← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 98

Sashe 94

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yaje ya kawo mata ta karba tana godiya,zama yayi a gefen bed din,tace dama zan kwanta ne ai zaka iya fita,yace Dan Allah wata sura nake so ki Kara min,tun rannan nake so a biya min ga malama yanzu please.
Ikhram tace okay dakko Qur'anin,Yana fita ya dawo Yace na manta na kaishi gida jiya,Ki koya min Salatul fati ni Dan izala ne zan dawo darika,tace ai ni Yar izala ce yace Ooooh....to shike nan amma dai ai bana bar bakuwa ba haka kafin mama ta dawo,Bargo ta shiga tare da lullube jikinta iya kanta kawai ake gani da fuska tace zauna to,ya zauna tuni harda Kara gyara zama.

Chika tana gida bayan Naila ta fita ta shirya ta fita zata Nemo abinci,tana tafiya a kafa Dake wajen ba Nisa sai da tazo cikin mutane kawai taji ta a kirjin mutum an rungumeta Kam cas a kirjinsa kamshin kawai taji tasan Misam ne,sakinta yayi ya Kara gaba ko irin ya nuna alamar ma ya taba mutum baiyi ba tana kallo ya shiga mota ya Kara gaba,tace yanzu haka hotel zai je wata karuwar ya siyawa abinci,juyawa tayi gida ta dakko motarsa Dake hannunta ta nufi hotel din,binsa tayi a baya har ciki taga ya shiga wani room daban, Dan wayo tayi ta kama daki a hotel din Dan ya samu shiga Inda take so,tana zuwa bayan an kaita dakinta ta fito ta nufi Inda taga Misam ya shiga,knocking tayi ta Murda handle din ta shige gaba daya Allah yasa ba key,tana shiga ta ganshi shi kadai Yana cin abincin da ya siya.

Kallonta yayi da mamaki yace babanku Yana gaishe ki,tace wa? Abbu Yana gaishe ki,mamaki ya kamata tace a Ina kasan haka muke cewa Abbu? Yace zo ki zauna ni sai na Baki tarihinki kaf kiji har dalilin shigarki gidan yari,tace ban yarda ba ta karasa ciki ta kulle kofar,yace ke wlh karki zaton karya nake zuwana gidanku Uku,Nan zuwa kika yi ki kureni Ina iskanci,baza ki taba kamani ba Allah Yana rufa min asiri,zauna kiji ba abinda zan miki,naje gidanku Chika nasan tarihinki Kuma naji tausayinki,Hannunta ya rike yace zaki aure ni? Kina so na a haka? Chika tace Allah ya kiyaye na auri me neman mata,ya zakiyi dani na zame miki ciwon Ido,ya jawota ta zauna a gefen bed yace Dan Allah ki aure ni kinji,Chika tace a'a,why? shuru tayi yace Ina sonki,taji dadi amma tayi shuru ta mike tace tafiya zanyi,yace Dan Allah ki kwana a nan,na miki Alkawari ba abinda zan miki,tafiya zanyi akan me zan kwana sai kace Karuwa,Key ya sa ya zare yace ba abinda zan miki fa,Ka bude min na tafi,yaki budewa har ta gaji da rokonsa ta zauna a kujera.

Hanan kuwa yau kwana ya dawo kanta,ganin Bai dawo gida na sai 6pm sai haushi Yana shugowa ta fara korafi da ace Amarya ce ai tun 2pm kana gida baka fita ko Ina amma Dake kwana nane shine kazo min gida sai 6pm,kwanciya yayi a kujera ya gaji ya Sha aiki har ma zazzabi yake ji,yace Baki ga bani da lafiya ba ma,ohhhh ta haka ka bullo wato sabo da karka min komai zaka ce baka da lafiya,sai a ranar kwanana rashin lagiyar zata zo wlh baka isa ba,sai ka jiyar Dani dadi ko mutuwa zaka yi,bacruwana da cutarka.
Mohsin yace me yasa Baki da hankali ne wai kin haukace gaba daya,ka dai haukace amma ba ni ba,tana Masa abinda yafi wannan ya hakura ma amma yau sai ta fada a akasi yace na sakeki Hanan,saki na yanzu biyu kenan igiyata biyu ta kare sai ka cike min ta uku na huta gana daya da jaraba,dama ni aurenka ya isheni,auren jaraba,annoba dangin tsiya dangin jaraba,yace na sakeki saki biyu,dama nayi Daya da farko na sake ki saki biyu yanzu igiya ta kare babu aure tsakanina Dake har abada,ya mike yaja tsaki ya fice.

Lokacin Kuma Hanan ta fara tsala ihu tana rusa kuka,Beauty har tayi addua ta kwanta taji ana knocking,fitowa tayi ta duba sai taga Mohsin ransa a bace,tace lafiya? Yace matsa na wuce,tace ba kwana na bane ka sani yau,bazan dauki hakkin wata ba,tureta yayi ya wuce bedroom ya kwanta,ta dame shi da sai ya tashi ya tafi,yace Hanan babu,fam fam na sake ta gaba daya karki dame ni,Beauty ba kunya ba sai ta danna wakar barmani choge ba a waya,tana mulamulan duwaiwai kaga na goggoron dake duwaiwai tana tika rawa,ba sharing ba sharing...ta kashe ta fada jikinsa ta rungume shi,tace ya naji Jikin zafi....

Abba ne ya fito Yana tafiya wata galleliyar mota ta ubansu ta tsaya a saitinsa tare da sauke glass aka ce Hashimu Dolo ,wa nake Gani kamar abokina Hashimu Dolo, Hashimu ya Kalli me motar sai ya washe baki yace Jauro baron mata? Jauro baron mata daga Ina yaushe kayi arziki haka,Jauro baron mata ne ya fito suka rungume da Abba suna murnar ganin juna,yace ya iyali? Abba yace Alhmdllh Alhmdllh Kubra Allah yarda Kubra tayi karko a gidan miji itace dai Daya jal har yau kamar filar machine,Jauro yace yaranka nawa Hashimu? Hashimu yace guda shida,kwana nan na aurar da Yata,yace Allah Hashimu,yace wlh ba iskanci ba cikin shege lafiya lafiya muka rabu,Dana Mohsin har ya Kara aure,ubansa Bai samu ya Kara ba Ashe Karin auren akan Dana yake shi yake kwashe dadin na hakura na bar Masa

Jauro yace kasan duk aure aurena ban taba haihuwa ba har na gaji Gani Allah ya sa min son yara shine ni Kuma nake bi gari gari duk Inda naji wata tayi cikin shege sai naje na rufa mata asiri na auro ta da cikin,Kuma idan ta haihu juyin duniya nawa ne kawai,ko za a mutu cewa nake nawa ne,Abba yace amma Jauro ba karamin Dan iska bane Kai,yace sekaru goma da suka wuce naji wata ance tayi cikin shege ta haihu ai kuwa naje nace nawa ne ta karfi sai da aka bani Dan,Abba ya dinga dariya yace yanzu nawa ka rike? yace guda tara duk yayan shegu ne Daya ne ciki Wanda bana shege ba shi Kuma uwarsa ce mijinta ya mutu ya barta da ciki naji labari na aure ta,Abba yace ai ba kyau wannan ba aure kayi ba,Jauro yace ai ni duk Wacce kaga na auro me ciki to dama ni ban taba saduwa da ita ba,ko shimfida bamu hadawa ajiyeta nakeyi a gidana na Bata ci da Sha a raini cikin ta haihu ta yaye shi sai na sallameta,Yara gasu Nan duk sun zama samari Wanda ma ba Dan shege ba Yana Nan hamshakin me kudi ne yanzu,sauran ma duk suna da aikin yi da sana'arsu,Abba yace ya sunan me kudin? Annoor sunansa,Abba yace uhmm a Ina kake zanzo na kawo ziyara,Jauro yace yanzu na dawo Kano da zama duk da yaran su ai har yau tunaninsu nine na haife su.

BA EDITING YAU KU KARANTA DA HAKURI.

MASU SHARHI INA GODIYA.

AsmaBaffa
[1/2, 12:24 AM] AsmaBaffa: PAID GROUP 300

0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD GTBANK

YAN NIGER
+22790795939

🏫TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI

BOOK 1

106-110

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

PAGE NAKU NE
Murjanatu Abu Nabanga
Ummy M
Rahma Mamuda (Mmn Hajiya

*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262

Abba ya Kalli Jauro yace yanzu matanka nawa na gaskiya Wanda ba masu cikin shege ba? Jauro yace matana Uku,Ina Habiba matata ta farko ta kauye ai har yanzu muna tare sai na karo Na'imatu da Nafisa,Abba yace dole goshinka ya dinga kyalli Jauro,gashi ana ganinka an San kana cikin kwanciyar hankali,su Kuma masu cikin shegen fa? Yace ai duk na basu kudi na sallame su mace tana yayewa zan sallameta da kudi ta ware Danta Kuma ya zama nawa amma duk sun san iyayensu mata da dangin Iyayensu mata a zuwan aure muka yi muka haife su na sake su.
Chapter 94 · 0% Book details