ta dane Mummy ta shake Mummy,Misam a ransa yace tunda yaron can yake fada haka yana da kamshin gaskiya ya kamata ayi bincike me tsanani.

Mummy ta kwace kanta da kyar tace namiji ya rungumeni Kuna kallo wayyo...namiji ya rungumeni fasiki ne, Naila hawaye baya tsayawa a kumatunta Taga dai Maza manya sun shiga part din Alhaji Aliyu ana Masa sutura, da kanta ta taka gaban police da suka shigo ta mika musu hannayenta biyu tace cikin turanci ku tafi dani muje nasan Allah zai fitar Dani,sai lokacin kowa yayi mamakin Jin turancinsa ba kowa ne ma ya iya irin nasa ba Dan kuwa Naila ta iya turanci ba karya.

Yan sanda suka sa mata sarka a hannu ta shige mota da sauri domin kallon da ake mata gwara ta shiga motar taji sauki tsoro take ji kar a gano macece ce shine damuwarta kawai, suka ce ai kuwa duk mutanen Dake gidan abin ya faru sai an tafi dasu har Mummy, Tagwadas itama kuka take domin itace ta jawa Naila wannan masifar haka ta daka tsalle tace nima a tafi dani,sai masu gadi suma an tafi dasu,Mummy tana an kashe min masoyi ta shiga motar Yan sanda aka tafi dasu,sai Yan uwa a gidan suna zaman makoki aka Masa sutura aka kaishi makwancinsa aka ci gaba da zaman makoki,wayoyin Ashraf Spark sunki samuwa dama haka yake yi ya tafi waje bazai kira kowa ba,da yawa ko number dinsa ta Nigeria wasu basu da ita,ko ka kira ma sai yaga dama zai dauka.

Sai Kamal aka sanarwa ya sanar Masa,yace shima Bai kirashi ba,Daddy yace to idan ya nemeka ka fada Masa tunda shi bashi da hankali,Dake da yawansu sojoji ne wasun su duk basu wani ji abin sosai ba sun Saba ganin mutuwa da kisa da cases daban daban.
Bayan kwana uku ana bincike amma Naila baza ta fita ba Sam, gaba dayansu case din kotu aka mika su,amma Mummy sai da tayi kutun kutun aka Maida karar can kotun Kano sai kudi take kashewa lallai ayi sauri a yanke hukunci kar bincike yayi tsanani a ganota.

Sanda aka sanarwa da su Mohsin me ke faruwa hankalinsu ya tashi matuka ba kamar Mohsin da suke shiri da Naila,yafi kowa shiga wani hali sai Abbansu shima ya damu sosai,Umma kuwa bala'i ta hau yi tace Yar iskar yarinya ce bata Jin magana,taurin Kai da ketare maganata shi ya jefa Naila a wannan halin,nayi Imani ko kaffara bazan yi ba kin Jin maganata da Naila ke yi shi ya jawo mata sai da nace kar ta siyar da maganin Nan bana so Bada yawu na ba,amma jarabar taurin Kai da jahilci da hauka shine ya ja mata ai gashi Nan hukuncin kisa za a yanke mata Allah yasa ba ita kadai na Haifa ba,nayi nayi tayi aure gata da masoya taki ji ai gashi Nan,Kuma wallahi babu Mai zuwa Kai mata ziyara a nan gidan sai taji jiki a gidan yari.

Abba yace koma mene ke kika jawo ke kika turata,to na turata baza kaje ko kotun ba wallahi,ance an kawo shariar Kano to baza kaje ba,nima baza ni ba Kai duk gidan Nan,Hidaya tace Haba Umma ke kika haifeta fa Dan Allah kiyi hakuri sharri aka mata wlh baza ta iya kashe wani ba,shima kaninsu yace wallahi sister baza tayi ba ni dai Ina tausayinta,kanwarsu ta karshe itama tace nima haka bana bayan Umma.

Umma da bala'i tace to naga Wanda zaije kotu ko an yanke hukunci naga me zuwa ziyara gidan yari,Hidaya tace nidai ance soyayyar Uwa da yaranta daban ne amma ke Umma taki ba haka bane, Umma jaka ta dauka ta fice an rasa Ina take zuwa tunda cikin ya Dan Kara girma Umma kullum sai ta fita ta dawo ko ina take zuwa oho Kuma idan zata dawo sai a ganta da fara'a ashe warin gardi take shakowa ko warin taba sigari.

Mohsin Kam baya iya bacci sabo da halin da Naila ke ciki kullum a cikin damuwa yake,gashi su ba masu kudi bane sai rufin asiri,ita Kuma Hanan matarsa ta takura Masa ita baya mata soyayya baya kulawa da ita sai tunanin kanwarsa,bashi da lokacin fada da ita sai dai addua da yake faman yi Allah ya fitar da Naila.
Chapter 15 · 0% Book details