← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 98

Sashe 19

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna ji suna gani aka Masa sharrin kisa ta karfi tare da yanke Masa daurin rai da rai shima a gidan yari.
Spark yaga masifa ana kawo shi ciki gidan yari Naila ce ta fara ganinshi tace wow, sai data tsaya ta kare Masa kallo Yana wani gadara da kyar yake tafiya fuskar nan a hade ba mutunci dama ya lafiyar Kura bare tayi zawo, sai kallonsa akeyi sabo da kyansa da gadararsa ana ganinsa an San Dan gidan wani kusa ne a kasar, Naila ce ta fito tana tafiyar Yan daudunta tabi bayansa tana kiransa tace wannan zaka dace da Daudu,ni Kam nayi budurwa,ta fara kiransa da Asabe....Asabe....ko Tabawa ce ne? Tabawa...ahhh Ashe ba tsohuwa bace sannu ko sunanki Kamariyya? Jin Muryar mace sosai yayi mamaki ya juyo ba shiri,gashin kawai ya kalla yace a ransa Ashe Dan daudu ne,Naila ce ta katse Masa tunaninsa da cewa Kaiiii gaskiya kina kama da Lady Gaga, jar Uba I love you, shike nan ga suna na Yan gayu Iklima ai yafi?,ni sunana Dahara,wani takaici ya kama Spark,Sam shi ya tsani mutum dandaudu wani tsanar mutum yake yi,ga wannan gaba daya suffar mata gare shi, Naila kuwa ta jera dashi taci gaba da cewa,Sunana Dahara sunan ya samo asali ne tun Ina karama Allah ya sa min yin tsarki,kullum ni dai na dauki buta nayi in tsarki shine aka canja min Suna Dahara, Kuma fa Ummata sanda tana da cikina ance Bata iya rike fitsarinta shine kullum ta dauki buta shine ana haifo ni nima kullum da buta a hannuna dole aka gaji Dani aka sa min Dahara.

Look ni ba wani abu nake so ba,kawai abokina zaka zama sabo da ba karamin girma bane a ganni tare da Kai,kawai ma ace Ina Dating naka ai ni na zama kadara, duk Inda ya sa kafa Naila tana biye da shi,mutanen gidan sai daga mata hannu akeyi a matsayin Dandaudu ne kowa sai yace su Jamilu Terror anyi sabon kamu, Naila tace harka ce ta Uhmm humhum,hankalinta ta Maida wajen Spark tace to shike nan da sunanka zan na kiranka, ya sunan naka? Ko kulata baiyi ba, ganin Dandaudu y matso kusa da shi hannu yasa ya ture Jamilu,ai Naila rikicif sai gata wanwar a kasa, lebenta na kasa ya fashe kadan,Mamaki ya kama Spark namiji guda daga Dan ture shi yayi wannan uban faduwar haka,Bai San macece ba,a ransa yace wannan ya gama kashe kansa ya zama macen gaske,wait tsayawa yayi Yana tunani da yasa hannu a jikinsa yaji Laushi haka,wani sabon mamakin ya dira a zuciyarsa,kallon jamilu a kasa Yana goge bakinsa, haka ya wuce bangarensa na masu kudi wajensu daban dakinsa shi kadai harda tv da fridge harda kujeru sai dai rayuwa kawai a waje daya musamman ga namiji akwai wahala.

Naila tashi tayi da kyar ta goge jikinta tana dingishi ta koma dakin su Alaramma Jilani,samunsu tayi suna Hira ai suna Ganinta ta shiga gaba daya suka jawo Qur'anansu kowa ya bude ba shiri,dariya suke Bata.

Gefen bed ta zauna Malam Garzali ya dago Kai ya saci kallonta ai kuwa karaf suka hada Ido Naila ta kashe Masa ido daya,da sauri ya duka karatunta Yana yiwa sauran magana kasa kasa yace kaiiiiiii wallahi Ido yake kashe min Kuma ya birge ni,Malam Garzali shima yace nima haka zuciyata

Naila Hanata akayi shiga indai ba da izinin me kudin ba to ba Wanda zai shigar musu sai da izini,shima ba kwana ba idan da kwana to Wanda ya shiga shima sai an biya Masa kudinsa daban,yini ma sai an biyawa mutum zai yini a wajen,bangaren masu kudin ma shi ba wani me kyau can ba kawai Dan akwai kujeru da fridge ga toilet ko Ina tiles sannan har wanki ma da guga yi musu akeyi zasu iya dauka a cikin Yan gidan yarin suna biyan mutum hakkinsa Yana musu.
Spark da wayarsa da komai amma ya canja layika gaba daya sai in shi ya Maka magana sannan kasan shine,in banda Kamal da Rafeeq da ya nema ba Wanda ya nema sai Mummy dinsa me kaunarsa itama ya kirata amma sauran ba Wanda ya kira sabo da duk sun yarda zai iya kisan Kai.

Spark bakin ciki ya taru ya Masa yawa ya rasa Inda zai sa kansa,Naila kuwa tsabar bala'i sai da ta bada cin hanci aka barta ta shiga dakin Spark,tace wato ita duniya dai ko Ina me kudi yake akwai banbanci a lahira ne kawai kowa zaici kwal ubansa Kai daya muke, ranar ba wani me kudi,palon ba kowa bedroom ta shiga a zaune ta hango shi ya hada Kai da gwiwa Yana hawaye shi daya.

Naila tana shiga a hankali take sanda,ya ganta tun shigowarta,a ransa yace wannan Dandaudun ko maye shege tsinanne,Naila da karfin hali zama tayi a gefen gadon nasa, cikin Muryar Maza mazanta da take amfani da ita tace Allah sarki hakuri zakayi kaddara ce,wallahi ka saki ranka idan sharri aka Maka zaka fita watarana,Allah zaka fadawa kawai,gidan yari idan ka saki ranka akwai dadi ma itama wata rayuwa ce ta musamman Kuma zaka yi nishadi,ka kwantar da hankalinka ka saki ransa idan sharri aka Maka uban Wanda ya Maka sharri yaci... dan me..Kai Dan kut...nace durun....kai...duk bata karasa zaginba idan ta dakko sai ta saki ta kama wani.

Ka tsaya kana kuntatawa kanka kana namiji aradu ka fito a dama da Kai,karka bari kanka ya kulle,gidan yarin bata rago bace aradun Allah,gidan Maza malam anan zaka tabbatar da namiji ne kai, anjima kadan yau za ayi gala rawar solo ka fito kayi nishadi karfe biyar za a fara har dare, Spark a ransa yace iyyeee a gidan yarin? Bai San a fili ya furta ba,Naila tayi dariya tace ai har koroso kullum sai anyi da wasanni kala kala kazo muje na nuna Maka komai ka huta da bacin rai, tunawa yayi da Dandaudu yake magana sai ya bata ransa ya daure fuska,Naila tace wasa nake Maka ni ba Dan daudu bane kawai Ina kama da mata ne shine Yan gidan yarin Nan suke fada min haka,amma wlh ni ba Dan Daudu bane sunana na gaskiya Jamilu,Spark ya Kalli Jamilu wato Naila sosai,murmushi ta saki a ransa salati ya saki kawai yayi shuru shi Kam wannan mata Maza ne gaskiya bai yarda ba sai dai Matamaza.

Tashi tayi ta fice,tana fita ta koma wajen su Goje har hudu tayi taje tayi sallah a boye malaman dakinsu jam'i baya wuce su,suna fita take yin tata kafin su dawo, suna mamaki Bata zuwa jam'i iya wuya a daki take sallarta,wanka tayi a toilet din ta shirya tsaf ba Wanda ya taba ganin jikinta,kaya ta canja suma sai masu kauri burma burma na Maza,harda shafa turaren da Scoler ya bata sai wajen da ake musu wasan Solo lokaci zuwa lokaci,Yan solo sunzo harda Yan film an kafa kida an fara cashewa kowa ya zauna ana kallo wasu suna ihu suna liki,sai ga Spark kamar ba a gidan yari ba ya Sha kana Nan kaya sai shining yake dake sabon zuwa ne gashi kyakyawan gaske fari,ga kyan sura da diri,ga kwarjini da cikar haiba,Jamilu abokinsa ya fara dubawa a wajen can ya hango Naila zaune a gefe daya bata shiga gwamitsin kartai,kujera ta nuna Masa a gefenta,wasu munafukai harda gulma dama tunda naga kalar guy Nan nasan shima Yana harkar Daudu,Terror an samu Dan uwa,Spark hannu ya mikawa Naila yayi sallama,Naila ta kalle shi kawai ta basar ta share,Yan Solo suna cashewa wata Yar bariki har da zuwa zata rungume Spark Naila tace ke dalla matsa na saka miki guba ki shaka ki mutu bar Nan Dan uwarki tana zaro ido ta koma Yar Zara,tana zare Ido tana magana ta Maza ta Yan Zara,amma duk da haka mace sak.

A hankali Spark ya dago Kai ya Kalli Naila,dariya ta kusa kama shi,a ransa yace ikon Allah namiji ta karfi sai ya koma mace to naga Dan ubansa ta ya zai canja Banana dinsa,ai sai ya yanketa kawai idan ya isa,shi kadai Yana tunani sai ga scoler yazo Yana rangwada yace da Naila Tantiriya ta? Jamilu Naila ya kalle shi yace Na'am my love Ina ka shige ne Ina ta missing naka.

Dandaudu Scoler yace ahayyeeeee Yana tafi yace Dan ma har yanzu kinki yarda kiji dumin jikina,Naila tana shagwaba tace ai karka damu Darling tana so tayi kuka,Scoler ya dafe kirji yace na shige su ni Yar Nan karka bari hawayenki ya zubo tawan mene ne? Jamilu Yana rangwada yayi fari sannan yace ba Kaine ba sabo da Allah haka ake saurayin kaki zuwa zance bare ko kudin zance ka bayar gashi Dan liki ma bani da kudin yi,Scoler yace Dan Allah daina fada jiya aka turo min kudi ungo yasa hannu a aljihu ya zaro Yan Dari bibiyu na dubu biyu ya mikawa Naila,badan yau Saturday ba Alqur'an sai na rungume ka cewar Naila,amma anyi rashin sa'a yau cikar shekarar kakata ta wajen uwa goma Sha biyar da mutuwa,ranar bakin ciki ce sai nan gaba.

Scoler yace kiyi hakuri amma gaskiya kakarki ta cuceni data mutu ranar asabar ai sai ta bari zuwa lahadi Sunday yanzu je kiyi liki,Yan wasan kwaikwayo suna ta uwar rawa a fili, Naila ta mike tace zaku ci ubanku sisi bazan lika muku ba,caca zanyi muku,ta wuce ciki filin rawar,Dj harda fadar sunanta ana ta cewa Jamilu Tantiriya Allah ya tsare mana Kai,Naila ita da kanta dariya ta kamata ta dinga dariya,mazan Nan sai kallonta suke ana ta son Jamilu sai kuskus ake yi.
Chapter 19 · 0% Book details