← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 98

Sashe 74

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har gidan Mummy suka shiga tare da parking,Chikar gayu ita ta shiga motar kayan Naila sun wuce gidan Amarya ita da me Jan motar.
Spark fitowa yayi ya budewa Naila tare da riketa ya fito da ita,Mummy suna leke ta window Baki ta tabe tace kuzo kuga duk Yan kauye ne suka kawota amma dai sunga kawayen Umma duk su Yan birni ne basu da mukusa,Oh ni na shiga uku ya kwaso min matsafa yaran talauci,dama wata yar film ce Yar gidan masu kudi, Ni tunda tayi yankan Kaunar ma wlh ban sake Ganinta ba,ita a Yan film din ma ba wata popular bace domin tunda naji ita ya aura na shiga bincike Ina tambayar kawayena ko sun San wata Nasiba Yankan kauna ba Wanda ya ganeta,wata tace maybe irin sababbin Nan ne Yan giggiwa ba Wanda ya sansu sai karya,idan kin kure su baifi a Waka suke fitowa ba,ai kyau ya bi da wanka,indai wanka ne basu da na biyu,Mummy tace ku gyara gasu Nan dangin tsiya anzo za aci arziki.

Zama suka yi suka nutsu, Spark cikin mota ya koma ya zauna,Goggo tace tafi a hankali Naila,cikin kawayen Umma daya sun rike hannunta sai zuba guda suke ayiririri,Spark yaji guda har kunnensa yace yanzu nasan Amarya ta iso harda Kara sauke glass yace bari naji da kyau.

Kida gaba daya motocin suka saki gaba daya iri daya wakar yan Nija,Rafeeq Yana mota harda rawa a zaune,Yana cewa layi yazo kanmu,Mummy su kansu dariya suke tace wannan yara namu anyi Yan iska, yanzu dan Amarya shine aka sa mana uban kida haka duk sun hanamu Jin kunne, Dangin Amarya suka shiga da sallama ga katon carpet, a nan suka zaunar da Amarya tana zuba kamshi,duk sauran mutanen dakin sun yaba da Amarya amma Banda Mummy ta dai danne ne kawai sabo da Spark kar yazo ya mata tijara,amma da sai ta jefar da magana,amma duk da haka sai da tace ai da baku batawa kanku lokaci ba ma ya dauki abarsa ai mun ganta a gidan nasa tuni tasan har gadon kwanansa.

Goggo tace yo ko ba komai ai tazo ta gaida iyayen Angon nata, ta ganku ku ganta ai wata girmamawa ce daga wajen Iyayen Amarya Hajiya,Badan yace muzo ba ma baza mu zo ba, sai mu wuce dakin mijinta kawai,idan badan zamani ba ma waye yake wani Yan biye biye da Amarya har wajen uwar rainon Ango,wai bama uwar da ta haifi Dan ba,sai zamani yanzu a fara wani biye biye da Amarya ana samu gantali a hanya,Mummy mukus suka yi sunji Goggo ta Maida martani,Mummy taji ciwon maganar Goggo wai uwar raino wato sabo da bata Haifa ba ake mata gori.

Kawar Mummy malamar makaranta ce itama tare suke koyarwa a primary school,tace please arziki ya kawo mu ba wani abu ba,Amarya ce gata nan yarku ce dai,ba wani abu ba, a bude taro da Addua,aka yi addua aka shafa Banda Mummy dake danna waya tana chat da Basiru Kusan ta, wata ce a dangin Ango babbar mace tayiwa Amarya nasiha sosai,tace Allah ya kade fitina kinji.

Naila ta fara kukan karya tana shesheka,su Goggo duk sun zaci da gaske kukan take,harda cewa yi hakuri yar nan kowa da haka ta Saba,Tani tace 'ya mace ai 'yar gidan wani ce, duk haka aka yi mana Naila aure sai hakuri,Goggo tana cewa rabuwa da iyaye ba wasa ba,Allah sarki sabo da gidane da iyaye,ko Kaka 'yar Nan ta tuna ai tayi kuka,Mummy ita dariya ma suka bata yarinyar da suka samu kwance a kirjin mijinta wai yanzu itace take kuka, Mummy tace ai fa Amarya sai da kuka ai,Rayya ce ta taba Naila tana girgiza kafadarta tace ki daina kuka kinji nima zaki sani kuka shike nan mun rabu an raba mu,ta rungume Naila ta fara kukan gaske ita,Naila ta kankame Rayya tana kukan karya,Goggo tace dole kuyi 'ya'yan nan,saurin kuka ne dani karku sani nima Dan Allah.

Mummy baki ta saki tana mamaki tace a ranta amma yarinyar nan anyi Karuwa kaga yar iskar yarinya,yau naga Bariki,lallai bariki iyawa ne wlh,Bariki ba sai an nemi Mazan banza ba,a fili tace to Alhmdllh mun gode Allah ya bada zaman lafiya,sai a kaita can gidan Mima din,suka yi godiya suka mike tuni matan dangin Ango suka rako su da Abinci anyi wrapping dinsa a wasu paper masu kyalli na musamman,ruwan roba da lemuka carton sunfi biyar, Mummy komai sai anyi karya,a bayan mota aka zuba,Amarya kafin tazo Ango ya bude mata ta shugo, yana cikin mota bai fito ba kidansu suke Sha kamar zasu tsaga gidan,Rayya ce ta rufewa Amarya murfin tana share hawayenta na gaske ta shiga mota suka fita sai gidan Mima.

Kidan suka rage sai kadan kadan kowa suke ji a motocinsu,Naila mayafinta ta janye kadan tace na Sha kukan karya kowa ya daka ta Tantiriya zai kashe kansa watarana,Spark yace au Kuka kika yi? Naila tace na karya ba sai bani hakuri akeyi,Rayya mahaukaciya wai kaji ta fara na gaske,Spark yayi dariya yace kin birgeni keep it up,Naila taji dadi ya yaba a ranta tace ka shiga uku idan muka je gida tunda kace naci gaba ai yau kwana zanyi Ina kuka sai na Kara birgeka.

Spark yace saura su Mima Kinga kunkan karya yasa kinyi zufa,driver karo AC,driver ya karo AC yace to shafa wata powder kar aga Amarya da gumi kamar na wani kwalbe,Naila powder ta sake shafawa sama sama ta gyara sosai harda gyara pink jambakinta tace yayi? lekawa yayi yace yawwa,Mayafin ya gyara mata yace badan kayan Nan suna da kyau ba da tuni sun yi dukun dukun a tafiyar motar nan,Naila tace na gaji ma wlh baka ji kafata ba,Yace wannan karki damu da gajiya Hallare zata sauke miki ita tsab,Naila tace sai kace wani magani da ake cewa Daga,tafi Daga ai.

Gidan Mima a cike yake da Yan uwa kaf Maza da mata sabo duk ba a San Amaryar ba,kowa ya baza Ido zaiga Amaryar Spark,za dai muga karyar Spark a Ina ya kare,Badia kanwarsu wacce itama tun daga Bauchi tazo har Abuja da yaranta kawai Dan taga matar Spark wacece,dama idan mutum yayi fice a iya shege da tsirfa to kowa zuba Masa Ido ake aga zabinsa.

Anam tace munzo bikin amma tsabar haushi Bai auri Wahida ba yasa duk muka koma, ko gidansa bamu je ba bare mu ganta, Munji dai ance Yar aikinsa ce,Yar kauye ce ma,tab yanzu haka ma mummuna ce,mazan Nan suna ta dariya suna jira su sha kallon Amaryar Spark,taron na Mata ne amma duk sunki tafiya kamar mayu.
Harda sake kunna fitilun palon,duk ranar da take gari,wani Arham yace tunda naga ko status Spark baiyi da ita ba nasan bata hadu ba, ai gudu yake kar ayi Masa dariya,Dan Allah Mima kuce ta yini a Nan mu ganta sosai zuwa yamma sai a kaita gidansa.

Mima tace ai dama yace anan zasu yini sai yamma za a kaita can,wai ko uban me ake saka Masa a bed masu aiki basu gama hada gidan ba,Badia tace lallai Yaya duk tsadar kayan gidansa? Mima tace ke kuwa zai kawo 'yar gold ya bazai canja komai ba,ai gidan ya koma sabo wlh ya canja komai na gidan,Kuma in Kinga kayan da ya canja sai kin rantse 'yar shugaban kasa ce zata tare a gidan.

Har kofofi duk an canja ke har su globes bai bari ba,ai naje gidan na Sha kallo, nan kusa baza ki samu gida me kyau da aka kashewa kudi haka ba,ni mamaki ya bani ma,mutumin da watarana budurwarsa ta Ghana ta yaudare shi, karshe ya gane kudinsa ta ci kawai, yazo nan gabana yana cewa Mima I swear na gama love har abada bazan Kara son wata ba, tana gwada yanda Spark ke magana,wai budurwarsa ta karshe Lilly?Anam ta tambaya, Mima tace ita fa.

Spark ya Sha wahalar soyayya mata hudu ne suka yaudare shi, Kuma duk da haka gaskiya Banga wacce yake so irin wannan da ya aura ba,cewar Mima,Yana sonta sosai,idan ta kirashi jikinsa har rawa yake,amma waccen kuwa wlh ko sun kira sai yaga dama yake dagawa,kiji Yana musu tsawa,sannan suna yaudararsa idan ya gane zaki ga ya rabu dasu ba wahala Kuma zai ci gaba da rayuwarsa normal kamar komai bai faru ba.

Wannan Naila kuwa akanta zai iya haukacewa na tsorata da Spark akan yarinyar nan,sai yanda tayi da shi,mu da a gabanmu ya fada mana ni da uwarsa Mummy yace ya zama Sallamamme,sai abinda tace,mu ja girman mu idan ba haka ba ko me tayi mana bazai iya magana ba,shi yasa ba ruwana da gidansa,badan ma yace muje muga gyaran gidan ba bazan je ba.
Badia tace to ko dai asiri suka masa kin San 'yan Fulani fa.
Chapter 74 · 0% Book details