← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 98

Sashe 13

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta mike tsaye tace bari na mike Kafi ganin tsayi na sai ka raina min hankali da kyau, wato sabo da wulakanci shine jiya kayiwa Asmau korar kare ka sani aure ba fashi gwara ma ka so ta, wallahi ka kiyaye ni karka ga wai ubanka babban Soja ne,kaima ka fara aikin soja kayi resine ba abinda ya dameni,ni na raineka Mahaifiyarka kawai haifarka tayi baka isa ka min iskanci ba,Dan karamin bakinsa ya tsuke yace Ohhh Mummy kin san bana sonta, ki daina jawowa Ina bata miki rai a kanta,ni fa ba yaro bane babba ne,Ina aiki Ina da kudi ku daina rainani komai kice sai yanda kika tsara zanyi bazai yuwu ba fa Ina fada miki kar kuyi Kuskuren daura auren nan wlh zan iya sakinta a wajen nan take,zaku ji kunya ki daina turota gidana haba ai ba tsari ba class mace tana bin namiji har gidansa Kuma gida ni kadai a ciki,duk ranar da ta sake zuwa sai na mata tsirara sannan zan jefota waje idan baku yarda ba ta sake zuwa ku gani, Kai ya girgiza kamar Wanda ya Sha kwaya yace nayi warning naku a daina takura min bana so a kiyaye, ya juya ya fice abinsa ba tare da ya saurari me zata ce ba.

Mummy ta zauna jiki a sanyaye tace innalillahi na cuci kaina Dana dinga barin yaron nan a kasar waje gashi nan yafi karfina ayi yaro duk ya gagari kowa ta zuba uban tagumi.

Shi kuwa gogan gidan Mima ya nufa wacce itace ta haife shi,gidan ko Ina sojoji ne birjik sabo da Babansa Babban Soja ne,sannan yayansa da kannensa ma mazan Sojoji ne, Yana shiga ya iske kannensa mata da Maza har da matan duk da kayan sojoji a jikinsu suna ta faman rawa a Palo sabo da tabara,Yana shiga suka kashe kidan sabo da sun san rashin mutuncinsa ba Wanda ya bari, part din Mima ya shiga tana bedroom tana shiryawa mijinta kayan tafiya zai bar kasar, sallama yayi ya shiga itama a tsaye yace morning Sweety

Murmushi tayi tace ka tashi lafiya? Ni fa bana son gaisuwa yanzu da ba lafiya nake ba ai bazanzo ba,to zauna mana ,bashi ya kawo ni ba,ki fadawa Kanwarki tunda ke yayarta ce ta daina matsa min bana son Asmau ki fada mata Ina ganin girmanta tunda ita kuka bawa rukona kawai an bata ni kyauta duk ta matsa min,bana so a fada mata.

Kai Dana ne dama? ai ni sanda na mallaka mata Kai har abada na bata ni ba ruwana da safgarku, ku kuka sani kunfi kusa ai,kar ka sake kawo min karar uwarka, Kai da Rafeeq me yasa bakwa son a zauna lafiya ne,ga Rafeeq Kuma ma ko Yan Nan gidan bai saurara sai yaga dama daga shi sai Islam abokinsa to ya fika ta wani bangaren shi Yana yiwa wacce ta rike shi biyayya baida kamarta,amma banda Kai you are so stubborn.

To kuwa an kusa sawa na fara neman mata nima indai za a aura min Asmau neman mata zan fara,Yar uwarka ce fa cewar Mima,yace Yar uwar me ni Ina ruwana da wasu Yan uwa,tace toooo zagi ya matso kaina,juyawa yayi ya fice abinsa ko bangaren mahaifinsa bai saurara ba ma yasan ba zama yake ba,duk Yan gidan basa gaisuwa daga Hey shike nan,ba Wanda ke safgar wani sai da dalili,ko sun hadu baza ka gane Yan uwa bane sai dai a kamanni,shi kuwa Spark bai ma fiye kama da su ba,kamar ba Dan kasa ba haka yake kamar a wata kasar aka haife shi can Jinin nasara,ga tsirfa wani irin murdadden mutum ne.

Bayan sati daya Spark yayi shiri ya bar kasar ya tafi Germany,ba wanda ya fadawa sai dai aga baya nan kawai, Kamal kadai ya fadawa,Indai suka ga shuru bai zo ba to baya kasar kowa yasan wannan amma indai Yana gari dole sai yaje ko fada anyi da shi.

Naila dai Umma ta sata gaba sai tabi Hajiya Tagwadas zuwa Abuja haka Mohsin yace tayi hakuri taje tunda sati biyu ne kawai zata yi,waya Yar karama keypad ya siya mata da layi rike wayarta na farko a duniya kenan ya koya mata yanda ake amfani da ita,ta hada kayanta a Yar jaka da Umma ta Bata.

Yau zasu tafi da wuri ta shirya taje har dakin Abban su ta same shi Yana Shirin fita aikin gadinsa da ya Saba tace Abba zan tafi ayi mana addua,yaran yanzu ana musu addua ma ya muka kare kana dai gani yanda dole sai mun lalace bare ace ba a yi min addua ai lalacewar Abba sai tafi haka,ni kaina tsoron kaina nake yi,Abba in kana jin Yar hau to nice sabo da haka a surfa min addua ta cire mayafinta tace dafa Abba sa min albarka.

Abba yace to.. to ya dafa kanta yanda tace ya furta Naila Allah ya tsare,iya albarkar kenan?ta tambaya, ya zazzaro idanuwansa Wanda suke kamar yayi zawo na shekaru yace a dai dinga kula,abi duniya a sannu,a Dinka taka duniya a hankali,yawwa na gama shike nan jeki cewar Abba, Naila bata gane hausar ba tace to Abba sai ta fito tana sanda tana tafiya kamar barauniya zata saci kayan wani.

Lokacin Mohsin ya shugo gidan ya iske abinda Naila keyi tana faman sanda yace ke Kuma mene haka? tace Abba ne yace nabi duniya a sannu na takata a hankali,dariya ta kama Mohsin ya dinga sheka dariya yace to Yar kauye ba haka yake nufi ba fada ya miki fa lokacin ya ganar da Naila me ake nufi,ta dinga dariya da maganarta ta yan Fulani tace aradu ni kwai wawiya bani da Kai sai na daukan kaya ai Affa shi baya min haka sai dai ya dinga washe min Baki.

Tace Abba kuwa harda zazzaro Ido duk akan zai sa min addua ya Ilahi wlh sai naga kamar Wanda ya Shekara a gadon asibiti yana jinya,gaskiya Umma tayi babban Jihadi data iya auren Abbanmu kan uba wlh da nice gwara na tafi yawon ta zubar, Mohsin yayi dariya kamar ba gobe,Naila tace Allah Yaya kirjin Abba kamar na fara,baki ta toshe da hannunta tana dariya a hankali tace a haka wai shine bargon Umma ai yasin ko quarter din Umma bazai rufe ba,ya Umma take yi da Sanyi? Allah ya bani kudi na siyo mata bargo babba na gaske karta dogara da kirjin Abba,ta sake rufe bakinta da tafin hannu tana dariya Kallon Mohsin ta yi tace Yaya da alama Kun shirya da matarka ko?

Rada ya mata a kunne yace ae maganin gargajiya za a bani,dariya tayi tace bana murna kishi nake yi da hassada me yasa kuka Jone? Ai tunda naga ka shugo kana yaye mana hakora nasan jiya an rufe kofa,baki ya make mata, tace nidai kishi nake ta fada tana harararsa.

Mohsin yace baki tambayi Amal yarki ba yau,Naila tace wai Kai Yaya Nan murna kake yi kayi abin kunya ya fito fili? Ban gane ba ya furta,tace abinda kayiwa Hanan matarka ta samu ciki ta haifo Amal ai rashin kunya kuka yi a daki sannan aka samu cikin gashi ta haihu kaga kowa yasan me kuka yi abin kunya ya fito fili,Mohsin dariya yayi yace ke kika sani ni dai na haifi 'yata, kallonsa Naila tayi tace uhmm kaji da shi, nifa shi yasa Sam ba sosai nake kiranka da Yaya Mohsin ba tunda ka haifi Amal nasan kaima A ne kana rufe kofa,Mohsin gashinsa me yawa ya shafa.

Hidaya yau ba school su hudun suna gida,tana ta aikin gida Hidaya komai ba abinda bata iya ba a rayuwa na aikin gida,ita kuwa Naila ko wanke wanke komai sai dai ayi mata.

Mohsin ne yaja Naila gefe yace ai dai gidan Yan uwanta zaki raka kawar Umma ko? Naila tace ae haka tace shine fa Umma tace masu kudi ne gidan suna da Maza wai na bude Ido na kalle su ko zanyi saurayi,wai yaran dangi ne gida gida duk dangi ne,Mohsin yace kina Jin wahala ko baza ki iya ba ko da matsala ki gudo gida kinji ko ki kirani a waya kinji ko? Tace ae naji Yaya,I will miss you,ka kular min da kanka,Jikin Nan natural a adana shi,zan tsananta bincike ko Kai ba Dan Abba da Umma bane ya kamata ayi bincike,zai wahala ma ba musaya aka yi musu a asibiti ba,Dariya suka yi Mohsin yace a gida aka haife ni ba a asibiti ba kinga dansu ne ma, kiyi hakuri ki samu wani yarinya, Nooo... rayuwa sai dai Yaya ta furta tana dariya,wasan su kenan tun Umma tana kulasu yanzu zuba musu Ido take yi.

Hajiya Tagwadas ce ta shigo da uwar akwati anci uban gogoro kamar Yar yorubawa tace yawwa ke 'yata fito mu wuce me napep zai kaimu tasha,Umma tace to kuje Naila Allah ya tsare,Naila tace ke Umma Tagwadas daukar min jakata ai ke zan raka unguwar bazanyi wahala ba, ni sandata kawai zan dauka waye yace kice na rakaki shike nan jakar ma sai na dauka ,Naila dai da kyar aka lallabata ta saka riga da skert na atamfa sabuwar da aka Dinka mata,tayi mata masifar kyau,ai suna ficewa daga gidan ta ja skert dinta sama ya dawo wajen gwiwa duk kaurinta a waje ana kallo,Tagwadas tasan taurin kan Naila yanzu sai tace ta fasa zuwa, ita da take so a can ta samu me kudi yace Yana son Naila cikin Yan uwan nasu shike nan ta samu hanyar shigar su burinta kenan shi yasa ta zuga Umman Naila tace zasu samo kudi da miji na gari me Naira.

Suna cikin Napep Tagwadas tace gidan da zamu je basu taba haihuwa ba,Kuma ance matsalar a mijin ne,Naila ta zaro ido tace to ga shawara ta samun kudi Umma Tagwadas,tace Ina jinki Naila,me zai Hana muje ayi min askin Maza me kyau ayi min Daadaa, nayi shigar Maza kawai na koma namiji sai na basu magani ko zasu dace Kinga idan suka dace mun zama masu kudi musamman ke da kika yi hanyar magani,idan naje a mace baza suyi Amanna da maganin ba
Chapter 13 · 0% Book details