← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 98

Sashe 25

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Naila kuwa Beauty ta kwalawa kira akace ta tafi wanka tace idan tazo kuce yau bazan samu Daman Hira da ita ba naga sakon waya na gode,suka ce to za a fada mata,Malam Sharu yace Kai ni wannan Jamilu adduar ma taki Masa aiki Inda kasan shedan,Dan Indo ne ya shigo yace Jamilu Terror taho taho ga abinci, Naila ta mike ta bishi suka tafi,Scoler ya tare su a hanya yace Habibty na ajiye Maka Kazarka soyayya ce,Naila tace Rasssss dani Ina zuwa zanzo na karba,Sai da taje Wajen su Dan Indo da Goje ta karbo rabonta tace sai dare zata ci amma tana zuwa ta bawa su Malam Sharu sai murna suke yi,taje ta karbo kazar Scoler a soye ta sake kawowa su Malam Sharu,ana ta Bata abubuwa sai ta duba duk Wanda baida gata a gidan yarin ko ba a zo Masa ziyara ba sai taje ta bashi,har wasu take Gani tace wane baka bani nawa ba,sai an bata sai tazo ta nemi yaku bayi a ciki ta basu,Jamilu ya sake suna sai mutuncinsa ake gani,bayan tayi wanka da dare kaikayin gaba ya isheta tace gobe asibiti zanje inshaallah, ta shirya cikin sabon kayan da aka kawo mata suma manya falka falkan gaske, ta gyara tarkacen kayanta,suna fita Sallar Isha tayi sallarta da addua Allah ya rufa mata asiri kar a gano ta sannan Allah ya fitar da ita, yanda take sallarta idan sun fita jam'i haka tayi abarta,Allah kuma Yana ta rufa mata asiri har yau ba a kamata da mayafi tana sallah ba a haka ma sai ta nemi lungu a cikin dakin take yin sallah.

Malamai suna dawowa suka zauna zasu fara karatu yau sunci nama harda fara addua kafin a fara karatu suka ce yaron nan Jamilu idan sharri aka Masa Allah ka fitar da shi,Allah ka shiryi Jamilu,Allah Dan darajarka ka kubutar da Jamilu daga gidan nan,ka Kara daukaka shi suna cewa Ameen Ameen, Bismillah da Ayatulkhursiyyu,Naila dariya ta kamata ta danne ta zauna a kasa ta daga hannu sama itama tana cewa Ameen,Allah Gani ni Jamilu Allah kana kallona,Mummy ka tarwatsata,Mummy data min Sharri Allah ka tattaro bala'in duniya Dana lahira ka danna acan cikin Mummy, Allah kasa kullum cikinta ya kumbura,ka sata zawo,komai taci ciki ya kumbura,Ya Allah da zawo,da kashin jini,da amai da gudawa colera,ciwon zuciya, ciwon kafa,ya Allah da ciwon Kai,Dana mara,ciwon Sanyi irin naw,,,,tunawa tayi zata tona kanta tace Allah karka bari ta auru,Allah kasa tayi kwantai,ba ita ba samun bazawari,Allah Danta Ashraf da take ji dashi Allah kasa ayi Masa sharri irin nawa ya fado gidan Nan,Allah ka hadani da Ashraf Dan Mummy a Nan gidan yari,Allah basai na fita ba Allah a Nan gidan,Allah ka bani ikon cin ubansa,kar naji tsoro,kar ya min kwar jini,naci ubansa daidai yanda ya kamata.

Su Malam Sharu suna addua sai suka tsaya kallon adduar Jamilu suna dariya Yana gama adduar suka ga ya mike yace na tafi wajen abokina mutumin kirki Ashe Yana da kirki duk gidan Nan babu me kirkinsa idan Kun ganshi ku dinga girmamashi wlh ga kudi ga kyau ga kirki iya kirki yau da shi muka samu ladar ciyayya ma yaci abincina naci nasa,Malam Garzali yaji wani mahaukacin kishi yace kaga Jamilu ka rabu da yaran masu kudi ka fiye rawar Kai ka kula ka tsare mutuncinka ato Ina baka shawara kar a Maka wayo kana yaro a lalataka Jamilu,Jamilu kayiwa kanka fada tam shike nan.
Naila tace a'a mutumin kirki ne wannan duk gidan Nan nafi kaunarsa,Wanda nake jira Allah ya hadani da shi Dan Mummy ne wallahi bala'i da masifa har sai na aro ta Ummata,rashin mutunci da tuggu kuwa shima sai na Nemo Kari sai na kusa halaka shi da sharrina,Malam Sharu yace wannan yaro Ashraf ya shiga uku har na fara tausayinsa mu kanmu da ba abinda ya hadamu ka buwaye mu bare shi,Naila ta fice abinta harda shafa turarenta sabo da Spark dan gayu ne.

Yana dawowa daga masallaci ya samu Jamilu ya shugo,yace Kai naci Dan tuwonka Yana Nan shine harda zuwa da wuri,Naila tace Ina laifi Dana jira akayi Sallah ma ko tuwonka ne? an kawo Maka ne daga gidanku? Spark uban isa da gadara yanzu kirki anjima rashin mutunci,yace gashi can dauki abinka,ya furta da gadara da kyar yake magana yana bata rai,Naila taji haushi tace koshi kayi shi yasa ka fada min haka taje ta dauki abincinta ta tattara da nasa gaba daya tayi waje,ya fito da sauri ya fisgota, shi mantawa yake Jamilu baida karfi,Naila sai gata ta zube a kasa har gwiwarta ta fashe,yace sorry, da sauri ya daga Jamilu yaji shi shafal ba nauyi,jikinsa wani shegen laushi haka,tsoro ya kama Spark yaja baya Yana kallon Jamilu,yace anya Jamilu bazan Maka tsirara ba kuwa na gani namiji ne ko mace,please muje ka tube wandonka,ni ba gay bane ba abinda zanji kawai so nake na tabbatar,Naila tace au ta haka ka bullo fyade zaka min dama ance yaran masu kudi Yan iska ne to duk gidan yarin Nan sai na fada musu Kai Gay ne,Spark ya zaro ido yace na janye maganata karka bata min Suna Ina respecting din kaina da kaina.

Naila tace to karka sake ce min haka yace never, muje zaka ci abincin? yace ni da zaka bar min abincin ma nafi son haka,Naila tace to muyi musaya Kaci nawa naci naka,yace good,ta koma ta shige ciki ya shiga shima Yana jinjina anya Jamilu ba mace bane,Haka yayi shuru ya zauna Yana kallon News,Naila ta dauki nasa snacks tana ci abinta cikin Jin dadi,shi kuwa baya cin tuwo ma a gida amma gidan yari tasa wai shine ke yin wayo akan a bar Masa tuwo,tsaki yaja yace akan tuwo da shinkafa duk mutuncina ya zube wai yau ni Spark nace wa wani katon zindiki sorry akan tuwo,bazan yafewa kaina ba yaja tuwon Yana fushi Yana cika Yana batsewa haka ya fara cinye tuwonsa Yana Santi,yace uhm Poor Umma da iya girki,maganarce ta fito fili Allah yasa Naila bata ji ba da ya gane kurensa akan iyayenta bata wasa.

Naila tace ance ku masu kudi Kun San juna watarana Kuna haduwa a wajen da sai me kudi ke zuwa,idan a Abuja kake Dan Allah kasan wani Ashraf babarsa dai wacce ta Raine shi Mummy ake ce mata duk family dinsu sojoji ne yawanci,ance ai shegen Ashraf din nata ya fara aikin soja ya bar aikin ya koma business sabo da shi bakin Dan iska ne,ance ai matsiyacin ya tara kudi,naji danginsu kowa sai yace Ashraf,baka sanshi ba? Tunda Spark yake bai taba dariya irin ta yau ba,ya dinga dariya a ransa yace Allah ya taimakeni ban fadawa Jamilu ni bane Alhmdllh da Ashraf ya sanni,Allah yasa bai San nasan shi Mummy tayiwa sharri ba,Naila ta tsaya tana kallonsa Yana ta dariya

Tace ka sanshi dan iskan algungumin? Spark yace ai abokina nane, Alhmdllh ta mikawa Spark hannu tace mu gaisa ya mika hannu suka gaisa yaji wani shegen shock duk jikinsa ya dauki vibration,itama Naila haka taji da sauri ya janye hannunsa yayi wani Sanyi itama haka,tunawa yayi namiji ne da sauri ya girgiza kansa ya dawo daidai,tace zaka min hanyar ganinsa idan Allah yasa na fita daga Nan gidan, Kai wannan dan nata sai na Masa akuya,wlh sai na huce a kansa Dan iska matsiyaci,mutumin banza Allah yasa ya talauce ga mijinta ya mutu ta rasa ko suturar sawa inshaallah sai na taimaka Masa da shi da ita,jahilan banza jahilan wofi, Spark yaji ana ta Masa mummunar addua shi ba da laifi ba yace Kai Jamilu addua akewa mutum kace Allah ya shirya Ashraf.

Naila tace wlh bazan ce ba sai dai na tsine Masa na sake tambade Masa albarka mutumin banza wa ya sani ma ko a turai din Mata yake bibiya Yana can Yana sheka iskanci da mata,shi baiyi aure yayi ibadar Allah ba ya zama Dan kwararo shine turai shine kudu Lagos wajen mata,Dan Bariki, Mayen mata,Ashraf yayi dariya kamar cikinsa zai ciwo yace wait Jamilu kazafi fa kake Masa ba wani kazafi ai mun sani yaran masu kudi me suka sani in banda lalata mata Yana can ya zama Dan aci kullum sai kace Ronaldo kullum aci kwallo haka ya Maida mata,zai gane kurensa Ina Nan Ina addua Allah ya hadani da shi sai na kwankwatse Masa Hallare, Spark yayi dariya kamar ba gobe,Naila tace wallahi tun a waya zaka hadani da shi na fara rage zafi da zagi na fara rage hanya kafin mu hadu,Ba fa shi ya maka laifi ba Jamilu,Naila tace nima ai ba Ummata ce tayiwa mummy laifi ba ta kare akan Dan Umma to nima akan Danta zan kare.....
Chapter 25 · 0% Book details