← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 98

Sashe 72

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya saketa sai ya auri wata matar a can kasar sa ta haifar masa Surayya,Rafeeqah,daga Nan sai matar tasa ta mutu, ya dawo Nigeria Abuja suka daidaita aurensu,Zeenatu tace ita baza ta koma kasar Somalia ba,sabo da Yana sonta ya tattaro yaransa suka dawo Nigeria gaba daya,sai da yaransu suka girma kaf suka aurar dasu bayan kowanne da karatusa da sana'ar yinsa,duk yaransu sabo da kyawawa ne babu wacce ta auri talaka a ciki ko wacce me kudi ta aura a garin Abuja.

Salamatu wacce aka fi sani da Mima itace ta fara aure,ta Auri matashin Soja me ji da kudi Ahmad,Allah ya Bata haihuwa,haihuwarta ta farko Khalid ta Haifa wanda shima Soja ne babba a yanzu a Lagos yafi zama tare da matarsa da yaransa hudu.
Na biyu ta haifo Nazeer lokacin anyiwa sauran Yan uwanta aure amma a cikinsu mutum hudu basa haihuwa,taso ta haifi yara mata sabo da ta basu su kyauta su rike amma Maza take Haifa,gajiya tayi ta hakura tana sake haifar Ashraf wato Spark kyakyawan gaske ne na karshe, ita kanta tana sonsa amma haka ta hakura ganin Yar uwarta Surayya ta damu da shi,kullum Ina Danta sabo da Spark kullum sai tazo gidan,kullum tana siyo Masa abubuwa,Mima tana yaye shi ta kaiwa Surayya har gida tace gashi nan ta bar mata tsakani da Allah har abada ya zama nata,babu ruwanta Kuma ko shiga safgarsu baza tayi ba.

Surayya sai murna amma Sam mijinta Alhaji Aliyu baya son rike Dan wani shi,kawai sai ya tsani Spark,tun Yana yaro har Spark yayi hankali yasan Mijin Mummy baya kaunarsa,gashi Mummy ta shagwaba shi sabo da haka ma Yana gama secondary ta dinga koya Masa business iri iri Kuma Allah ya taimake shi din,Makarantar Soja ta sashi sai da yayi nisa yace bazai iya ba shi,a haka tana lallaba shi ya daure har ya gama ya fito a Soja sak,ana turashi yaki wata kasar yayi resining dama ba so yake ba ya bar aiki,dama shi ya gaji Yana so ya dinga tara sumarsa da shanawa duk babu kullum aiki aiki duk yayi duhu zai lalace yace bazai iya ba,baza a canja Masa halitta ba haka kawai akan fatararsa ta lalace gwara ya zauna da talauci.

Yo Mummy ta gama shagwaba shi baya Jin magana,gashi da mugun ra'ayi idan ya kafe a Abu sai dai a kyale shi,ba a Masa dole shi,ya taso ba abinda yake nema ya rasa, Alhaji Aliyu Kuma baya sonsa tun asali,zagi hantara duk Yana Masa har ma ya daina jin haushi, Mummy kasar waje ta turashi yayi masters akan business,dama tun Yana secondary take biya Masa kasar waje tana kaishi, Yana zuwa hutu can ya shakata har ya girma kullum a tafiye tafiye yake kasa kasa baya rayuwa sosai a kasa Nigeria.

Gashi da Nasibi a rayuwa,tunda suka taso su ba musu fada duk abinda kayi daidai ne,su kansu su Mummy iyayensu sunyi duniyanci kadan, daga baya suka tuba,basu basu wata tarbiyyar kirki ba bare su bawa wani.

Spark kullum kudinsa na bunkasa ganin mijin Mummy ya tsane shi sai ya Gina gidansa katafaren kawai ya koma can,Alhaji Aliyu da kansa yace Spark ya daina kulashi sabo da bakin ciki yaga yaro ya girma a gabansa yazo ya fishi kudi.
Mummy suna yawan zuwa asibiti akan rashin haihuwa amma sai ace kalau suke mijinta ne da matsala,sannan baya iya biya mata bukatarta,a haka ta hakura take zaune da shi,ya Sha gwada nemo aure Mummy ce take ruwa da tsaki ta Hana auren ta hanyar masifa da tijara .

Tunda taji ance ita kalau take kullum suna yin fada da Aliyu zata Masa gorin haihuwa tace hakuri take alfarma take Masa,ga shegen son kudi duk family din su Mummy haka suke su da sunga me arziki to shine nasu,sannan duk kusan kangararru ne basu da kyawawan halaye na iyaye mata,shi yasa tunda mijinta Taga lallai aure zai kara da gaske Taga ita bata haihu ba,ta ya za a kawo wata idan ta haihu ita shike nan baza ta samu gado ba,akan gado taga gwara ta kasheshi.

Tana tunanin ya zatayi idan ta kashe shi ta tsira kar a gane itace sai katsam Jamilu yazo me magani dabara ta fado mata ta aikata.

Bayan Mima ta bada Spark sai ta sake haifo namiji Misam ta dauke shi data yaye shi sai ta bawa Dan uwanta Namiji Uzairu lokacin Dansa Daya a duniya tal wato Kamal, ya dade da aure Kuma ,sai ta Kara Masa da Misam,bayan an bashi Misam sai Kuma ya Kara aure duka matansa suka dinga haihuwa sai da suka haifar Masa yara takwas Kamal shine babba shine Kuma mate din Spark,abokin Spark ne tare sukayi school,amma a kasar waje Kamal shi Engineering ya karanta ya dawo Yana aikinsa Yana samun kudi,ya Gina gidansa shima sannan Yana da budurwa har an kusa biki ma.

Misam shi matar Uzairu ce bata kaunarsa,idan mijinta baya gidan sai ta dinga dukan sa tana zagin sa,idan mijinta na gidan ba Wanda take so kamar Misam a gaban miji,Yaranta sune yara su take wa fada da tarbiyya,Misam ko me zaiyi baza ta yi Masa fada ba, har ya taso ya girma ya fara yawon dare amma bata taba yi Masa fada,tana kallo Uzairu Bai sani ba Idan ma taga zai gane sai ta boye ta kare zancen kar ma ayi Masa fada ya shiryu,har Misam yayi nisa a neman mata sannan Kuma Kamal ya gaji ya fadawa Abbansa Uzairu,Uzair hankalinsa ya tashi an bashi Amana.

Yaransa kaf gasu Nan a shirye amma na wata an bashi ya lalace a hannunsa sabo da rashin kula,ya dawo lallai sai Misam ya shiryu Misam yace kayi sake Baba da baka bibiyar Amanar ka, ka manta matarka azzaluma ce kawai ka barni a hannunta ba ruwanka da bincika me ake min Ina ta nuna Maka ka gane kaki sai da na lalace, yanzu bazan daina ba nasan mata nayi nisa,kullum ana bata min rai ba dole na tafi Inda zanji dadi ba,Ba irin nasihar da bai yiwa Misam ba yaki ji,sai addua ya koma a dalilin haka ya saki uwar gidansa gaba daya Kuma yaki dawo sa ita har gobe.
Kawaici irin na Mima Bata taba zancen ba tasan Kuma me Misam keyi, tana yi Masa nasiha ma amma bata taba zancen ba a wajen wasu, ko da kuwa ace danginta ne, tunda ta bayar ta Bada tsakani da Allah, babu bincike ya zama Danka duk da tana Jin ciwo tasan ana zaluntar Misam a gidan amma ta hakura.

Bayan Misam duk sauran Yan uwan suna haihuwa su har su Babar Wahida,mace daya ce Bata haihuwa itama, ita Kuma uba daya suka hada da su Mima, Yan ubanci yasa ta hanata Dan ita,Ahmad Mijinta shine ya dauki Rafeeq da hannunsa ya bawa Yusra itama yace ai babu dadi kin bawa Wanda kuke uwa daya uba daya kin Hana waccen Dan Kuna yan Uba,Mima tace ni wlh banyi niyyar Bada Rafeeq ba duk yarana kyawawan ciki duk na bayar dasu,yace kika Bada Spark ma wato ita waccen Dake Yar uwarki ce uwa daya uba daya,me yasa yanzu zumunci ba ayi Dan Allah? ba kara ba komai, kowa Keke da Keke wlh ni na bata Rafeeq ya dauke Rafeeq ana yaye shi ya bata kyauta.
Duk Wanda suke uwa daya uba daya da Mima sai da suka ji haushi.

Shike nan Mima ta tsaneta sosai sannan tayi mugun sawa Rafeeq Ido,ta takura Masa har ya girma idan yaje gidan sai ta dinga tambayar shi me da me ake Maka? Kana cin abinci? Bata dukanka? sabo da haka Rafeeq ya daina zuwa gidan ya tsane su gaba daya har su Khalid ba ruwansa da kudinsu da kayansu,shi yafi son wacce ta raine shi, akan a zageta gwara a zage shi,ba Wanda ya isa ya taba Masa wacce ta Raine shi,ita Kuma Yusra mijinta akwai kudi amma ba wani sonta yake ba,aurenta yayi sabo da sha'awa tana Masa biyayya iyakar iyawar ta amma baya Gani,ya tsaneta ma sai auri saki ya iya, Dake shine baya haihuwar, gashi da mugun son kudi Yana da kudi amma baya ciyar da iyali,kullum gidansa garau garau ake ci a haka ma da taimakon Rafeeq,Yusra tana Shan wulakancin da namiji tayi tayi ya saketa yaki Kuma Bai fasa wulakantata ba,duk abinda tayi Dan ta birge shi to fa bata birge shi, shi tsabar mugunta ma baya so wani ya taimaka Masa a gidansa amma shi zaici me dadi a waje zai sa suturar da yake so sannan zai hau motar da ya ga dama amma banda iyalinsa,Rafeeq ganin haka ya fita shirginsa,Spark ne ya dauki nauyin karatun Rafeeq da komai nasa,da kasar waje zai kaishi yace a'a ya barshi a Nan Nigeria sabo da Mama babu Mai taimakon ta sai shi, Spark yace ya Fadi sana'ar da zai iya ya bashi jari,yace ai shi joint za a bude Masa,anci dariya aka bude Masa Kato me kyau da ma'aikata da komai shike nan ya zama Baban shawarma joint,ga school dinsa Yana zuwa private da hostel dinsu sabo da tsakanin su da gida akwai nisa shi yasa.

Mummy Kuma tunda Taga Yana samun kudi Yana taimakon Yusrah mamansa wacce ta Raine shi sai haushi ta sawa kudin Rafeeq Ido,sai ya tara kudinsa a accnt sai tace lallai sai yazo ya bata kudi,ta dinga ta karbe kudin ta hanashi gaba ta hanashi baya,ko yaushe a Dora jari Spark yake watarana Kuma Misam Yana bashi,Khalid ya siya Masa mota amma ya siyar ya Dora jarinsa shike nan suka yi fada da Yan uwa Dan me zai siyar da mota ya Dora jarin Shawarma,Sai ya daina kulasu du sai yaga dama, ya fita harkar kayan su, ko an bashi baya karba tunda ana Masa gori a dinga sashi Yana yin abinda baiga dama ba.

Mima kanta sai Kara ta kaiwa Spark ta Rafeeq ya daina kula su gashi gashi,ya same shi ya Masa fada shine ya Dan sakko,amma idan ba Spark ba da Misam ba ruwansa da sauran,shima tarbiyyar tasa da gyara sai dai bai Kai sauran lalacewar ba.
Chapter 72 · 0% Book details