Sashe 8
Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umma....Umma....yawu cike a bakin wacce aka kira da Umma ta fito tace Naila tafiyar ce ne? Naila tace ae Umma daga kauye sai Abuja tunda daga can zamu wuce kince na biya na gaisar da Affa ko? Ai gwara ki bi Hajiya Tagwadas kije Abujar Nan wallahi wannan dolon uban naku ba komai yake tsinanawa ba shima sai dai a bashi,Naila tace Dan Allah Umma ki daina yiwa Abba haka bai dace ba Kuma a gaban mu haba wannan fa yawa kike Umma.
Umma share Naila tayi taci gaba da magana idan kinje Abuja ki bude idonki ki gano hanyar samun kudi ko kanwarki ma Hidaya kizo ki jata karki biyewa babban yayanku Mohsin da shegiyar bokon nan marar amfani,Ina boko Taga amfani a kasar Nan ka gama duk karatunka mutumin da ko primary Bai je ba bakauye sune masu kudin kazo wai kana neman aiki a karkashinsa sabo....yawun da ya sake cika mata baki ta zubar tace jeki Allah ya tsare ki kyale su Mohsin kuje kauye ku gaida ubana ki wuce can garin kudi Abuja garin Alhazawa,Naila kyakyawar gaske ajin farko tayi dariya tace maganin da Affa ya koya min shi zan Kara koyowa gaskiya naje da sana'ata Abuja,tunda a nan Yaya Mohsin ya hanani Bada magani,Umma tace ni kaina bana son wannan sana'ar Ina mace Ina siyar da maganin karfin Maza,Naila tace sai ni wlh burina kenan na dinga gyarawa mata mazajensu Ina fixing din wacce ta samu matsala in ta kama ma na kalla,Harara Umma ta balla mata tace haka na muku tarbiyya ki zama me class ai gwara in kinje can ki dinga gayu kina samo alhazawa masu kudi kina cin kudinsu,Baki Naila ta tabe tace nidai gwara na samu halak dina tallan maganin karfin Maza tunda Ina da nasibi Akai kina ganin awwalu matarsa bata taba haihuwa ba amma da na bashi maganina ya warke yanzu yaransa biyu a kauye.
Sannan nan tsohon Nan Tafida abokin Affa da zai Kara amarya ni na tsumashi ki duba tsufansa amma sai da na Masa garanbawul ya Mike,ga wannan Dan lukutin Alhaji shehu,Allah ya rabamu da Maza Yan lukutaye Dan Ina Jin kunyarki ne Umma da na Baki labari,Umma wacce ta zubawa Naila Ido baki bude tace ke fa halina Dake bakya Jin magana ba Wanda ya isa dake ba Wanda yake saki ko ya hanaki haba Naila ba mutuncinki bane ki daina biyewa Affa sabo da kin taso a hannunsa, kina daji baki san me ake ciki ba yanzu an waye mata aji ne dasu gaki kyakyawa,lalacewar da kika yi yasa na kwato ki daga can rugar Fulanin,Affana ya lalataki da ya koya miki irin sana'arsa bakya gani shi namiji ne,Naila p-cap dinta ta gyara tare da turo baki gaba tace wallahi ni nafi son kauye bana son birnin nan Kun fiye takura ta furta tana karkada handkerchief a hannunta, ta duka tare da goge takalminta Snickers black me kyau na zamani Wanda Mohsin ya siya mata,wando ne a jikinta pencil baki sai rigarta shirt me dogon hannu tsayin rigar ya Kai gwiwarta gata me Fadi da ace bata da kyau da mugun Muni zata yi amma Dake fara ce kyakyawar gaske ga diri me kyau sai tayi kyau sosai ta zama wata Yar gayu,gashin dai gashi nan a cukurkude bata son a taje mata gashi Kuma baza ta taje ba gashi irin na Fulani jaja ba baki ba sai tsayi da santsi.
Kudin mota Umma ta mika mata tace gashi tashi kije ku tafi ta kawo kudin mota ta mika mata,Naila ta karba ta irga taga dubu bakwai ta Kalli Umma tace me nake gani haka in this situation? Dubu bakwai Ina zata kaini inje kauye Kuma naje Abuja duk a dubu bakwai,dama kin san baki da kudi kika ce na bita Abuja ni bazan je ba wallahi Allah na fasa,yanzu ko maleji ai sai ki hau,Ihu Naila ta kwala tace ni kamata Yar gayu a maleji Allah ya kiyaye,Umma kin san fa ni ban san babu ba ato duk abinda nake so Affa yi min yake wallahi sai abinda naga dama,nace muku idan baza ku iya dani ba ku maidani wajensa for God sake makaranta ce nayi Kuma nafi su Hidaya iya turanci ma tunda turanci ku kunce shine Ilimi,nifa bazan iya daku ba yawwa.
Mohsin ne ya shigo yaci wankan kana nan kaya,yace ke Kuma wa kike dagawa Murya? Umma? Oh na San baki da tarbiyya dama tunda Affa ya kaiki kauye nasan jahila zaki dawo mahaifiyar taki kike fadawa magana anyhow? Naila kwalar rigarta ta gyara tace ni nace a bada ni,gaskiya na fada taya zata turani Abuja da 7k a rayuwar yanzu,hasali ma abinda take nuna min nayi ba me kyau bane,wai na tara samari nayi amfani da kyau na naci kudinsu me Hakan yake nufi? Nayi karuwanci,Umma ce ta buga tsalle tare da toshewa Naila baki kar aji wai,Mohsin da mamaki ya Kalli Umma yace hakane? Ina...Ina Umma ta fara tace karanta mata nake akan ta zama me aji,amma kanaji fa tallan maganin karfin Maza zata yi,Naila baki ta cuno tace sana'ar Dana iya kenan ko kai Yaya idan Hanan bata gamsuwa ba matsala zan iya baka magani in ta kama ma na kallet.., Mari ya zubawa Naila kafin ta rufe baki yace kina hauka ne ni sa'anki ne? Banza Yar kauye jahila,Naila murmushi tayi tace saiwowi ne Yaya, Umma tace na shiga uku ni Kubra,na yarda shi yasa a kauye suke ce mata Tantiriya Naila,ai na cancanci sunan Umma bana Jin magana wlh kuyi hankali Dani tarbiyyata sai an shirya na lalace kunyi sake,ni da kaina watarana Ina zama in ta tunanin kaina da kaina nace ke Naila kanki babban ne cewar Naila.
Ni kuwa zanga Wanda zan aura a duniya,ya shiga uku duk Wanda ya aureni ya auri alakakai babu zancen soyayya ni ban iya ba,mene soyayya ban santa ba zaici ubansa mijina Alqur'an.
Yanzu dai kin fasa zuwa in kina so naje ki karo kudi ba maganar maleji ban san shi ba. To kawo kudin a ajiye idan kudi sun cika sai ki tafi,Murmushi Naila tayi tana goge takalminta tace wannan ai saidai naci tsire dasu sunzo kenan ai ni kudi basu taba shiga hannuna sun fita wlh bazan bayar ba dama na dade banci nama ba,kullum daga shinkafa da wake Mai da yaji,sai tuwo sai dafaduka shike nan nake ci a gidan Nan.
A wajen Affa kuwa kullum sai ya yanka mana zabi munci abinmu ,dagani sai matarsa Iya tsohuwa mu uku abinmu,ni bana farin ciki da samun kanwa irinki a rayuwa cewar Mohsin ya ja tsaki ya fice ,Naila tace tsaya Yaya mu tafi gidanka mana,Allah ya kiyaye na daukeki a haka a machine dina ki canja kaya na mutunci,Naila tace jeka zanzo da kaina ka cewa Hanan ta min faten wake masu gidan zasu zo,Dake ke kika Gina min gidan ko,Kinga ni bana farin ciki da zuwanki kowa ya tafi Islamiyya Banda ke,Islamiyya zanje yanzu da girmana sai kace sabon tuba ko wata yarinya ni yanzu karatun Islamiyya ai bazan iya ba Ko Kai Mohsin wlh sai na kureka a karatun addini,nifa bana ji ne kawai yawwa duk Inda naje sai na buwayi kowa Kun dakkowa kanku,in kana jin tsiya to nice,Umma juyawa tayi kawai daki tana tunani ita Ina zata samu Wiwi ta shaki warinta sabo da ta samu kwanciyar hankali,yau Dan cikinta warin Wiwi yake so.
Abba ne yayi sallama sanye cikin wata jallabiya fara tasha wanki,Yana shugowa Naila tace sannu da zuwa Abba Dan sawalwali,dariya Abba yayi ba shiri yace Naila bakya rabo da shiririta,Naila tace Allah Abba da Kai me kudi ne Kuma jajirtacce da mata rububinka zasu yi,Abba harda shafa kasumbarsa wacce ta Sha gyara Yana wani murmushi Yana Jin dadi Naila tana yabonsa a ransa yace Yar cikina ma Taga kyawuna bare Yan mata,Me kake tunani ne Abba ta furta tana goge shegen takalminta,Cikin kasa da Murya Abban su Naila yace shi yasa kullum idan na fito sai naga su Harira suna ta kallona na rasa dalili ashe so na suke yi sunga kyau na, gaskiya naga fa'idar Tsafta,rannan haka Lami me abinci a bakin tasha ta dinga kallo na,da Debora me siyar da Amala, haka zaki ga ana ta rububina musamman mata abin nan Yana daure min Kai,Naila saura kadan dariya ta kwace mata karya ta shirgawa Abba dan yaji dadi,a fili ta maze tace Abba dole yau mu fita na rakaka wajen manyan yara ka kyale su Debora,Abba yace shike nan watakil ma shine silar samun Wata attajira ta aure ni Kinga ni na huta Kuma wallahi ke zan fara kaiwa Aikin hajji na kaiki Dubai daga Nan na siya miki shirgegiyar mota,Naila tace yawwa Abba ta samo Maka aiki me kyau ma,fuska ya bata harda shagwaba yace a'a bana son aiki ni nafi so ni kawai ta dinga bani kudi Ina hutawa,Naila irin shagwabar da Abba yayi itace tasa itama ta shagwabe fuska tana kallonsa dariya tana cinta a rai tasan Abbansu baya son neman na kansa ko kadan ko ya samu aikin baya yi sai ya dinga sakaki har sai an kore shi,a Hakan Ummansu don tana koyarwa a secondary ne itace ke daukan nauyinsu sai Mohsin da yake Nurse a asibitin Aminu Kano shima Yana bajinta a gidan basa Shan wahalar komai suna da rufin asiri.