← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 98

Sashe 52

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya yayi yasan yarinta ce kawai,yace to wacce irin kulawa za a min? Beauty ta danyi kasa da Kai ana rufe fuska a hankali tace sai nazo gidan bazan fada maka ba yanzu karka manta hularka sabo da farin ciki, yace ke kin san me akeyi ne ma sai dai na koya miki,girki kika sani da shara,Beauty tace me ka Mai dani yarinya ko me?, Yace ai ke gidanki daban Daddy yace ya bani,tace no da Aunty zamu tare ai gidanka ne ba nawa ba karka ga wai ubana ne ya baka kace wai nawa wlh ba nawa bane,ba ruwana ban San alakarku ba, yanzu ya hada mu, kaga kuwa duk abinda ya Maka badan ni bane,idan haka ne ma ka Maida ita Uwar gidanka can ni a gyara min Wanda take ciki ai nasan gidan har kofar gidan na taba zuwa tare da Naila gidane me kyau wlh.
Mohsin sai yaga hankalin Beauty sosai yaji ta Kara shiga ransa Kuma ta birge shi matuka.

Kamar sun Saba haka suka dinga hira sosai sai wurin magriba yace zai tafi,sai lokacin tace ban gaisheka sosai da ladabi ba, na manta,dariya suka yi yace a haka za a kula da mijin? tace sai naga kamar Naila ce mun Saba hira,karki fada mata kinji ki bari ta Sha mamaki,Beauty tace to shike nan ta rakoshi,ya hau machine dinsa Wanda yasha wanki,ya wuce.

Beauty ta koma ciki tana ta murna tayi Miji itakam, Chikar gayu ta kira tana bata labari,Chikar gayu tace inye yan mata an dace, Yayan Naila ne tab to ya kika ganshi? Beauty tace haduwa za aci uban love,Allah ke? Chikar gayu ta tambaya,tace hmm Yana da mata wai Ashe,Chikar gayu tace to mene Ubanta zamuci kawai idan tace zata mana iskanci,Beauty tace ah zata karba matukar tace baza a zauna lafiya ba to sunanta sakakkiya domin tabarar da zanyi a gidan nan ta baci shi yasa nake so a hadamu gida Daya taga salon Yan gidan yari,kyankyasar gidan yari,Chikar gayu tace ke dai bari har naji ma ni ta fita an sake ta,ai baza ta iya zama dake ba,Naila ta bani labarinta tace Dan iskanci wai idan taga dama sai ta bude nono a tsakar gida tana yawo haka,Beauty tace Ashe Mohsin zai Sha kallo nonuka hudu a tsakar gida yaga ta kansa,rabu da ita ai sai mu bude masa hudu rigis,tana budewa zan bude nima Abu kowa da nasa,Chikar gayu tace yawwa mu da muka iya girgiza shi,Ashe gasar Nan tamu zata yi rana oh duniya kinji kishiya dai dai mu,suna dariya Beauty tace ai yanzu shuru zanyi kamar saliha sai na shiga zata ga karuwanci kin san Allah dama ta tanadi kudin mota domin ta kulla da yaji kenan,ita da yaji sun daura kawance,iyayenta sai sun gaji da maidota gidan miji,Chikar gayu tace ki tabbatar an hadaku gida Daya dama Naila tace bata da mutunci,idan ta miki kawai design her face,Beauty tace yawwa mu baza mu cuceta ba sannan ba ruwanmu da ita amma tana fara iskanci a hankali zan jawo Dictionary Dina na rashin mutunci chapter by chapter zan dinga budewa a hankali Ina koya mata Ina koya mata a hankali sai ta haddace shi tsab.
Chikar gayu tana dariya tace yawwa tawan ba wani shege,a nuna mata lallai fa munje gidan yari mu ba irinsu bane da suka zauna a iya gida,shi yasa Naila take birgeni,ai ba a Kai banza gidan yari cewar Beauty, taci gaba tace dama nifa yanzu kadan nake jira abokin mutuwa nake nema,na Dade bamu fafata da wata ba,Chikar gayu tace ke dai bari rashin fada da tashin hankali Yana damuna,na gaji da hakuri kowa salihi a gari na rasa Tantirin da yazo daidai Dani,daga Naila sai ke sai ni haba mun wani zama kawaye bama fada kullum sai mutunci a gaskiya mutuncin yayi yawa.

Gidan yari Washer ne Wanda ya Rabauta da pant din Tantiriya ya fito daga wanka sanye da wandon Naila da tabarwa Malam Sharu a haka daga shi sai pant din Naila ya fito Yana karairaya ya nufi dakin su Malam Sharu,suna karatu ya shiga tumbur sai pant Yana karairaya yace Salam bayin Allah bakwa gajiya ne, kunfi kowa karatu amma Yan banza ma sai ficewa suke daga gidan suna barinku bayin Allah,ku dinga sararawa kanku Dan Allah,wlh ni tausayi ma kuke bani dan dadin duniyar nan bakwa ji,ya kuka ganni?nayi kyau Dan Allah? Allah dai yayiwa Jamilu albarka kaji dadin da nake ji kuwa,su Malam Sharu suka Kalli washer suka ce Allah ya shirya.

Yace Ameen Yana fari yace tunda nasa wandon Nan nake kawowa,kayi asara Malam Sharu daba saka ba,yo yanzu Nike Nan a wanka,Ina sakashi kullum sai na jini a harka wlh tallahi abin yayi,daga sashi nayi wanka ya Kai biyar,Scoler ne ya shugo ahhh washer me zan gani gaskiya kinyi kyau ahhhh Dan Allah in ka gama dashi Ina son kwance,Jamilu guda ta saka a bar so a bar kauna Ohhh ni yasu wai idan ka gama wallahi Ina son kwance nima na kwashi tabarakina.

Washer yace akwai wani kamar a kayan nata duba ka dauka kaima kaji ,Scoler ya sake bude kayan Naila Yana bincike ya dakko wani pink yace kalar ta birgeni irin tamu,wlh sai naji wani rassss nima bari naje na chake,ya sake daga pant din yace nida falmaran haba sabo da Allah wannan duwawun na Jamilu ai dole sai katon wando oh,lallai sai kace bodin mota,juyawa sukayi tare da ficewa.

Suna fitowa suka hadu da Goje ya kallesu suka ce Goje Dawa Dawa uban Dawa, kaga Scoler ma ya Rabauta,Goje yace shashashu ana neman wajen da kansa kun kare a abinda ake sawa a wajen, Kuna hauka,au Baku hakura da Jamilu ba har yau? Goje yace never wlh sai ta dawo gidan nan ai mun kafa mata kahon zuka,ita muke so,Kuma kullum a cikin fafutukar nemanta muke sai mun samota yanzu ma mun sa anyi gabas ana nemota,Dariya Scoler yayi tare da furta wata sabuwa inji Yan chacha Kun dorawa kanku aiki,ke kiji Dan Allah washer wai sunyi gabas nemanta,Washer yace to Allah yayi yamma da Naila su suyi gabas din.

Bangaren mata kuwa Mama data kashe Asmau Bata Saba da wahala ba amma a nan gashi nan ta shiga wani hali,ta rasa Inda zata saka kanta,ga Yan matan ciki basu da kunya,duk da Yan uwanta sun sa an maidata layin manya vip amma Ina sam,duk ta rame tayi duhu,ga sauro Idan dare yayi haka zata fito tayi ta birgima tana susa ita ga Yar Madara,akwai wata matashiya a ciki ta sa mata ido kullum da dare idan ta fito ta ishesu da wayyo sauro ta kwanta tana ta malelekuwa a kasa sai yarinyar tazo tayi ta Sosa mata jiki tana waka a Sosa...a Sosa..har wasu suma ko wacce tazo wucewa sai ta Sa hannu ta yakushi Mama tace a Sosa sannan ta Kara gaba, ayi ta dariya,har suna suka sa mata Mama Comedy, tunda taga haka ta daina wannan iskancin bata fitowa.

Umma kuwa tunda ta haihu yaranta idan suna gida suke yin komai,idan Kuma suna makaranta Hashimu Dolo ke yi,yau ma da yamma ba kowa a gidan ana saura kwana biyu suna,sai shi sai makwafta da suke ta shugowa,shugowa yayi wasu mata su biyu suna zaune suna hira ya kira Umma da Yar Inna me kike so yanzu a dafa ruwan shayi ko kuwa kunu zaki Sha? Umma tace a'a Abban Mohsin ruwan shayin dai kunun kanwar nan na jiya daka dama min yayi zafi da yawa,yace haba Yar Inna yo ai sai ki fada nazo na fifita miki,su dai mata Yan barka suna Shan kallo wasu ma sabo da Hashimu da Umma suke zuwa gidan wai su a dole masoya, ita kuma Umma Dan ace ta mallake mijinta take ta wani goyawa Hashimu baya,ba a dade ba Hashimu ya kawo flask na ruwan zafi ya ajiye a gefen Yar Inna yace Yar Inna gashi,ya duko yace Yar Inna wanka fa yanzu zakiyi a hada ruwan ko sai anjima?

Umma ta shagwabe tace ni sai anjima kar a dafa yanzu,Abba yace sorry sorry Allah ya kaimu,ya fito ya zubo mata danwaken da yayi a plate ya kawo yace a kawo Maggi? tace barshi haka,yazo ya dauki new Baby tare da shigewa bedroom da ita.

Matan da suke zaune suka ce wlh ke dai Kubra kinyi dace ki godewa Allah,irin wannan mijin ba kowa ke samu ba,sai kace Jinin larabawa soyayya bata tsufa,Umma tace to kana zamanka da mijinka lafiya ya kawo biyar ka kawo goma ba a San ya kuke zamanku ba mutane a dinga cewa ka mallaki miji,dariya suka yi suka ce ai gaskiya ce kin mallaka shi Kubra.

Abba yana jinsu suna zancen mallake miji,yace a'a na tuna da Batoola wlh aure zan Kara fa Ashe, ya tuna ya fito ya mikawa Umma yarta yace riketa zanje wajen Batoola ni wlh sai yanzu ma kuka tuna min zan Kara aure, dariya ta kama matan nan amma ko ba komai Umma tana shanawa duk da dolancinsa,mutum zai Kara aure amma ya manta ma,suka dinga dariya.

Mohsin kuwa sau uku Yana zuwa zance wajen Beauty ba Wanda ya fadawa,sun shaku sosai da sosai,wani mugun kaunar juna suke kullum baya shiga gida da wuri sai yasha soyayya a waya da ita,sai yanzu yake Jin kamar ma yanzu ya fara soyayya a duniya Beauty ta tafi da Imaninsa,ko ta Hanan baya yi,kullum suna manne a waya da Beauty,haka Idan Yana wajen aiki,Hanan dai Taga duk ya canja mata amma bata taba Jin yayi waya da wata a gidansu ba,ta rasa gane kansa Sam sam,gashi da Yana yin Sallar Isha yake dawowa yanzu ya daina,watarana kuma sai taga da yamma ya dau wanka na gaske ya fice,shi Kuma Mohsin mamaki zai bata sai an kusa bikinsa da Beauty zai fada mata,ganin haka Hanan ta fadawa babarta abinda Mohsin ke mata yanzu,tace zanje gidan Malam sani na karbo miki rubutu kin san dangin Miji idan suka saka gaba to sai sun ga bayanka.
Chapter 52 · 0% Book details