Sashe 42
Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Beauty tace na yarda da ke wlh tunda kika shiga gidan Maza kika fito lafiya ba kamarar Tantiriya bace ke,Naila tace ta can ciki ma kuwa,Chikar gayu suka kira nan take ta dauka,Beauty tace aiki ya samu fa tawan,Chikar gayu tace kice na bar Kaduna na taho Beauty tace ai nace zan zo,a'a tsakani da Allah dama na gaji kin san ni dama ba wani mafadi ne dani ba zanzo kawai gobe turo min kudin mota,Beauty tace to angama,Naila tace Shegiya me kudi gashi sai gudanar da abubuwa kike da kanki,kema ai zaki kudin idan kika auri Spark,Naila tace wlh ai da na fara baje Masa ai shike nan Kuma sai arziki dama tsohon tuzuru ne kadan yake jira Dan banzan da wani blue blue eye ai yaron nan na gana Masa azaba a gidan Dan kande ,na dinga jona Masa chaji sai kiga ya dauka Yana signa,Beauty ta sheke da dariya tace saurayin da kike so ma kenan kina zaginsa,Naila tace ai Ina aurensa bakina kanin kafata,oh ashe Spark soyayya kuka kulla,Naila tace bai fa ce Yana so na ba nima ban fada ba,Very soon zaku furtawa juna ne,Allah yasa number dinsa nake so na Nemo wlh,ya gama yarda shi zai fitar Dani giyar so na kwankwanda wannan fitowar da kika ga nayi ta ba a hayyacina na fito na,ai duk cikin Mayen giyar so ne yasa nayi zuciya na fito.
Nan suka lalace suna Hira har dare sallah ce da cin abinci ke tashinsu,ana idar da Sallah Naila tace anjima zaki kaini wani aiki wajen budurwar Abbanmu ita zan cikawa aiki na kafin na bar Kano,Karfe nawa?10pm mu dawo 2am, Beauty ta zaro ido tace kawai ki shirya karki tsorata, ni sai dazu ma na tuna gidan su Batoola Ashe gidansu kusa da gidan Yaya Mohsin ne,anyway ma dai yau zan gama da auren Nan.
Beauty tace anya kuwa ba shedanu ne suka shiga jikinki ba duk ke kadai zaki wannan aikin? ga gidan yari kin fito yanzu Abuja zaki je neman fansa,ga Budurwar Abbanku gashi kince kina gamawa zaki dawo wajen matar Yayanki,Naila tace ki zuba Ido ki gani,yanzu Jallabiyya zaki samo min fara,sai dai ta babanmu,dakko min aronta Beauty ta dakko Jallabiyar Daddy dinsu,tace saura farin Chalk,a daren nan suka Nemo abinsu komai da komai,Naila tace muje ki kaini yanzu zuwa 2am idan na fito na ganki a kofar gidan kina jirana da mota,Beauty tace an gama.
Naila kayanta ta cire ta saka Jallabiyar Daddy, ta dauki garin chalk dinta a leda da cumb,da wata color kamar jini tace muje,Beauty ta shiga mota ta ja suka tafi abinsu sai ungunwar su Mohsin,suna zuwa Naila Hijab ta Kifa a kanta sannan ta fita,gidan su Batoola a bude dama daga ita sai dattijuwar babarta a gidan sai wani tsoho tukuf babanta Wanda baya gani ma sosai.
Naila kamar abin arziki ta shige gidan,Tsohuwar da tsohon suna daki,Batoola an tafi gidan suna Naila ta shige dakin Batoola da yake a bude ta turo kofar kadan.
Wani ruwan color kamar jini ta yarfa a Jikin mudubin dakin Batoola kamar jini yayi tsartuwa,ta samu dakin ta hargitsa kayan ciki tayi kaca kaca da kayan dakin Batoola,sai 10pm taji Sallamar Batoola tana cewa Hajiya na dawo ni Kam na gaji sai da safe bacci zanyi,Naila da sauri ta samu tarin kayan wanki ta shige ciki ta rufe kanta ruf,Batoola tana shugowa tana wakarta.
Ta hau cire Kaya Naila ta leko da kanta kadan tana kallon Batoola,ita dai Batoola da hasken waya ta haska dakinta ta tube har bra dinta,Naila tace ji nonon shegiya sai kace kwababbiyar flour da za ayi meat pie irin an gama tabileta a inji,a haka take so Abba yazo ya jawo mana asarar kudi,Abba idan zaka lallaba na Umma ka hakuri da shi to,ni na kasa ganewa Maza kana da mace da yaranka kana wahala wajen ci da su da kyar ake Sha amma wai ka tafi neman wata macen,nifa na kasa gane muku Maza tsakani da Allah ahhh cewar Naila a ranta,tace shegiya ji cikinta duk da gani ta zazzagar da yara duk yayi spring yayi wani dabbara dabbara ayi fatar cikin bawa ta wani cuccure ba excesise ko wacce sai dai taci ta koshi ta kwanta,Dan motsa jiki irin na ciki da akeyi Yana damewa ya danyi kyau matanmu mu basa yi.
Batoola kayan bacci ta saka ta fada Saman katifarta,Naila tace ashshaa dole Allah ya bani sa'a a kanki shi yasa na samu damar shugowa Bata azkhar sai wake wake katifar ma baza a karkade ba ko da shedanu a Kai kawai an fada Kai,ai kuwa zaki ga shedanu yau,Batoola dai Bata San da kowa ba,wutar nepa aka kawo ta mike zata kashe kwai kawai taga jini a Jikin mudubi sai lokacin ta kula da yanda aka hargitsa mata dakin,tace menene haka jini,tsoro ne ya kamata tayi Maza ta kashe wutar ta kwanta ta lulluba da bargo jikinta na rawa,ta tashi ma ta fice ta kasa sabo da tsoro,tana haka bacci ya kwasheta wurin 2am lokacin gari yayi tsuuuu kowa yayi bacci an kulle kofar gida da Naila a ciki,a hankali Naila ta fito daga Inda take boye,ta lallaba ta zare key din dakin Batoola ta bude kofa ta fito Sadaf Sadaf taje ta bude kofar gidan da aka kulle ta barshi a bude ta dawo garin chalk dinta ta shafe fuskarta da shi ta cire Hijab dinta ta jefo shi tsakar gida da chalk din da wannan kalar Jinin.
Bulalar data shugo da ita ta daga ta tsulawa Batoola,a firgice Batoola ta bude idonta taga dodo sak Aljani gashi gashin Naila ta tashe sama kamar kayar bushiya,ta canja Muryar aljanu......tana zaro harshe kamar mayya tace bamuuuu... yardaaaaa.... kiyiiiiii....aureeee...baaaaa.....ko....zakiiiii ...aure.....to.oooooo......ki.....auri wani.....mun....lamunce.....ta sake zabga mata bulalar taci gaba da magana......amma.....Banda.....Hashimu Dolo .......bazai....iyaaaaa....ciyar....daaaaa ke.....ba...muuuuuu...Kuma....muna...kaunarki.....tunda aka haifi kakanki na talatin.....muke.....tareee....dakuuu....bama....son...abinda....zai ..tabaaaaaa.....mana ke....idan...Kuma...kinki ji....zamu...bawa.....sarki jininki....ya....shanye....Naila ta nuna Jikin mudubi da yatsa...ta sake zaro harshe waje kamar karya tace....waccen....Jinin...tsohon mijinki ne.....sabo ..da ya Saba mana umarni muka aika shi lahira....sarki ..ya shanye jininsa......ki....tabbatar kin fadawa.....Hashimu Dolo....kin fasa aurensa....Kuma....kiyi gaggawar......fitar da miji cikin sati daya...kiyi wani auren.....karki bari ni....na dawo ..na samu... Baki auri wani ba amma Banda Hashimu Dolo ... yanzu zan tafi kasar Ethiopia mu asalinmu a can muke.....Hallaren Hashimu baza tayi miki ba ....sai dai tsofaffi.....Naila tayi wata dariya tace....karki bari na dawo baki da aure.....sai ta canja harshe ta koma fulatanci tafi minti talatin tana fulatanci a kan Batoola,karshe cikin tsawa tace kwanta ki lulluba ta sake tsula mata bulalar tace lulluba da bargo....wannan bulalar da muke miki.... ta karban dubu goman Hashimu Dolo ce.....da kika ce zaki anko......Bama son karya.
Batoola ta hada zufa sharkaf jikinta Yana uban bari ko wacce addua tazo bakinta karantawa take tace bazan aure shi ba wlh dama Ina da wani Usman nafi sonsa ma,Naila tayi haushin kare wan... wan ...mun sani... ba sai kin... bamu labari ba ...sannan tayi fulatanci tace zan... koma suffata ta aljanu..... Wacce Allah ya halicceni da ita kina kallona zaki mutu.....zaki mutu...
Batoola magana ma ta kasa ta rufe kanta cikin bargo jiki na bari karrrrr karrrrr, Naila fit ta fice ta kwashe Hijab dinta da tarkacenta da tazo da su har bulalar ta tafi da ita ta fice da gudun gaske lokacin Kuma yaran Dan Indo suka sake zuwa bincike suma cikin dare Neman Jamilu suna fara buga gidan Naila ta fito daga gidan su Batoola da uban gudu kamar zata tashi sama ga fuskarta duk chalk fari tas ga gashinta buuuuu.....ga farin kaya,ai suma yaran Dan Indo sai gudu suka rasa ta Inda ma zasu shiga motar tasu, jiki na bari suka bude kamar zasu ballata suka shige,Driver hannu na mazari ya kasa saka key dinma Yana hakki Yana karkarwa Yana cewa wlh bazan sake zuwa unguwar nan ba ko me Dan Indo zaiyi sai dai yayi,wani aciki yace ka ja mota dalla Aljanu ne suke wasan buya buya yau a..,driver ya fisgi mota suka fita a million,sai da suka yi nisa wani a ciki yace tunda nake ban taba ganin aljani Ido da Ido ba sai yau,Kai kaga wani gudu wannan gudun ya wuce na mutum.
Bangaren Naila tana bi ta lungun da tace Beauty tazo ai kuwa tana zuwa Beauty tana jiranta a mota,Naila ta bude kofar gaba ta fada tace muje na gama da wannan case din, Beauty sai dariya take Naila ta yayyafa ruwa a hijab din ta goge chalk din tare da yafa mayafu, Beauty tana sharara gudu sai ga yaran Dan Indo suma a kwalta kamar zasu tashi sama sun wuce a million wani yuuuuut.....Beauty itama ta Kara take gudun motarta tace ko barayi ne suka biyo su wannan gwara muyi ta kanmu,Naila tace naga wasu fa kamar suna dukan kofar gidan Mohsin dina ko su ne oho dake a hargitse nake shi yasa,suna komawa gida sai bacci kawai.