← Book details Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 98

Sashe 10

Tantiriya A Gidan Yari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abincin ya bude har da cinyar kaza guda biyu manya manya,Me fushi Hanan ta dakko ragowar girkin rana jullof din shinkafa wacce ta sandare da kyar take turawa,Mohsin ya baje a Saman Center carpet Yana ci,Hanan sai satar kallonsa take yi tana kallon kwanon fried rice dinsa ta Sha hadi, tana ta kallon abincin, ta zaci hankalinsa baya kai ta zura hannu a hankali zata zari cinyar kazar,ji kake tassss ya make hannunta,hannun ta janye tare da galla Masa
harara taci gaba da cin daskararren abincinta,ta sake mika hannu ta zari lemonsa da sauri ta kafa Baki tana kurba kafin ta hadiye ya Mike ya matse bakinta sai da ta zubo shi waje ta karfin tsiya sannan ya kwace abinsa ya Mike gaba daya ya canja kujerar zama ya cinye abinsa tas har kashin sai da ya rumurmushe,wanka yake so yayi har 9pm Naila taki bude kofar ta fito bacci yake ji.

Ita kuwa Hanan har ta mike taje tayi kwanciyarta a daya dakin me dauke da katifa,yasan yanzu hakkinsa haihata haihata shike nan, yace to shike nan Kuma Yar karuwar da nake samu da dan tagomashi ta tafi da abinta taje da tsiyarta.

Kofar ya Mike ya bubbuga yace Yar kanwata Naila,Naila dake ta faman fesa Masa turare a jiki tace na'am da karfi,yace dan bude min wanka zanyi na kwanta bacci nake ji,Naila ta karaso bakin kofar tana murmushi tasan dama tunda taji ya kwantar da Kai to da dalili,tace haka kawai na bude ka zaneni aradu bani budewa,yace na fasa na huce,tace anya Yaya to rantse, yace wallah kinji na rantse haba My sweet sis, budewa tayi, ya waro idanu ganin yanda ta canjawa furniture din dakin wajen zama ta gyara bed ta dame shi yayi masifar kyau,yace ai ko Dan wannan gyaran bazan zaneki ba.

Ina kika samu tsintsiya da mopper? Naila tace naga matarka kazama a daki ta barsu sabo da kazanta da ganda tayi aiki da safe ta barsu a daki,kaga a toilet na ebo ruwa a famfo na zuba Omo duk a toilet na gani Kalli yanda yayi kyau ko uwarta Abu me man kuli baza ta iya irin aikin nan nawa ba,bakinta ya bige taji zafi,yace bana son rashin iya maganarki ki dinga zagin mutane kina ambatar sunan iyayenta kina zagi,Bai dace ba matar yayanki ce yanda zaki min biyayya haka zaki mata to nima ba biyayyar kike min ba bare ita,ki daina kinji ko ba tarbiyya bace wannan sannan wannan shigar da kike shi yasa ake ce miki Yar kauye bana Jin dadi in ana miki haka,nace muje na kaiki Saloon a gyara miki gashin kinki yarda,Umma tace ki tsaya ta taje miki kinki kowa yace ki bari a gyara miki kinki ji sai dai ki wanke shi a cukurkude babu sharcewa ba komai da ya bushe a haka zaki tufke abinki, Naila tace zafi Yaya ni bazan yarda ba wallahi akan a taje min gashina gwara a maidani kauye,ai sai da nace baza ku iya rike ni ba ka wani je ka dakko ni a dole ni wlh bana son birnin nan,gwara Ina kauye da yanzu nayi ashar tafi million amma anan ba dama sai da dalili ake ashar haba rayuwa tayi tsanani ba freedom ba kolabo,ni wallahi na gaji,sau daya ne aka taba cinye ni a caca badan na tafi da wasu kayan ba da zigidir za a min sabo da suturar da take jikina na saka a caca.

Mohsin Allah birni ba dadi ba kolabo iskancin banza suke yi na karya suke yi iskancin,Allah wallahi saura kadan Yaya na sa budurcina a caca,Mohsin ya saki salati da sallalami yace ke wai da gaske kike? Ni Ina wasa ne wlh da gaske nake yi Maka a dajinmu mata da Maza caca suke yi har matan aure, ranar da nace na sa budurcina a caca ranar kazo ka dakkoni,samari sunyi ca kowa ya shiga cacar ko zai dace harda dattijai sun shiga cacar kawai kuka zo daukana shi yasa samarin kauyen suka ce duk ranar daka koma wallahi sai kasha ruwan sanduna tunda ka cuce su,Kai ka sanni kuwa kowa respecting Dina yake a garin babu kamata,ga iya wankan gayu,ga kyau gani chass Umma ta haifi yarinya,babu me taurin kaina duk garin shi yasa aka sa min tantiriya amma ni ba yar iska bace fa,banyi komai ba kalau nake Yaya fess nake ba abinda ya faru da budurcina.

Mohsin sai da ya gama sauraronta sabo da idan ko yaro ne yazo da shirme ka saurara maybe akwai abin dauka ko na gyara sai a dauki mataki,yace ai bamu San haka kika lalace ba Naila,Naila tace ai na wuce haka ma,mu da muke zama a cinyar Maza watarana ma Affa ne ya min duka yace idan na sake sai ya yanka ni,shine ban Kuma ba,Mohsin ya saki salati yace Allah ya hadaki da mijin da zaici ubanki yayi maganinki Naila,dariya ta sheke da shi tace sai dai naci nasa uban Yaya,idan ba duk Wanda ya aureni ya auri masifa da kudinsa ba Allah ya konani,Mohsin yace Baki hadu da Wanda ya fiki bane,dole kizo ki buwaye mu ashe kin lalace da yawa

Naila tace ba karamar lalacewa ba Yaya Dan Allah yasa ma na tsaida Sallah wata daya da suka wuce,Mohsin ya sake bude Baki yace dama bakya sallah duk shekarunki har Sha Tara 19yrs to 20yrs? Naila tace wallahi sai bana Allah ya nufa,ai azumi ma sai shekarar Nan data wuce na tsayar da shi amma duk na karya nake yi sai na buya na Sha ruwa da Koko,watarana Kuma idan naje kiwo sai mu kafa baki a nonon saniya direct musha mu koshi.

Dan Allah full stop zo ki tafi gida goma tayi,a kauye ma sai na Kai 12 na dare a waje muna wasa bare Nan birni fitila ko Ina gari kamar rana,to naji ke duk turancin da kika iya a Ina kika koya? Makaranta mana,na yarda ai kina da brain,bature ne yazo dajinmu yawon bude Ido Ina zuwa makaranta,sai watarana zan baka labari,yanzu ka kaini gida Yaya,bacci nake ji na fada miki ki shiga napep,to kuwa sai dai na kwana,tsaki yaja yace jeki Palo bari nayi wanka nazo,Palo ta dawo ta zauna tana kallo har yayi wanka ya fito cikin 3qurt fari da t-shirt brown,yace muje mana kina ta kallona kamar baki sanni ba.

Naila tace, kayi kyau Yaya Ina ma ba Umma ce ta haifeka ba,gaskiya Umma Bata kyauta ba ta cuceni data haifo ka Kuma ta haifo ni ai sai ta tsaya idan ta haifeka ma ba laifi sai ta bari ni a haifeni a wani gidan can sai mu hadu sai muyi aurenmu ko ya kace,ai haihuwa ta mana illa kawai yanzu sabo da Allah sai a haife mu a gida daya the same father and mother haba haba,ai da ba gida daya bane ni nasan ma da Kai zan hadu dole in aureka, da anga 'Ya'ya wai wai zuky, dariya ce ta kwacewa Mohsin sabo da suna masifar kama da Naila duk gidan sunfi kama kowa ya gansu basai ance Yan uwa na jini bane.

Dariya ya dinga yi sosai tana kallonsa tana murmushi Yana dariya yace taso mu tafi ya riko hannunta, ta mike ta dauki sandarta da bata mantawa da ita,shi ya manta ma da shegiyar sandar yasan wannan sandar baza ta kwatu ba,ya bata rai yace ajiye sandar nan,haushi taji tace idan baza ka kaini ba ni zan tafi a kafa,ba yanda ya iya haka ya fitar da machine dinsa lifan.

Tace ban iya hawa machine ta gaba ba mu zaman dare muke a kaikaice muke Hawa, Yaya sai an dorani,ko Affa dorani yake yi,tayi tayi ta kasa hawa sai faman juye juye takeyi da kyar dai ta hau ta juya Masa baya maimakon ta Kalli gaba sai ta Kalli baya ma'ana sun hada baya da baya,ga sanda sakale a wuyansa, Mohsin yace wallahi idan kika fado ba ruwana Dan iskanci kinyi kusan wata guda a birni kina kallo yanda ake Hawa machine sai ki juya baya zaki fado kinji na rantse"

Naila tace to Yaya kaifa yayana nane na jini yanzu idan na juyo Enndu(Boobs) Dina suka taba jikin ka fa,mu mun iya hawa machine a haka,yace ke kika san Enndu shashasha, yaja machine dinsa suka Kara gaba ana ta kallo ta zauna daram amma dole ta rike machine din ta Dafe da hannaye biyu sanda Kuma ta tsakiyarsu a kwance.

Tana ganin me tsire Yana yawon dashi a Kai a bude tace Mohsin tsaya na siyi tsire,da karfi tayiwa me tsire magana Kai me tsire da zafinsa? Mohsin yace wannan abin ya gama Shan iska duk kwayoyin cuta sun hau Kai,tace mu haka muke siya a can kauye idan munje kasuwa,ta sake cewa da me tsire kaga ya hanani siya Kuma Ina so,kowa Yana jinta duk na gefen titi tana cewa ya hanani siyen tsire Kuma Ina so, sai dariya ake musu ga hanyar gefen tasha ne,Mohsin Yana ji yace nan ba haka bane to ba a wannan shirmen, sai da ya karasa waje me kyau Wanda nasu a cikin glass yake yace na nawa zaki siya? Tace na dari biyu

Uban wa zai baki nama a dari biyu,sauka tayi shima ya sauka ya siya mata na dubu daya,ya siyi na dubu biyu yace gashi nan ba yawa wannan nasu Umma ne da yaran,tace to mun gode ta sake juyawa zata hau machine irin dazu,Mohsin yace wallahi kika hau da baya sai dai na barki a nan,dole ta juya gaba ta shako wuyansa sannan ta hau ta rirrike shi Kam a haka ya kaita har gida,yace to shiga Kinga ma basu rufe gida ba da alama ke ake jira ta sauka
Chapter 10 · 0% Book details